Zuwa ga Romawa
8 Don haka, waɗanda suke da haɗin kai da Kristi Yesu ba za a same su da laifi ba. 2 Gama dokar ruhu da ke ba da rai ga waɗanda suke da haɗin kai da Kristi Yesu, ta ꞌyantar da ku daga dokar zunubi da kuma ta mutuwa. 3 Abubuwan da Dokar* ta kasa cim ma domin ajizancin mutane, Allah ya cim ma ta wurin aiko da Ɗansa cikin kamannin ꞌyanꞌadam masu zunubi, don ya kawar da zunubi, ta hakan ya hukunta zunubi da ke jikinmu. 4 Hakan ya faru domin abubuwan adalci da Dokar ta ce a yi su cika a kanmu, mu da ba ma rayuwa bisa ga shaꞌawoyin jiki, amma bisa ga abin da ruhu yake so. 5 Gama waɗanda suke rayuwa bisa ga shaꞌawoyin jiki suna mai da hankali ga abubuwan da jiki yake so, amma waɗanda suke rayuwa bisa ga ruhu suna mai da hankali ga abubuwan ruhu. 6 Domin mai da hankali ga shaꞌawoyin jiki, yana jawo mutuwa, amma mai da hankali ga abubuwan ruhu, yana kawo rai da salama; 7 gama mai da hankali ga shaꞌawoyin jiki, yana nufin yin gāba da Allah, domin jikin ba ya biyayya ga dokar Allah. Hakika, ba zai iya yin biyayya ba. 8 Don haka, waɗanda suke rayuwa bisa ga jiki, ba za su iya faranta wa Allah rai ba.
9 Amma idan ruhun Allah yana tare da ku da gaske, kuna rayuwa ne bisa ga ruhun, ba bisa ga jiki ba. Duk wanda ba shi da ruhun Kristi, shi ba na Kristi ba ne. 10 Idan Kristi yana da haɗin kai da ku, jikinku ya mutu saboda zunubi, amma ruhun Allah yana sa ku kasance da rai saboda adalci. 11 Yanzu, idan ruhun wanda ya ta da Yesu daga mutuwa yana cikinku, wanda ya ta da Kristi Yesu daga mutuwa zai ba ku rai ta wurin ruhunsa da yake zama a cikinku.
12 Saboda haka ꞌyanꞌuwa, muna da hakki, amma ba ga jiki don mu yi rayuwa bisa ga jiki ba; 13 Idan kuna rayuwa bisa ga jiki, tabbas za ku mutu; amma idan kun kashe ayyukan jiki ta wurin ruhu, za ku rayu. 14 Gama dukan waɗanda ruhun Allah ne yake musu ja-goranci, su ꞌyaꞌyan Allah ne. 15 Domin ba ruhun bauta ne aka ba ku da zai sa ku sake jin tsoro ba, amma an ba ku ruhun da ya sa kuka zama ꞌyaꞌya, kuma ruhun ne yake sa muke faɗa da babbar murya cewa: “Abba,* Uba!” 16 Ruhun da kansa yana ba mu* shaida cewa mu ꞌyaꞌyan Allah ne. 17 Tun da mu ꞌyaꞌya ne, mun kuma zama magāda, wato za mu sami gādo daga wurin Allah. Kuma zai ba mu gādon tare da Kristi, idan dai mun sha wahala tare, za a ɗaukaka mu tare.
18 A ganina, wahalar da muke sha a yanzu ba kome ba ne idan aka kwatanta wahalar da ɗaukakar da za a bayyana a kanmu. 19 Domin halittu suna jira da marmari, lokacin da za a bayyana ꞌyaꞌyan Allah. 20 Gama an sa halittun su yi rayuwa marar amfani, ba da son ransu ba, amma ta wurin wanda ya sa su a yanayin ne, saboda bege 21 cewa za a ꞌyantar da halittun da kansu ma daga bauta ga ruɓewa kuma su sami ꞌyanci mai ɗaukaka na ꞌyaꞌyan Allah. 22 Mun san cewa dukan halittu sun ci-gaba da nishi tare da kuma kasancewa cikin azaba tare har yanzu. 23 Ƙari ga haka, mu da kanmu da muke da nunan fari na gādonmu, wato ruhun Allah, mu da kanmu muna nishi a cikinmu, yayin da muke jira da marmari, lokacin da Allah zai ɗauke mu a matsayin ꞌyaꞌyansa, ta wurin ꞌyantar da jikinmu ta fansar Yesu. 24 Gama Allah ya cece mu ta wannan begen; amma begen da ake gani ba bege ba ne, don idan mutum yana ganin wani abu, zai yi begen abin kuma ne? 25 Amma idan muna begen abin da ba ma gani, za mu ci-gaba da jiran sa da marmari da kuma jimrewa.
26 Haka ma, ruhun ma yana taimaka mana a cikin kasawarmu; matsalar ita ce, a wasu lokuta ba mu san abin da muke bukatar mu yi adduꞌa a kai ba, sai dai ruhun da kansa yana roƙo a madadinmu, da nishe-nishe waɗanda kalmomi ba za su iya bayyana ba. 27 Amma mai bincika zukata ya san maꞌanar abin da ruhun yake roƙo, domin yana roƙo a madadin tsarkaka bisa ga nufin Allah.
28 Mun san cewa Allah yana sa dukan ayyukansa su kasance da haɗin kai don waɗanda suke ƙaunar sa su amfana, wato waɗanda aka kira bisa ga nufinsa; 29 domin tun da farko ya san waɗanda zai zaɓa kuma ya yanke shawara* cewa za su kasance da siffar Ɗansa, domin Ɗansa ya zama ɗan fari a tsakanin ꞌyanꞌuwa da yawa. 30 Ƙari ga haka, waɗanda ya zaɓa, su ne kuma waɗanda ya kira; kuma waɗanda ya kira, su ne kuma ya ce da su masu adalci. A ƙarshe, waɗanda ya ce su ne masu adalci, su ne kuma ya ɗaukaka.
31 To, mene ne za mu ce game da abubuwan nan? Idan Allah yana tare da mu, wane ne zai iya yin gāba da mu? 32 Tun da bai bar wani abu ya hana shi ba da Ɗansa dominmu ba, amma ya ba da shi a matsayin fansa domin dukanmu, ba kwa ganin zai ba mu sauran abubuwa da dukan zuciyarsa? 33 Wane ne zai zargi waɗanda Allah ya zaɓa? Allah shi ne Wanda ya ce su masu adalci ne. 34 Wane ne zai hukunta su? Kristi Yesu ne ya mutu, hakika ban da haka ma, shi ne wanda aka ta da daga mutuwa, wato wanda yake zaune a hannun dama na Allah kuma wanda yake roƙo a madadinmu.
35 Wane ne zai raba mu da ƙaunar da Kristi yake nuna mana? Ƙunci ne, ko wahala, ko tsanantawa, ko yunwa, ko rashin kayan sakawa, ko haɗari, ko kuma takobi ne? 36 Kamar yadda yake a rubuce cewa: “Saboda kai ne ake kashe mu dukan yini; an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.” 37 Amma duk da waɗannan abubuwan ma, muna yin nasara sosai ta wurin wanda ya ƙaunace mu. 38 Gama ina da tabbaci cewa ko mutuwa, ko rai, ko malaꞌiku, ko gwamnatoci, ko abubuwa da suke nan yanzu, ko abubuwa masu zuwa, ko iko, 39 ko tsawo, ko zurfi, ko kuma wata halitta, ba za su iya raba mu ba da ƙaunar da Allah yake nuna mana ta wurin Kristi Yesu Ubangijinmu.