Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • th darasi na 6 p. 9
  • Ka Bayyana Nassin da Ka Karanta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Bayyana Nassin da Ka Karanta
  • Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Gabatar da Nassi Yadda Ya Dace
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Kammalawa Mai Dadi
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Ka Nuna Yadda Za Su Amfana
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Mutane Su Koyi Darasi Daga Jawabin
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
Dubi Ƙari
Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
th darasi na 6 p. 9

DARASI NA 6

Ka Bayyana Nassin da Ka Karanta

Nassin da aka rubuta

Yohanna 10:​33-36

ABIN DA ZA KA YI: Kada ka karanta nassi kuma ka ci gaba da magana ba tare da ka bayyana nassin ba. Ka sa masu sauraronka su ga yadda nassin ya jitu da abin da kake gaya musu.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka ambata muhimman kalmomi. Bayan ka karanta nassi, ka ambata kalmomin da suka shafi abin da kuke tattaunawa. Kana iya yin hakan ta wajen maimaita kalmomin da ke cikin nassin ko kuma ka yi tambayar da za ta sa masu sauraronka su ga batun da kake so su fahimta.

    Shawara mai amfani

    Idan ka yi amfani da wasu kalmomi dabam don ka bayyana nassin, ka tabbata cewa masu sauraronka sun fahimci alaƙar da ke tsakanin kalmomin da ke nassin da kuma batun da kake gaya musu.

  • Ka nanata batun da kake so a fahimta. Idan ka gabatar da wani nassi kuma ka faɗi dalilin da ya sa kake so ka karanta, ka bayyana musu yadda kalmomin da ke nassin suka goyi bayan dalilin.

    Shawara mai amfani

    Ka bar Littafi Mai Tsarkinka a buɗe yayin da kake bayyana nassin. Hakan zai taimaka wa masu sauraronka su ma su bar nasu Littafi Mai Tsarki a buɗe kuma hakan zai sa su ga abin da kake bayyanawa daga nassin.

  • Ka sa bayaninka ya zama da sauƙin fahimta. Kada ka riƙa yin bayani a kan abubuwan da ba su shafi batun da kake tattaunawa ba. Ka yi tunani a kan abin da masu sauraronka suka riga suka sani game da batun, domin hakan zai sa ka san abubuwa masu muhimmanci da ya kamata ka bayyana musu.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba