Ayyukan Manzanni
2 Da ake yin Bikin Fentikos, dukan mabiyan Yesu suna wuri ɗaya. 2 Ba tsammani, sai aka ji wata ƙara daga sama kamar ta babbar iska, kuma ta cika dukan gidan da suke zaune a ciki. 3 Sai ga waɗansu abubuwa kamar harsunan wuta da aka rarraba sun bayyana a gare su, kuma sun sauka a kan kowannensu ɗaɗɗaya, 4 sai aka cika dukansu da ruhu mai tsarki, kuma suka soma magana da yaruka* dabam-dabam, yadda ruhu mai tsarki ya ba su ikon magana.
5 A lokacin akwai Yahudawa masu tsoron Allah da ke zama a Urushalima da suka fito daga kowace ƙasa a duniya. 6 Da suka ji ƙarar iskar, sai jamaꞌa suka taru, kuma suka yi mamaki, domin kowannensu ya ji mabiyan Yesu suna magana a yarensa. 7 Hakika, suka yi mamaki sosai, kuma suka ce: “Wannan abin ban mamaki ne, dukan mutanen nan da suke magana ba mutanen Galili ba ne? 8 To, yaya aka yi kowannenmu yana jin maganarsu a yarensa? 9 Mutanen da muke tare da su a nan Fartiyawa ne, da Midiyawa, da Elamawa, da mutanen Mesofotamiya, da Yahudiya, da Kafadokiya, da Fontus, da kuma yankin Asiya, 10 da yankin Farijiya, da Famfiliya, da Masar, da yankunan Libiya kusa da Sayirin, da baƙi daga Roma waɗanda Yahudawa ne da waɗanda suka karɓi addinin Yahudanci,* 11 da mutanen Kirit, da kuma Larabawa, mun ji su suna magana a yarenmu game da abubuwan ban mamaki na Allah.” 12 Hakika, dukansu sun yi mamaki kuma suka ruɗe suna tambayar juna cewa: “Mene ne wannan yake nufi?” 13 Amma wasu sun yi wa almajiran baꞌa suna cewa: “Sun bugu da ruwan inabi mai zaƙi.”*
14 Sai Bitrus ya tashi tsaye da manzanni goma sha ɗayan nan, kuma ya ɗaga murya ya yi musu magana ya ce: “Ku mutanen Yahudiya, da dukan mazaunan Urushalima, ku kasa kunne sosai kuma ku ji abin da nake faɗa. 15 A gaskiya, waɗannan mutanen ba a buge suke ba kamar yadda kuke tsammani, domin yanzu wajen ƙarfe tara ne na safe.* 16 A maimakon haka, abin da annabi Jowel ya faɗa ne yake cika a kansu, cewa: 17 ‘Allah ya ce, “A kwanakin ƙarshe, zan zubo wa kowane irin mutum ruhuna, ꞌyaꞌyanku maza da mata za su yi annabci, samarinku za su ga wahayi, kuma tsofaffinku za su yi mafarkai, 18 har ma a kan bayina maza da mata, zan zubo ruhuna a kwanakin nan, za su kuma yi annabci. 19 Zan yi abubuwan ban mamaki a sama, da alamun ban mamaki a duniya—za a ga jini da wuta da kuma baƙin hayaƙi. 20 Za a sa rana ta yi duhu, a sa wata kuma ya zama jini, kafin babbar rana mai ɗaukaka ta Jehobah* ta zo. 21 Kuma duk wanda ya kira ga sunan Jehobah* zai sami ceto.”’
22 “Ya ku mutanen Israꞌila, ku saurari maganar nan: Yesu mutumin Nazaret, mutum ne da Allah ya amince da shi, ya nuna hakan a fili ta wurin ayyukan ban mamaki da abubuwan ban mamaki da alamu waɗanda ya yi ta wurin Yesu a cikinku, kamar yadda ku ma kuka sani. 23 Wannan mutumin da aka miƙa a hannunku, bisa ga shawarar Allah da kuma abin da ya sani tun da daɗewa, shi ne kuka rataye a kan gungume ta hannun masu taka doka, kuka kuma kashe shi. 24 Amma Allah ya ta da shi ta wajen ꞌyantar da shi daga mutuwa,* domin ba zai yiwu ba mutuwa ta riƙe shi. 25 Shi ya sa Dauda ya yi magana game da shi cewa: ‘Na sa Jehobah* a gabana kullum, kuma domin yana a hannun damana, ba zan taɓa jijjiguwa ba. 26 Saboda haka, zuciyata tana murna kuma bakina yana magana da farin ciki sosai.* Kuma zan kasance da bege; 27 domin ba za ka bar ni* a cikin Kabari* ba, ko kuma ka bar wanda yake da aminci a gare ka ya ruɓe ba. 28 Ka koya mini hanyar da za ta kai ga rai; za ka sa ni in yi farin ciki sosai a gabanka.’
29 “Ya ꞌyanꞌuwana, zan iya yin magana da ku game da kakanmu Dauda ba tare da shakka ba. Ya mutu, an binne shi, kuma kabarinsa na nan tare da mu har wa yau. 30 Domin shi annabi ne kuma ya san cewa Allah ya yi masa alkawari tare da rantsuwa cewa zai naɗa wani daga cikin zuriyarsa ya zauna a kujerar mulkinsa, 31 ya hango hakan tun kafin ya faru, kuma ya yi magana game da tashiwar Kristi daga mutuwa, cewa, Allah bai bar shi a cikin Kabari* ba, kuma bai bar jikinsa ya ruɓe ba. 32 Allah ya ta da Yesun nan daga mutuwa kuma dukanmu mun shaida hakan. 33 Don haka, da yake an ɗaukaka shi zuwa hannun dama na Allah, kuma ya karɓi ruhu mai tsarki da Uban ya yi masa alkawarin sa, shi ne ya zubo mana da ruhu mai tsarkin nan, kamar yadda kuke gani kuma kuke ji. 34 Dauda bai haura sama ba, amma shi da kansa ya ce, ‘Jehobah* ya ce wa Ubangijina: “Ka zauna a hannun damana 35 har sai na sa abokan gābanka su zama matashin ƙafafunka.”’ 36 Saboda haka, bari dukan mutanen Israꞌila su sani cewa wannan Yesu da kuka kashe a kan gungume, a gaskiya Allah ya mai da shi Ubangiji da kuma Kristi.”
37 Saꞌad da suka ji wannan, hakan ya dame su sosai, sai suka ce wa Bitrus da kuma sauran manzannin: “Ya ꞌyanꞌuwanmu, mene ne ya kamata mu yi?” 38 Sai Bitrus ya ce musu: “Ku tuba, kuma a yi wa kowannenku baftisma a cikin sunan Yesu Kristi, domin a gafarta zunubanku kuma ku samu kyautar ruhu mai tsarki. 39 Gama wannan alkawarin domin ku ne, tare da ꞌyaꞌyanku, da kuma dukan waɗanda suke nesa, wato, dukan waɗanda Jehobah* Allahnmu zai iya kira su zo wurinsa.” 40 Ya kuma yi musu waꞌazi sosai, ta wajen maganganu da yawa, kuma ya ci-gaba da yi musu gargaɗi, yana cewa: “Ku yi abin da zai sa a cece ku daga wannan muguwar tsara.” 41 Waɗanda suka yarda da maganar Bitrus da dukan zuciyarsu,* an yi musu baftisma. A ranar sun sami ƙarin mutane wajen dubu uku. 42 Sun ci-gaba da mai da hankali sosai ga koyarwar da manzannin suke yi, kuma suna yin abubuwa tare,* da cin abinci da kuma yin adduꞌoꞌi.
43 Sai tsoro ya soma kama kowa, domin Allah yana yin ayyukan ban mamaki da alamu da yawa ta wurin manzannin. 44 Dukan waɗanda suka ba da gaskiya suna tare kuma suna amfani da abubuwan da suke da su tare. 45 Kuma suna sayar da filayensu, da dukan abubuwan da suke da su, suna rarraba wa kowa kuɗin bisa ga bukatarsa. 46 Kowace rana kuma, suna zuwa haikali da nufi ɗaya, kuma sukan ci abinci a gidaje dabam-dabam, sun yi farin cikin rarraba abincinsu ga juna, kuma sun yi hakan da zuciya ɗaya. 47 Suna yabon Allah da kuma samun farin jini a gaban dukan mutane. Ƙari ga haka, a kowace rana Jehobah* yana ƙaro musu mutanen da za su samu ceto.