Zuwa ga Romawa
13 Bari kowa ya yi biyayya* ga hukumomi masu iko, gama babu wani iko sai dai daga wurin Allah; Allah ne ya bar hukumomin da ake da su yanzu su kasance da matsayi dabam-dabam da suke da su. 2 Saboda haka, duk wanda yake gāba da hukuma, yana gāba ne da tsarin da Allah ya kafa; waɗanda suke gāba da hukuma za su jawo wa kansu hukunci. 3 Gama masu mulkin nan abin tsoro ne ga mugaye, ba ga waɗanda suke aikata abin da yake daidai ba. Kana so ka rabu da jin tsoron hukuma? To, ka ci-gaba da yin abin da yake daidai kuma hakan zai sa a yabe ka; 4 gama hukuma tana yi wa Allah hidima domin amfaninka ne. Amma idan kana aikata abu marar kyau, ka ji tsoro, domin ba a banza ne hukuma take riƙe takobi ba. Gama tana yi wa Allah hidima ne, domin ta wurinta ne Allah yake nuna fushinsa a kan wanda yake aikata mugunta.
5 Saboda haka, akwai dalili mai kyau da ya sa ya kamata ku yi biyayya ga hukumomi, ba don fushin Allah kawai ba, amma saboda lamirinku ma. 6 Shi ya sa ma kuke biyan haraji; gama su maꞌaikatan Allah ne waɗanda suke aikin nan a kowane lokaci domin mutane su amfana. 7 Ku ba wa kowa hakkinsa: wanda ya bukaci haraji, sai ku ba shi haraji; wanda ya bukaci ku biya wani abu, sai ku biya shi; wanda ya bukaci tsoro, sai ku ji tsoron sa; wanda ya bukaci girmamawa, sai ku girmama shi.
8 Kada ku riƙe hakkin kowa, sai dai ku ƙaunaci juna; gama duk wanda ya ƙaunaci maƙwabcinsa ya cika abin da doka ta ce. 9 Domin doka ta ce, “Kada ka yi zina, kada ka yi kisa, kada ka yi sata, kuma kada ka yi kwaɗayin abin wani,” a gaskiya dokokin nan da sauran dokokin, doka ɗaya ce, wato: “Dole ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” 10 Wanda yake da ƙauna ba ya yin mugunta ga maƙwabcinsa; don haka ƙauna ce take cika doka.
11 Kuma ku yi wannan domin kun san lokacin da muke ciki, wato lokaci ya riga ya yi da za ku farka daga barci, domin cetonmu ya yi kusa a yanzu fiye da a lokacin da muka fara ba da gaskiya. 12 Dare ya yi sosai; kuma gari ya kusan wayewa. Saboda haka, bari mu kawar da ayyukan duhu kuma mu saka kayan yaƙi na haske. 13 Bari mu yi ayyukan kirki yadda ya dace da waɗanda suke rayuwa cikin haske, ba tare da bukukuwan iskanci da shaye-shaye ba, ba tare da lalata da halin rashin kunya* ba, ba tare da faɗa da kishi ba. 14 Amma ku saka Ubangiji Yesu Kristi kamar riga, kuma kada ku riƙa yin shirin gamsar da shaꞌawoyin jiki.