Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Mayu pp. 8-13
  • Jehobah Zai Ƙarfafa Ka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Zai Ƙarfafa Ka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • JEHOBAH YANA GAFARTA MANA
  • JEHOBAH YA BA MU BEGE
  • JEHOBAH YANA TAIMAKA MANA MU DAINA JIN TSORO
  • Jehobah “Yakan Warkar da Masu Fid da Zuciya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ba Za Mu Taɓa Zama Mu Kaɗai Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Mayu pp. 8-13

TALIFIN NAZARI NA 20

WAƘA TA 7 Jehobah Ne Ƙarfinmu

Jehobah Zai Ƙarfafa Ka

“Albarka ta tabbata ga . . . Uba mai yawan tausayi, Allah wanda yake yi mana kowace irin taꞌaziyya!”—2 KOR. 1:3.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da za mu koya daga yadda Jehobah ya ƙarfafa Yahudawa da suka yi zaman bauta a Babila.

1. Saꞌad da Yahudawa suke zaman bauta a Babila, yaya rayuwarsu ta kasance?

KA YI tunanin yadda Yahudawa suka ji lokacin da suke zaman bauta a Babila. Sun yi shekaru da yawa suna yi wa Jehobah rashin biyayya. Saboda haka, ya ƙyale mutanen Babila su halaka ƙasarsu kuma su kwashe su zuwa bauta. Yaya rayuwarsu ta kasance a wurin? (2 Tar. 36:​15, 16, 20, 21) An bar Yahudawan su yi ayyukansu na yau da kullum a Babila. (Irm. 29:​4-7) Amma, ba irin rayuwar da suke so ba ne, domin abubuwa sun yi musu wuya. Ya suka ji game da yanayin da suke ciki? Wani cikinsu ya ce: “A bakin kogunan Babila, a can muka zauna muna kuka, saꞌad da muka tuna da Sihiyona.” (Zab. 137:1) Babu shakka, Yahudawan suna bukatar ƙarfafa. Amma a ina za su samu?

2-3. (a) Mene ne Jehobah ya yi don ya taimaka wa Yahudawan da aka kai zaman bauta a Babila? (b) Me za mu tattauna a wannan talifin?

2 Jehobah Allah ne da “yake yi mana kowace irin taꞌaziyya!” (2 Kor. 1:3) Yana ƙaunar bayinsa kuma yana so ya taꞌazantar da su, wato ya ƙarfafa su. Jehobah ya san cewa wasu daga cikin Yahudawan za su tuba, kuma su soma bauta masa a hanyar da ta dace. (Isha. 59:20) Saboda haka, fiye da shekaru 100 kafin a kai su bauta a Babila, Jehobah ya sa annabi Ishaya ya rubuta littafin Ishaya. Ta yaya littafin zai taimaka musu? Annabi Ishaya da kansa ya ce: “‘Taꞌazantar da jamaꞌata, Ka taꞌazantar da su!’ in ji Allahnku.” (Isha. 40:1) Ta wurin littafin da Ishaya ya rubuta, Jehobah ya sa Yahudawan su sami ƙarfafan da suke bukata.

3 Kamar Yahudawan, mu ma muna bukatar ƙarfafa. A wannan talifin, za mu ga hanyoyi uku da Jehobah ya ƙarfafa Yahudawan saꞌad da suke Babila. (1) Ya yi alkawari cewa zai gafarta wa duk wanda ya tuba, (2) ya ba su bege, kuma (3) ya taimaka musu kada su ji tsoro. Yayin da muke tattauna waɗannan batutuwa, ka lura da yadda mu ma za mu amfana daga kalmomi masu ban ƙarfafa da Jehobah ya gaya musu.

JEHOBAH YANA GAFARTA MANA

4. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa shi Allah ne mai tausayi? (Ishaya 55:7)

4 Jehobah “Uba mai yawan tausayi” ne. (2 Kor. 1:3) Ya nuna halin tausayi saꞌad da ya yi alkawarin gafarta wa Yahudawan da suka tuba. (Karanta Ishaya 55:7.) Jehobah ya ce: “Cikin ƙauna marar canjawa zan nuna miki tausayi har abada.” (Isha. 54:8) Ta yaya Jehobah zai nuna wannan tausayin? Ko da yake Yahudawan za su yi shekaru da yawa a Babila domin rashin biyayya da suka yi, Jehobah ya yi musu alkawari cewa a kwana a tashi za su koma gida. (Isha. 40:2) Babu shakka, hakan ya ƙarfafa Yahudawan da suka tuba!

