Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 11/1 pp. 25-30
  • Suna Farin Ciki Duk Da Ana Tsananta Musu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Suna Farin Ciki Duk Da Ana Tsananta Musu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Wahala Saboda Aikata Adalci
  • An Zage Su Saboda Kristi
  • Suna Farin Cikin an Tsananta Musu Kamar Yadda Aka Yi wa Annabawa
  • Dalilai Masu Ƙwari na Farin Ciki
  • Ku Yi Farin Ciki Domin Sakamakon
  • Shan Tsanani Domin Adalci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ku Yi Farin Ciki Idan Ana Tsananta Muku
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Za Ka Iya Jimre Tsanantawa
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Yadda Zantattukan Yesu Ke Kawo Albarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 11/1 pp. 25-30

Suna Farin Ciki Duk Da Ana Tsananta Musu

“Albarka [farin ciki] tā tabbata gare ku sa’ad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku, suka kuma ƙaga muku kowace irin mugunta, saboda ni.”—MATIYU 5:11.

1. Wane tabbaci ne Yesu ya yi wa mabiyansa game da farin ciki da kuma tsanantawa?

SA’AD da Yesu ya tura manzanninsa da farko su yi wa’azin Mulki, ya yi musu gargaɗi cewa za su fuskanci hamayya. Ya gaya musu: “Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana.” (Matiyu 10:5-18, 22) Amma da farko, a cikin Huɗubarsa a kan Dutse, ya riga ya tabbatar wa manzanninsa da kuma wasu cewa irin wannan hamayya ba za ta daƙile musu matuƙar farin cikinsu ba. Hakika, Yesu ya nuna alaƙar farin ciki da tsanantawa ga Kiristoci! Ta yaya tsanantawa za ta kawo farin ciki?

Wahala Saboda Aikata Adalci

2. In ji Yesu da kuma manzo Bitrus, wace irin wahala ce take kawo farin ciki?

2 Farin ciki na takwas da Yesu ya ambata shi ne: “Albarka [farin ciki] tā tabbata ga masu shan tsanani saboda aikata adalci, domin Mulkin Sama nasu ne.” (Matiyu 5:10) Wahala zallarta ba abar yabo ba ce. Manzo Bitrus ya rubuta: “To, ina abin taƙama don kun yi haƙuri in kun sha dūka kan laifin da kuka yi? Amma in kun yi aiki nagari kuka sha wuya a kansa, kuka kuma haƙura, to, shi ne abin karɓa ga Allah.” Ya daɗa cewa: “Kada shan wuyar ko ɗaya cikinku ya zama na horon laifin kisankai ne, ko na sata, ko na mugun aiki, ko kuma na shisshigi. Amma in wani ya sha wuya a kan shi Kirista ne, to, kada ya ji kunya, sai dai ya ɗaukaka Allah saboda wannan suna.” (1 Bitrus 2:20; 4:15, 16) Kalmomin Yesu sun nuna cewa wahala tana kawo farin ciki sa’ad da aka jimre ta saboda aikata adalci.

3. (a) Menene yake nufi a sha wahala saboda aikata adalci? (b) Ta yaya tsanantawa ta shafi Kiristoci na fari?

3 Adalci na gaskiya ana gwada shi ne ta wajen jituwa da nufin Allah da kuma bin dokokinsa. Saboda haka, shan wahala domin aikata adalci yana nufin, shan wahala saboda mutum ya tsayayya wa matsin lamba ya ƙeta mizanai ko kuma dokokin Allah. Shugabannin Yahudawa sun tsananta wa manzannin domin sun ƙi su daina wa’azi cikin sunan Yesu. (Ayyukan Manzanni 4:18-20; 5:27-29, 40) Shin wannan ya daƙile murnar su ne ko kuma ya dakatar da wa’azinsu? Ko da wasa! “Suka tashi daga gaban majalisar, suna farin ciki a kan an ga sun isa su sha wulakanci saboda sunan Yesu. Kowace rana kuwa, ko a Haikali ko a gida, ba su daina koyarwa da yin bishara, cewa Yesu shi ne Almasihu ba.” (Ayyukan Manzanni 5:41, 42) Wannan tsanantawa ta ba su farin ciki kuma ta sabonta kuzarinsu wajen aikin wa’azi. Daga baya, Romawa suka tsananta wa Kiristoci na fari domin sun ƙi su yi wa Kaisar sujjada.

4. Waɗanne dalilai ne suke sa ake tsananta wa Kiristoci?

4 A zamaninmu na yau, ana tsananta wa Shaidun Jehovah domin sun ƙi su daina wa’azin “bisharan nan ta Mulki.” (Matiyu 24:14) Sa’ad da aka hana taronsu na Kirista, sun gwammace su wahala da su daina taro kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya umurta. (Ibraniyawa 10:24, 25) An tsananta musu domin tsakatsakinsu na Kirista ko kuma domin sun ƙi su yi amfani da jini. (Yahaya 17:14; Ayyukan Manzanni 15:28, 29) Duk da haka, wannan manne wa aikin adalci yana ba wa mutanen Allah a yau salama da kuma farin ciki.—1 Bitrus 3:14.

An Zage Su Saboda Kristi

5. Domin waɗanne dalilai ne ake tsananta wa mutanen Jehovah a yau?

5 Farin ciki na tara da Yesu ya yi maganarsa a Huɗubarsa a kan Dutse ma game da tsanantawa ne. Ya ce: “Albarka [farin ciki] tā tabbata gare ku sa’ad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku, suka kuma ƙaga muku kowace irin mugunta, saboda ni.” (Matiyu 5:11) Ainihin dalilin da ya sa ake tsananta wa mutanen Jehovah shi ne domin su ba na wannan mugun zamani na yau ba ne. Yesu ya gaya wa almajiransa: “Da ku na duniya ne da duniya ta so abinta, amma saboda ku ba na duniya ba ne, na kuma zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku.” (Yahaya 15:19) Hakazalika, manzo Bitrus ya ce: “Suna mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, kuna zarmewa, kuna aikata masha’a irin tasu, har suna zaginku.”—1 Bitrus 4:4.

6. (a) Me ya sa ake zagi da tsananta wa raguwar shafaffu da kuma abokanansu? (b) Shin irin wannan zagin yana rage farin cikinmu ne?

6 Mun riga mun ga cewa an tsananta wa Kiristoci na fari domin sun ƙi su daina wa’azi cikin sunan Yesu. Kristi ya umurci mabiyansa: “Za ku kuma zama shaiduna . . . har ya zuwa iyakar duniya.” (Ayyukan Manzanni 1:8) ’Yan’uwan Kristi amintattu shafaffu da suka rage, da abokanansu “ƙasaitaccen taro,” suna cika wannan umurni da ƙwazo. (Wahayin Yahaya 7:9) Saboda haka, Shaiɗan ya “ɗaura yaƙi da sauran zuriya tata [zuriyar “macen” sashen samaniya na ƙungiyar Allah], wato waɗanda ke kiyaye umarnin Allah, suke kuma shaidar Yesu.” (Wahayin Yahaya 12:9, 17) Mu Shaidun Jehovah, muna yin shaidar Yesu, Sarki mai sarauta a yanzu a Mulkin da zai halaka gwamnatocin mutane da suke hamayya da sabuwar duniya mai adalci ta Allah. (Daniyel 2:44; 2 Bitrus 3:13) Domin wannan ake zaginmu ake tsananta mana, amma mun sani cewa albarka ta tabbata a gare mu da aka ga mun dace mu wahala saboda sunan Kristi.—1 Bitrus 4:14.

7, 8. Wace ƙarya ’yan hamayya suka yi game da Kiristoci na fari?

7 Yesu ya ce mabiyansa ya kamata su kasance masu farin ciki har sa’ad da mutane ‘suka kuma ƙaga musu kowace irin mugunta’ domin sunansa. (Matiyu 5:11) Wannan hakika gaskiya ne game da Kiristoci na fari. Sa’ad da aka kama manzo Bulus a Roma, a tsakanin shekara ta 59-61 A.Z., shugabannin Yahudawa sun ce game da Kiristoci: “Don in dai ta ɗarikan nan ne, mun sani ko’ina ana kushenta.” (Ayyukan Manzanni 28:22) An zargi Bulus da Sila da “ta da duniya tsaye,” da kuma “saɓa dokokin Kaisar.”—Ayyukan Manzanni 17:6, 7.

8 Da yake rubutu game da Kiristoci a lokacin Daular Roma, ɗan tarihi K. S. Latourette ya ce: “Zargin sun sha bambam. Domin sun ƙi su yi bikin arna an ce da su kafirai. Domin ƙaurace wa yawancin irin rayuwar jama’a, irin su bikin arna, nishaɗin jama’a . . . ake yi musu ba’a ake cewa su maƙiya mutane ne. . . . An ce mata da maza suna saduwa cikin dare . . . suna masha’a. . . . Domin ana bikin [Tuna Mutuwar Kristi] tare da mabiya kawai aka fara yaɗa jita-jita cewa Kiristoci a kullum suna yanka jariri suna shanye jininsa suna kuma cinye namansa.” Bugu da ƙari, domin Kiristocin sun ƙi su bauta wa Kaisar, aka ce da su abokan gaban Gwamnati.

9. Ta yaya Kiristoci na ƙarni na fari suka mai da martani ga zargin ƙarya da aka yi musu, ba, kuma yaya yanayin a yau?

9 Irin waɗannan zargi ba su hana Kiristoci na fari cika umurnin da aka yi musu ba na yin wa’azin bisharar nan ta Mulki. A shekara ta 60-61 A.Z., Bulus ya yi maganar “bishara” cewa “tana hayayyafa, tana kuma ƙara yaɗuwa” ya kuma ce an “yi wa dukkan talikan da ke duniya.” (Kolosiyawa 1:5, 6, 23) Haka yake faruwa a yau. Ana yi wa Shaidun Jehovah zargin ƙarya, kamar yadda aka yi wa Kiristoci na ƙarni na farko. Duk da haka, aikin wa’azin bisharar nan ta Mulki yana yaɗuwa kuma yana ba da farin ciki ga waɗanda suke yin sa.

Suna Farin Cikin an Tsananta Musu Kamar Yadda Aka Yi wa Annabawa

10, 11. (a) Ta yaya Yesu ya kammala batun farin ciki na tara? (b) Me ya sa aka tsananta wa annabawan? Ka ba da misalai.

10 Yesu ya kammala batun farin ciki na tara yana cewa: “Ku yi murna . . . gama haka aka tsananta wa annabawan da suka riga ku.” (Matiyu 5:12) Annabawa da Jehovah ya aika wa Isra’ila marar aminci sau da yawa ba a sauraran su sai kuma a tsananta musu. (Irmiya 7:25, 26) Manzo Bulus ya ba da shaida a rubuce: “Me kuma zan ƙara cewa? Ai, lokaci zai ƙure mini wajen ba da labarin su . . . annabawa, waɗanda ta bangaskiya suka . . . sha ba’a da bulala, har ma da ɗauri da jefawa kurkuku.”—Ibraniyawa 11:32-38.

11 A zamanin mugun Sarki Ahab da matarsa, Yezebel, an kashe annabawan Jehovah da yawa da takobi. (1 Sarakuna 18:4, 13; 19:10) An saka annabi Irmiya a mari daga baya kuma aka zurara shi cikin rijiya mai laka. (Irmiya 20:1, 2; 38:6) Annabi Daniyel kuma an jefa shi cikin kogon zakoki. (Daniyel 6:16, 17) An tsananta wa dukan waɗannan annabawa kafin lokacin Kiristoci domin sun kāre bauta mai tsarki ta Jehovah. Shugabannin addinin Yahudawa ne suka tsananta wa da yawa cikin annabawan. Yesu ya kira Marubuta da Farisawa “ ’ya’yan masu kisan annabawa.”—Matiyu 23:31.

12. Me ya sa gata ce a wurinmu Shaidun Jehovah mu sha tsanani yadda annabawa na dā suka sha?

12 A yau, ana tsananta wa Shaidun Jehovah ne domin suna wa’azin bisharar Mulki da ƙwazo. Abokan gabanmu suna zarginmu da “tilasta tuba,” amma mun sani cewa waɗanda suka gabace mu bauta wa Jehovah sun fuskanci irin wannan kushewar. (Irmiya 11:21; 20:8, 11) Gata ce a gare mu mu wahala domin dalilin da annabawa na dā masu aminci suka wahala. Almajiri Yakubu ya rubuta: “A kan misalin shan wuya da haƙuri kuma, ’yan’uwa, ku dubi annabawa ma da suka yi magana da sunan Ubangiji. Ga shi, mukan yaba wa waɗanda suka jure.”—Yakubu 5:10, 11.

Dalilai Masu Ƙwari na Farin Ciki

13. (a) Me ya sa tsanantawa ba ya karya mana lago? (b) Menene yake taimakonmu mu jure, kuma menene wannan ya tabbatar?

13 Maimakon tsanani ya karya mana lago, sanin cewa muna bin tafarkin annabawa, Kiristoci na fari, da kuma Yesu Kristi kansa yana ƙarfafa mu. (1 Bitrus 2:21) Muna samun cikakkiyar gamsuwa daga Nassosi, kamar waɗannan kalmomin manzo Bitrus na gaba: “Ya Ƙaunatattuna, kada ku yi mamakin matsananciyar wahalar da ta same ku a kan gwaji, kamar wani baƙon abu ne yake faruwa gare ku. Albarka ta tabbata a gare ku in ana zaginku saboda sunan Almasihu, don Ruhun ɗaukaka, wato Ruhun Allah yā tabbata a gare ku.” (1 Bitrus 4:12, 14) Mun sani daga abin da muka fuskanta cewa mun jure wa irin wannan tsanantawa ne domin ruhun Jehovah ya tabbata a gare mu kuma yana ƙarfafa mu. Taimakon ruhu mai tsarki yana tabbatar mana cewa albarkar Jehovah tana tare da mu, kuma wannan yana ba mu farin ciki mai yawa.—Zabura 5:12; Filibiyawa 1:27-29.

14. Waɗanne dalilai muke da su na yin farin ciki sa’ad da ake tsananta mana saboda aikata adalci?

14 Wani dalili kuma da ya sa hamayya da tsanantawa saboda aikata adalci yake ba mu farin ciki shi ne domin yana tabbatar mana cewa muna rayuwa na Kiristoci na gaskiya da bauta ta ibada. Manzo Bulus ya rubuta: “Duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Almasihu Yesu, za su sha tsanani.” (2 Timoti 3:12) Muna kuma farin ciki matuƙa idan muka tuna cewa kasancewa da aminci sa’ad da muke fuskantar gwaji yana ba da amsa ga ƙalubalanci na Shaiɗan cewa dukan halittun Jehovah suna bauta masa ne saboda son kai. (Ayuba 1:9-11; 2:3, 4) Muna murna cewa mun saka hannu, ko da kaɗan ne, wajen ɗaukaka mulkin mallaka na adalci na Jehovah.—Karin Magana 27:11.

Ku Yi Farin Ciki Domin Sakamakon

15, 16. (a) Wane dalili ne Yesu ya bayar saboda mu yi “murna da farin ciki matuƙa”? (b) Wane lada ne aka ajiye wa Kiristoci shafaffu a sama, kuma ta yaya za a ba wa abokanansu “waɗansu tumaki” lada?

15 Yesu ya ba da ƙarin dalili na yin farin ciki sa’ad da ake tirtsatsa mana ake tsananta mana kamar yadda aka yi wa annabawa na dā. A kusan ƙarshen farin ciki na tara, ya ce: “Ku yi murna da farin ciki matuƙa, domin sakamakonku mai yawa ne a Sama.” (Matiyu 5:12) Manzo Bulus ya rubuta: “Sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawwami cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.” (Romawa 6:23) Hakika, ‘babban lada’ rai ne, kuma ba lada ba ne da za mu iya samu da guminmu. Baiwa ce. Yesu ya ce sakamakon ‘yana sama’ domin Jehovah ne yake bayarwa.

16 Shafaffu sun sami “kambin rai,” wato, a gare su, rai marar mutuwa tare da Kristi a sama. (Yakubu 1:12, 17) Waɗanda suke begen duniya kuma, “waɗansu tumaki,” suna sauraron rai madawwami a cikin aljanna a duniya. (Yahaya 10:16; Wahayin Yahaya 21:3-5) Ga dukan azuzuwa biyun, “sakamakon” ba abin da suka samu ba ne da guminsu. Shafaffu da kuma “waɗansu tumaki” sun sami ladansu ne daga alherin Jehovah “marar misaltuwa,” da ya motsa manzo Bulus ya ce: “Godiya tā tabbata ga Allah saboda baiwa tasa da ta fi gaban a faɗa.”—2 Korantiyawa 9:14, 15.

17. Me ya sa za mu yi farin ciki sa’ad da ake tsananta mana kuma mu yi “murna matuƙa”?

17 Manzo Bulus ya rubuta zuwa ga Kiristoci da waɗansun su ba da daɗewa ba Sarki Nero ya yi baƙin tsananta musu, ya ce: “Muna taƙama da shan wuyarmu, da ya ke mun sani shan wuya ke sa jimiri, jimiri kuma ke sa ingantaccen hali, ingataccen hali kuma ke sa sa zuciya, ita sa zuciyan nan kuwa ba ta sace iska faufau.” Kuma ya ce: Ku yi “farin ciki, ku jure wa wahala.” (Romawa 5:3-5; 12:12) Ko muna begen samaniya ko duniya, sakamakon amincinmu a lokacin gwaji ya fi dukan wani abin da muka dace a ba mu. Farin cikinmu na begen rayuwa har abada cikin bautar Ubanmu mai ƙauna, Jehovah, a ƙarƙashin Sarki Yesu Kristi ya fi gaban a kwatanta. Hakika muna da dalilin “murna matuƙa.”

18. Menene za mu yi tsammani daga al’ummai sa’ad da ƙarshe ya yi kusa, kuma menene Jehovah zai yi?

18 A wasu ƙasashe an tsananta wa Shaidun Jehovah kuma har yanzu ana tsananta musu. A annabcinsa game da ƙarshen zamanai, Yesu ya gargaɗi Kiristoci na gaskiya: ‘Duk al’ummai za su ƙi ku saboda sunana.’ (Matiyu 24:9) Sa’ad da ƙarshe ya yi kusa, Shaiɗan zai sa al’ummai su nuna ƙiyayyarsu ga mutanen Jehovah. (Ezekiyel 38:10-12, 14-16) Wannan zai sa Jehovah ya ɗauki mataki. “Da haka kuwa zan bayyana girmana da tsarkina in kuma sanar da kaina ga al’ummai. Ta haka za su sani ni ne Ubangiji.” (Ezekiyel 38:23) Domin haka Jehovah zai tsarkake sunansa kuma ya ceci mutanensa daga tsanani. Saboda haka, “albarka [farin ciki] tā tabbata ga mai jimirin gwaji.”—Yakubu 1:12.

19. Sa’ad da muke jiran babbar ‘ranar Jehovah,’ me ya kamata mu yi?

19 Sa’ad da babbar ‘ranar Jehovah’ ta kusato sosai, mu yi murna domin ‘an ga mun isa mu sha wulakanci’ saboda sunan Yesu. (2 Bitrus 3:10-13; Ayyukan Manzanni 5:41) Kamar Kiristoci na fari, mu ci gaba da ‘koyarwa da yin bishara cewa Yesu shi ne Almasihu’ da kuma Mulkinsa sa’ad da muke jiran sakamako a sabuwar duniya ta adalci ta Jehovah.—Ayyukan Manzanni 5:42; Yakubu 5:11.

Domin Bita

• Me ake nufi da wahala saboda aikata adalci?

• Ta yaya tsanantawa ya shafi Kiristoci na fari?

• Me ya sa za a ce ana tsananta wa Shaidun Jehovah kamar yadda aka tsananta wa annabawa na dā?

• Me ya sa za mu yi “murna da farin ciki matuƙa” domin ana tsananta mana?

[Hotuna a shafuffuka na 28, 29]

‘Farin ciki tā tabbata gare ku sa’ad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku’

[Inda aka Dauko]

Mutane a kurkuku: Chicago Herald-na Amirka

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba