Ta Hannun Luka
22 Lokacin Bikin Burodi Marar Yisti wanda ake kira Bikin Ƙetarewa ya yi kusa. 2 Kuma da yake manyan firistoci da marubuta suna tsoron jamaꞌa, sai suka soma neman hanyar da ta dace don su kashe Yesu. 3 Sai Shaiɗan ya shiga cikin zuciyar Yahuda, wanda ake kira Iskariyoti, ɗaya daga cikin almajiransa goma sha biyu. 4 Sai ya je ya yi magana da manyan firistoci da shugabannin masu gadin haikali a kan yadda zai ba da shi gare su. 5 Da suka ji hakan, sun yi farin ciki sosai kuma sun yarda cewa za su ba shi kuɗin azurfa. 6 Don haka, ya amince kuma ya soma neman dama mai kyau da zai ba da Yesu a hannunsu, saꞌad da jamaꞌa ba sa tare da shi.
7 Da ranar Bikin Burodi Marar Yisti ta kewayo, wato a ranar da za a miƙa hadayar dabba ta Bikin Ƙetarewa, 8 sai Yesu ya aiki Bitrus da Yohanna, yana cewa: “Ku je ku shirya mana Bikin Ƙetarewa don mu ci.” 9 Sai suka ce masa: “Ina kake so mu je mu shirya bikin?” 10 Sai ya ce musu: “Saꞌad da kuka shiga cikin gari, wani mutum da yake ɗauke da tulun ruwa zai same ku. Ku bi shi zuwa duk gidan da ya shiga. 11 Ku ce wa maigidan, ‘Malam ne ya aike mu mu ce maka: “Ina ɗakin da zan ci abincin Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina?”’ 12 Mutumin zai nuna muku wani babban ɗaki da ke saman gidan, wanda aka gyara. A wurin ne za ku shirya mana bikin.” 13 Sai almajiran suka tafi, kuma suka sami abubuwa yadda Yesu ya gaya musu. Suka kuma shirya Bikin Ƙetarewan.
14 Da lokaci ya yi, sai Yesu ya zauna tare da manzanninsa suna cin abinci a teburi. 15 Sai ya ce musu: “Na yi marmari sosai in ci wannan Bikin Ƙetarewa tare da ku kafin in sha wahala. 16 Domin ina gaya muku, ba zan ƙara cin bikin nan ba, har sai maꞌanarsa ta cika a Mulkin Allah.” 17 Sai ya karɓi kofi, ya yi godiya kuma ya ce: “Ku karɓi kofin nan kuma ku miƙa wa juna. 18 Ina gaya muku, daga yanzu ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai Mulkin Allah ya zo.”
19 Ƙari ga haka, ya ɗauki burodi, ya yi godiya ga Allah, ya kakkarya, ya kuma ba su yana cewa: “Wannan yana wakiltar jikina wanda za a bayar domin ku. Ku dinga yin haka don tunawa da ni.” 20 Ƙari ga haka, ya yi hakan ma da kofin, bayan da suka gama cin abincin yamma, ya ce: “Wannan kofi yana wakiltar sabuwar yarjejeniya wadda aka tabbatar da ita da jinina, wanda za a zubar a madadinku.
21 “Amma ga shi, wanda zai ci amanata yana cin abinci tare da ni a teburi. 22 Hakika, Ɗan mutum zai tafi kamar yadda aka faɗa. Duk da haka dai, kaiton wanda ta wurin shi ne za a ci amanar Ɗan mutum!” 23 Sai almajiransa suka soma tattaunawa da juna a kan wane ne a cikinsu zai yi hakan.
24 Ƙari ga haka, almajiran suka soma gardama sosai a kan wanda ake ganin ya fi girma a tsakaninsu. 25 Sai ya ce musu: “Kun san cewa sarakunan alꞌummai suna wahalar da waɗanda suke mulki a kansu. Kuma masu iko a kansu ana kiran su Masu Taimako. 26 Ku kam, kada hakan ya faru a tsakaninku. Amma bari wanda ya fi girma a tsakaninku ya zama kamar wanda ya fi ƙanƙanta. Wanda yake yi muku ja-goranci kuma ya zama kamar bawanku. 27 Wane ne ya fi girma, wanda ya zauna yana cin abinci ne, ko kuma shi wanda yake raba abinci? Ai, wanda ya zauna yana cin abinci ne. Amma ga shi ina a cikinku kamar mai raba abinci.
28 “Duk da haka, ku ne kuka kasance tare da ni saꞌad da nake shan wahala. 29 Kuma na yi yarjejeniya da ku, kamar yadda Ubana ya yi yarjejeniya da ni game da mulki, 30 domin ku ci, ku sha a teburina da ke Mulkina, kuma ku zauna a kujerun mulki kuna yi wa kabilu goma sha biyu na Israꞌila shariꞌa.
31 “Siman, Siman, ga shi, Shaiɗan ya nemi izini ya tankaɗe dukanku kamar yadda ake tankaɗe hatsi daga dusa. 32 Amma na yi adduꞌa a madadin ka domin kada ka rasa bangaskiyarka, kuma da zarar ka dawo, ka ƙarfafa ꞌyanꞌuwanka.” 33 Sai Bitrus ya ce masa: “Ubangiji, a shirye nake in bi ka har zuwa kurkuku da kuma mutuwa.” 34 Amma Yesu ya ce masa: “Ina gaya maka Bitrus, kafin zakara ya yi cara yau, za ka yi mūsun sani na sau uku.”
35 Ya kuma ce musu: “Saꞌad da na aike ku ba tare da jakar kuɗi, da jakar abinci, da kuma takalma ba, ba ku rasa kome ba, ko akwai abin da kuka rasa ne?” Sai suka ce: “Aꞌa!” 36 Sai ya ce musu: “Amma yanzu, bari wanda yake da jakar kuɗi ya ɗauka, haka ma da jakar abinci. Kuma wanda bai da takobi ya sayar da mayafinsa ya sayi guda. 37 Ina gaya muku cewa, dole ne abin da aka rubuta ya cika a kaina, wato, ‘An haɗa shi da masu mugunta.’ Kuma hakan yana cika a kaina.” 38 Sai suka ce masa: “Ubangiji, ga takubba guda biyu a nan.” Sai ya ce musu: “Biyun sun isa.”
39 Saꞌad da ya bar wurin, sai ya tafi Tudun Zaitun kamar yadda ya saba, kuma almajiransa ma sun bi shi. 40 Da suka isa wurin, sai ya ce musu: “Ku ci-gaba da yin adduꞌa domin kada ku faɗi cikin jarraba.” 41 Sai ya bar su ya yi gaba, misalin nisan jifa. Sai ya durƙusa kuma ya soma yin adduꞌa, 42 yana cewa: “Ya Uba, idan kana so, ka ɗauke mini wannan kofi. Duk da haka, bari a yi nufinka, ba nufina ba.” 43 Sai wani malaꞌika daga sama ya fito ya ƙarfafa shi. 44 Amma da yake yana cikin baƙin ciki sosai, sai ya ci-gaba da yin adduꞌa, har zufarsa ta zama kamar jini da yake ɗiga a ƙasa. 45 Saꞌad da Yesu ya gama adduꞌa, sai ya je wurin almajiransa, kuma ya same su suna barci, domin baƙin ciki da suke ciki ya gajiyar da su. 46 Sai ya ce musu: “Me ya sa kuke barci? Ku tashi ku ci-gaba da yin adduꞌa domin kada ku faɗi cikin jarraba.”
47 Yayin da Yesu yake kan magana, sai jamaꞌa suka zo. Kuma wani mutum mai suna Yahuda, ɗaya daga cikin almajiransa goma sha biyu ne ya ja-gorance su. Sai ya zo wurin Yesu don ya sumbace shi. 48 Amma Yesu ya ce masa: “Yahuda, da sumba ne kake cin amanar Ɗan mutum?” 49 Saꞌad da waɗanda suke tare da shi suka ga abin da yake so ya faru, sai suka ce: “Ubangiji, mu kai hari da takobin ne?” 50 Har ma ɗaya daga cikinsu ya sari bawan shugaban firistoci ya yanke kunnensa na dama. 51 Amma Yesu ya amsa ya ce: “Ya isa haka.” Sai ya taɓa kunnen mutumin kuma ya warkar da shi. 52 Sai Yesu ya ce wa manyan firistoci, da shugabannin masu gadin haikali, da kuma dattawa waɗanda suka zo su kama shi cewa: “Shin kun fito ne ku kama ni da takubba da sanduna, sai ka ce ɗan fashi? 53 A kullum, ina tare da ku a haikali, ba ku kama ni ba. Amma wannan ne lokacinku da lokacin da mutanen da ke cikin duhu za su nuna ikonsu.”*
54 Sai suka kama shi suka tafi da shi, kuma suka kawo shi cikin gidan shugaban firistoci. Amma Bitrus yana bin su daga nesa. 55 Saꞌad da suka kunna wuta a tsakiyar farfajiyar gidan kuma suka zauna tare, Bitrus yana zaune a cikinsu. 56 Saꞌad da wata yarinya mai hidima a gidan ta gan shi yana zaune kusa da wutar, sai ta kalle shi da kyau kuma ta ce: “Wannan mutumin ma yana tare da shi.” 57 Amma ya yi mūsun hakan, yana cewa: “Ban san shi ba.” 58 Bayan ɗan lokaci, sai wani mutum ya gan shi kuma ya ce: “Kai ma ɗaya daga cikinsu ne.” Amma Bitrus ya ce: “Ba na cikinsu.” 59 Bayan kamar awa ɗaya, sai wani mutum ya soma nacewa sosai yana cewa: “Ba shakka, mutumin nan yana tare da shi, domin shi mutumin Galili ne!” 60 Amma Bitrus ya ce: “Ban san abin da kake faɗa ba.” Kuma nan da nan saꞌad da yake kan magana, sai zakara ya yi cara. 61 Sai Ubangiji ya juya ya kalli Bitrus, kuma Bitrus ya tuna abin da Ubangiji ya ce masa: “Kafin zakara ya yi cara yau, za ka yi mūsun sani na sau uku.” 62 Sai Bitrus ya fita waje, ya yi kuka sosai.
63 Sai mutanen da suka kama Yesu, suka soma yi masa baꞌa, da dūka. 64 Kuma bayan da suka rufe fuskarsa, sai suka ci-gaba da cewa: “Idan kai annabi ne, ka gaya mana, wa ya mare ka?” 65 Kuma suka faɗi wasu abubuwa marasa kyau game da shi.
66 Saꞌad da gari ya waye, sai dattawan jamaꞌa, wato manyan firistoci da marubuta suka taru, suka kai shi wurin taro na Sanhedrin,* kuma suka ce: 67 “Idan kai ne Kristi, ka gaya mana.” Amma ya ce musu: “Ko na gaya muku ma, ba za ku taɓa yarda ba. 68 Ƙari ga haka, idan na yi muku tambaya, ba za ku ba ni amsa ba. 69 Amma daga yanzu, Ɗan mutum zai zauna a hannun dama mai iko na Allah.” 70 Da jin haka, sai dukansu suka ce: “Kana nufin kai ne Ɗan Allah?” Sai ya ce musu: “Ku da kanku ma kun faɗi hakan.” 71 Sai suka ce: “Me ya sa muke bukatar ƙarin shaida? Domin mu da kanmu mun ji ya faɗi hakan da bakinsa.”