5. Me ya sa muke da tabbaci fiye da Yahudawan cewa Jehobah zai gafarta mana?

5 Mene ne muka koya? Jehobah yana a shirye ya gafarta wa bayinsa da suka tuba. A yau, muna da tabbaci fiye da Yahudawan cewa Jehobah zai gafarta mana idan muka tuba. Me ya sa? Domin mun san abin da Jehobah ya yi don ya gafarta mana zunubanmu. Wajen shekaru 700 bayan annabcin da annabi Ishaya ya yi, Jehobah ya aiko Ɗansa duniya, don ya ba da ransa a madadin mutanen da suka tuba. Yadda Yesu ya ba da ransa, ya sa Jehobah zai iya gafarta mana zunubanmu gabaki ɗaya. (A. M. 3:19; Isha. 1:18; Afis. 1:7) A gaskiya, Jehobah Allah ne mai gafartawa!

6. Ta yaya za mu amfana idan muka yi tunani a kan abin da ke Ishaya 55:7? (Ka kuma duba hoton.)

6 Idan mun yi zunubi kuma muka tuba, amma zuciyarmu ta ci gaba da damunmu, abin da ke Ishaya 55:7 zai iya ƙarfafa mu. Zuciyarmu za ta iya damunmu musamman idan muna kan shan wahala don wani kuskuren da muka yi. Amma mu tuna cewa, idan mun riga mun tuba kuma mun daina yin zunubin, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah ya gafarta mana. Kuma idan Jehobah ya gafarta mana, ba zai sake tunawa da zunubin ba. (Ka duba Irmiya 31:34.) Da yake Jehobah yakan manta da zunuban da muka yi a dā, zai dace mu ma mu yi hakan. Abin da ya fi muhimmanci ga Jehobah shi ne abin da muke yi a yanzu, ba kurakuran da muka yi a dā ba. (Ezek. 33:​14-16) Nan ba da daɗewa ba, Ubanmu mai tausayi za cire duk matsalolin da muke fama da su don kurakuran da muka yi a dā.

Wani ɗanꞌuwa yana takawa ba tsoro. Hotuna: Akwai kananan hotuna da suka nuna halinsa a dā da halinsa a yanzu. Abubuwan da ya yi a dā: Na 1. Buga wasan bidiyo da ake mugunta a ciki. Na 2. Shan giya da yawa da kuma shan taba. Na 3. Kallon abubuwa marar kyau a kwamfutarsa. Abubuwan da yake yi yanzu: Na 1. Yana shara a Majamiꞌar Mulki. Na 2. Yana magana da wata ꞌyarꞌuwa da ta tsufa. Na 3. Yana waꞌazi.

Abin da ya fi muhimmanci ga Jehobah shi ne abin da muke yi a yanzu, ba kurakuran da muka yi a dā ba (Ka duba sakin layi na 6)


7. Me zai sa mu nemi taimako idan muna ɓoye wani zunubi mai tsanani da muka yi?

7 Me ya kamata mu yi idan zuciyarmu tana damunmu domin mun ɓoye wani zunubi mai tsanani da muka yi? Littafi Mai Tsarki ya ce mu nemi taimakon dattawa. (Yak. 5:​14, 15) Wani lokaci, bai da sauƙi mu gaya wa dattawa laifin da muka yi. Amma mu tuna cewa, taimako ne Jehobah zai yi mana ta wurin ꞌyanꞌuwan nan. Ƙari ga haka, za su tausaya mana kuma su nuna mana ƙauna kamar Jehobah. Don haka, idan mun tuba da gaske, za mu so mu nemi taimakonsu. Alal misali, Jehobah ya yi amfani da dattawa don ya taimaka ma wani ɗanꞌuwa mai suna Arthur,a da ya yi zunubi kuma zuciyarsa ta yi ta damunsa. Ɗanꞌuwan ya ce: “Na yi wajen shekara ɗaya ina kallon abubuwan batsa. Amma da na ji wani jawabi game da kasancewa da zuciya mai tsabta, sai na gaya wa matata da dattawa zunubin da na yi. Da na yi hakan, sai na ji sauƙi, amma ban daina baƙin ciki don abin da na yi ba. Dattawan sun gaya mini cewa Jehobah ba ya fushi da ni, kuma yana so in kusace shi. Sun ce yana mana gyara ne domin yana ƙaunar mu. Kalmominsu sun ratsa zuciyata, kuma sun taimaka mini in fahimci cewa Jehobah ya gafarta mini da gaske.” Yanzu, Arthur majagaba na kullum ne, da kuma bawa mai hidima. Ba shakka, sanin cewa Jehobah yana tausaya mana idan muka tuba, abin farin ciki ne!

JEHOBAH YA BA MU BEGE

8. (a) Wane bege ne Jehobah ya ba wa Yahudawan da suke zaman bauta a Babila? (b) Bisa ga Ishaya 40:​29-31, ta yaya wannan begen ya taimaka wa Yahudawan da suka tuba?

8 Yahudawan sun zata ba za su taɓa komawa garinsu ba, domin mutanen Babila ba sua sake bayinsu. (Isha. 14:17) Amma, Jehobah ya ba su bege. Ya yi alkawari cewa zai sa su sami ꞌyanci, kuma ba abin da zai iya hana shi cika alkawarinsa. (Isha. 44:26; 55:12) Mutanen Babila ba kome ba ne, su kamar ƙura ne a gun Jehobah. (Isha. 40:15) Idan ka hura ƙura, nan take zai ɓace. Don haka ba zai yi wa Jehobah wuya ya kuɓutar da mutanensa daga Babila ba. Ta yaya wannan alkawarin ya taimaka wa Yahudawan? Ya kwantar musu da hankali, amma ba shi ke nan ba. Ishaya ya ce: “Masu sa zuciya ga Yahweh za a sabonta ƙarfinsu.” (Karanta Ishaya 40:​29-31.) Begen samun ꞌyanci ya sa Yahudawan sun sami ƙarfi sosai kamar gaggafa da ke tashiwa sama.

9. Wane dalili ne Yahudawa suke da shi na gaskata cewa Jehobah zai ciki alkawarinsa?

9 Jehobah ya kuma ba wa Yahudawan dalilin da zai sa su gaskata cewa zai ciki alkawarinsa. Me ya sa muka ce haka? Domin akwai abubuwa da dama da ya faɗa da sun riga sun faru. Alal misali, ya ce Assuriyawa za su ci kabilu goma na Israꞌila da yaƙi kuma su kai su bauta. Kuma abin da ya faru ke nan. (Isha. 8:4) Ya ce Babiloniyawa za su halaka Urushalima kuma su kai mutanen bauta. Hakan ma ya faru. (Isha. 39:​5-7) An ƙwaƙule idanun Sarki Zedekiya, aka kuma kai shi Babila kamar yadda Jehobah ya ce. (Irm. 39:7; Ezek. 12:​12, 13) Dukan abubuwan da Jehobah ya faɗa sun faru. (Isha. 42:9; 46:10) Babu shakka, sanin hakan ya sa sun ƙara gaskata cewa Jehobah zai ꞌyantar da su kamar yadda ya ce!

10. Me zai taimaka mana mu ci gaba da mai da hankali ga begenmu a waɗannan kwanaki na ƙarshe?

10 Mene ne muka koya? Idan muna cikin damuwa, begen da muke da shi zai ƙarfafa mu. Muna rayuwa a mawuyacin lokaci kuma maƙiyan Allah suna gāba da mu. Amma kada mu bar hakan ya sa mu yi sanyin gwiwa. Jehobah ya ba mu begen yin rayuwa har abada cikin salama da kwanciyar hankali. Mu ci gaba da mai da hankali ga wannan begen. Domin in ba mu yi haka ba, za mu zama kamar wanda yake kallon wuri mai kyau ta wundo da aka yi da gilashi, amma wundon ya yi datti sosai. Mutumin ba zai ga wurin da kyau ba. Ta yaya za mu mai da hankali ga begenmu? Zai yi kyau mu riƙa samun lokaci muna yin tunani a kan yadda rayuwarmu za ta yi daɗi a Aljanna. Mu karanta talifofi, mu kalli bidiyoyi, kuma mu saurari waƙoƙi game da abubuwan da Allah zai yi mana a nan gaba. Ƙari ga haka, idan muna adduꞌa, mu gaya wa Jehobah abubuwan da muke marmarin gani a Aljanna.

11. Me ya taimaka wa ꞌYarꞌuwa Joy ta sami ƙarfin jimrewa?

11 Begen wata ꞌyarꞌuwa mai suna Joy da take rashin lafiya sosai ya ƙarfafa ta. Ta ce: “Idan damuwa ta yi min yawa, nakan gaya wa Jehobah kome don na san zai fahimci yadda nake ji. Jehobah kuma yakan ba ni ‘ikon da ya fi duka’ don in iya jimrewa.” (2 Kor. 4:7) ꞌYarꞌuwa Joy tana kuma tunani a kan yadda rayuwarta za ta kasance a Aljanna, inda “ba mazaunin ƙasar da zai ce, ‘Ina ciwo.’” (Isha. 33:24) Idan mu ma muna gaya wa Jehobah yadda muke ji a cikin adduꞌa, kuma muna mai da hankali ga begenmu, za mu sami ƙarfin jimre matsalolinmu.

12. Me ya tabbatar mana cewa Jehobah zai cika alkawuransa? (Ka kuma duba hoton.)

12 Mu ma Jehobah ya ba mu dalilan gaskata cewa zai cika alkawuransa. Abubuwa da dama da ya ce za su faru suna faruwa a yau. Alal misali, Mulkin Birtaniya da Amurka ya kasance “gauraye da ƙarfi da rashin ƙarfi” kamar yadda aka annabta. (Dan. 2:​42, 43) Muna kuma jin yadda ake yin “rawar ƙasa a wurare dabam-dabam,” kuma muna waꞌazi “ga dukan alꞌumma.” (Mat. 24:​7, 14) Ganin yadda waɗannan annabce-annabce suke cika, yana sa mu ƙara gaskata cewa Jehobah zai cika dukan alkawuran da ya yi mana.

Wata ꞌyarꞌuwa tana karanta annabce-annabce da ke Littafi Mai Tsarki kuma tana tunani mai zurfi a kansu. Kananan hotuna: Na 1. Wani ɗanꞌuwa da matarsa suna magana da wani mutum a inda suke waꞌazi da amalanke. Na 2. Wani balaꞌi ya auku kuma wani mutum da ɗansa suna kallon ɓarnar da balaꞌin ya jawo. Na 3. Wani dutse ya daki ƙafafun gunkin da Nebukadnezzar ya gani a mafarki, da aka yi zancensa a littafin Daniyel sura 2. Na 4. Mutane suna jin daɗin rayuwa a Aljanna.

Annabce-annabcen da suke cika a yau tabbaci ne cewa Jehobah zai cika alkawuransa (Ka duba sakin layi na 12)


JEHOBAH YANA TAIMAKA MANA MU DAINA JIN TSORO

13. (a) Wane abin ban tsoro ne zai faru dab da lokacin da Yahudawan za su sami ꞌyanci? (b) Bisa ga Ishaya 41:​10-13, ta yaya Jehobah ya kwantar wa Yahudawan da hankali?

13 Duk da cewa Jehobah ya ba Yahudawan bege don ya ƙarfafa su, ya san cewa abubuwan da za su faru dab da lokacin samun ꞌyancin, ba zai zo musu da sauƙi ba. Wani sarki mai iko sosai zai yaƙi kasashen da ke kewaye da Babila, bayan haka zai yaƙi Babila da kanta kamar yadda Jehobah ya annabta. (Isha. 41:​2-5) Shin, ya kamata hakan ya tayar wa Yahudawan hankali ne? Aꞌa. Domin shekaru da yawa kafin hakan ya faru, Jehobah ya ce: “Kada fa ka ji tsoro, gama ina tare da kai, kada ka damu, gama ni ne Allahnka.” (Karanta Ishaya 41:​10-13.) Me yake nufi saꞌad da ya ce, “Ni ne Allahnka”? Ba tuna musu yake yi cewa su bauta masa ba, domin sun san hakan. Amma, yana tuna musu ne cewa yana tare da su kuma zai taimaka musu.—Zab. 118:6.

14. Mene ne kuma Jehobah ya yi don ya kwantar wa Yahudawan da hankali?

14 Jehobah ya kuma kwantar wa Yahudawan da hankali ta wurin tuna musu da ikonsa da hikimarsa marar iyaka. Ya gaya wa Yahudawan cewa su dubi taurari a sama. Shi ne ya halicce su, kuma ya san sunan kowannensu. (Isha. 40:​25-28) Idan Jehobah ya san sunan kowane tauraro, babu shakka ya san sunan kowane bawansa! Kuma tun da Jehobah yana da ikon halittar taurari, zai iya taimaka wa bayinsa. Hakika, bai kamata Yahudawan su damu ko kuma su ji tsoro ba.

15. Ta yaya Jehobah ya shirya mutanensa don abin da zai faru a lokacin da za su sami ꞌyanci?

15 Jehobah ya kuma gaya wa mutanensa abin da za su yi a lokacin da za su sami ꞌyancin. A farko-farkon littafin Ishaya, Jehobah ya gaya wa bayinsa cewa: “Ku tafi ku shiga ɗakunanku, ku rufe ƙofofinku ku ɓoye kanku, sai fushina ya wuce.” (Isha. 26:20) Mai yiwuwa, Yahudawa sun bi wannan umurnin saꞌad da Sarki Sairus ya kawo wa Babila hari. Wani marubucin tarihi ya ce saꞌad da Sairus ya kawo wa Babila hari, ya “umurci [sojojinsa] su kashe duk wanda suka same shi a waje.” Ba shakka, mazaunan Babila sun ji tsoro! Amma ba mamaki Yahudawan sun tsira domin sun bi umarnin nan da Jehobah ya ba su.

16. Me ya sa bai kamata mu ji tsoro ba don abubuwan da za su faru a lokacin ƙunci mai girma? (Ka kuma duba hoton.)

16 Mene ne muka koya? Nan ba da daɗewa ba, za a soma ƙunci mai girma, kuma lokacin zai zama lokaci mafi muni da ba a taɓa ganin irinsa a duniya ba. Idan aka soma ƙunci mai girma, mutane za su ruɗe kuma su ji tsoro. Amma bayin Jehobah ba za su ji tsoro ba, domin mun san cewa Jehobah ne Allahnmu. Za mu kasance da ƙarfin zuciya ‘domin cetonmu ya yi kusa.’ (Luk. 21:28) Ko a lokacin da haɗin gwiwan alꞌummai za su kawo mana hari, ba za mu ji tsoro ba. Za mu ci gaba da dogara ga Jehobah. Jehobah zai yi amfani da malaꞌikunsa ya tsare mu, kuma zai ba mu umurnai da za su sa mu tsira. Ta yaya zai ba mu waɗannan umurnan? Ba mu sani ba. Amma, da alama cewa ta ikilisiyoyinmu ne za mu sami waɗannan umurnan. Ƙila su ne za su zama mana “ɗakunan” da aka ambata a Ishaya 26:​20, inda za mu sami kāriya. Ta yaya za mu yi shiri don abubuwan da za su faru a nan gaba? Mu kusaci ꞌyanꞌuwanmu maza da mata, mu kasance a shirye don mu bi umurnan da ƙungiyar Jehobah take bayarwa, kuma mu tabbata cewa Jehobah ne yake yi wa ƙungiyarmu ja-goranci.—Ibran. 10:​24, 25; 13:17.

ꞌYanꞌuwa maza da mata suna cikin wani ɗaki suna karanta Littafi Mai Tsarki a lokacin kunci mai girma. Da dare ne. Sun buɗe labule suna kallon waje ta wundo, kuma ɗaya daga cikinsu ya daga hannu yana nuna sama.

Idan muka tuna cewa Jehobah mai iko ne sosai, kuma zai cece mu a lokacin ƙunci mai girma, ba za mu ji tsoro ba (Ka duba sakin layi na 16)b


17. Me za mu yi don mu sami ƙarfafa daga wurin Jehobah?

17 Ko da yake irin rayuwar da Yahudawan suka yi a Babila ba sauƙi, Jehobah ya ba su abubuwan da za su ƙarfafa su. Mu ma zai yi mana hakan. Saboda haka, ko da me ya faru da kai, ka ci gaba da neman ƙarfafa daga wurin Jehobah. Ta yaya? Ka tuna cewa shi mai tausayi ne sosai da kuma gafartawa. Ka ci gaba da mai da hankali ga begenka. Ka kuma tuna cewa, Jehobah ne kake bauta wa, don haka ba ka bukatar ka ji tsoron kome.

ME YA SA NASSOSIN NAN SUKE ƘARFAFA KA?

  • Ishaya 55:7

  • Ishaya 40:​29-31

  • Ishaya 41:​10-13

WAƘA TA 3 Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu

a An canja wasu sunayen.

b BAYANI A KAN HOTO: Wasu ꞌyanꞌuwa sun taru a wani ɗaki. Da suka kalli taurari ta wundo, sai suka tuna cewa Jehobah yana da iko kuma zai iya kāre mutanensa ko da a ina ne suke a duniya.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba