Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • es25 pp. 57-67
  • Yuni

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yuni
  • Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Lahadi, 1 ga Yuni
  • Litinin, 2 ga Yuni
  • Talata, 3 ga Yuni
  • Laraba, 4 ga Yuni
  • Alhamis, 5 ga Yuni
  • Jumma’a, 6 ga Yuni
  • Asabar, 7 ga Yuni
  • Lahadi, 8 ga Yuni
  • Litinin, 9 ga Yuni
  • Talata, 10 ga Yuni
  • Laraba, 11 ga Yuni
  • Alhamis, 12 ga Yuni
  • Jumma’a, 13 ga Yuni
  • Asabar, 14 ga Yuni
  • Lahadi, 15 ga Yuni
  • Litinin, 16 ga Yuni
  • Talata, 17 ga Yuni
  • Laraba, 18 ga Yuni
  • Alhamis, 19 ga Yuni
  • Jumma’a, 20 ga Yuni
  • Asabar, 21 ga Yuni
  • Lahadi, 22 ga Yuni
  • Litinin, 23 ga Yuni
  • Talata, 24 ga Yuni
  • Laraba, 25 ga Yuni
  • Alhamis, 26 ga Yuni
  • Jumma’a, 27 ga Yuni
  • Asabar, 28 ga Yuni
  • Lahadi, 29 ga Yuni
  • Litinin, 30 ga Yuni
Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2025
es25 pp. 57-67

Yuni

Lahadi, 1 ga Yuni

Sai tare da azaba mai yawa za mu shiga mulkin Allah.—A. M. 14:22.

Jehobah ya yi wa dukan Kiristoci a ƙarni na farko albarka yayin da suka ci-gaba da bauta ma Jehobah duk da matsalolin da suka fuskanta. An tsananta musu sosai, a wasu lokuta ma hakan ya faru a lokacin da ba su yi tsammani ba. Ka yi laꞌakari da abin da ya faru da manzo Bulus da kuma Barnaba saꞌad da suke waꞌazi a Listira. Da farko, mutanen sun marabce su kuma sun saurare su. Amma jim kaɗan, wasu maƙiya sun “rinjayi taron,” kuma hakan ya sa wasu daga cikin mutanen da suka marabci Bulus da Barnaba, sun jejjefi Bulus da duwatsu da niyyar kashe shi. (A. M. 14:19) Duk da haka, Bulus da Barnaba sun ci-gaba da yin waꞌazi a wani wuri dabam. A sakamakon haka, sun “sami almajirai da yawa,” kuma maganarsu da abin da suka yi sun ƙarfafa ꞌyanꞌuwansu Kiristoci. (A. M. 14:​21, 22) Da yake Bulus da Barnaba ba su daina yin waꞌazi ba duk da tsanantawa da aka yi musu, mutane da yawa sun amfana. Mu ma idan ba mu daina yin aikin da Jehobah ya ba mu ba, zai yi mana albarka. w23.04 16-17 sakin layi na 13-14

Litinin, 2 ga Yuni

Ji adduꞌata, ya Yahweh, saurari kukana na neman taimako. Zan kira gare ka a lokacin wahalata, gama za ka amsa mini.—Zab. 86:​6, 7.

Sarki Dauda ya fuskanci maƙiya da yawa a rayuarsa, amma a kowane lokaci ne yake adduꞌa ga Jehobah. Dauda yana da tabbacin cewa Jehobah ya ji adduꞌarsa kuma ya amsa. Kai ma za ka iya kasancewa da wannan tabbacin. Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa Jehobah zai iya ba mu hikima da kuma ƙarfin jimre matsaloli. Zai iya yin amfani da ꞌyanꞌuwanmu maza da mata ko waɗanda ba sa bauta masa yanzu ya taimaka mana a wasu hanyoyi. Ko da yake ba a kowane lokaci ne Jehobah zai amsa adduꞌoꞌinmu yadda muka yi tsammani ba, muna da tabbacin cewa zai amsa su. Zai ba mu ainihin abin da muke bukata a lokacin da ya dace. Don haka, ka ci-gaba da yin adduꞌa, ka gaskata cewa zai amsa adduꞌoꞌinka, zai kula da kai yanzu kuma zai “ƙosar da kowane mai rai bisa ga bukatarsa” a sabuwar duniya.—Zab. 145:16. w23.05 8 sakin layi na 4; 13 sakin layi na 17-18

Talata, 3 ga Yuni

Me zan ba Yahweh saboda dukan alheransa gare ni?—Zab. 116:12.

Zai dace ka mai da hankali ga amfanin da za ka samu idan ka cim ma maƙasudinka. Wane amfani ne za ka iya mai da hankali a kai? Idan burinka shi ne ka kyautata yadda kake yin adduꞌa ko karanta Littafi Mai Tsarki, ka yi tunanin yadda hakan zai ƙarfafa dangantakarka da Jehobah. (Zab. 145:​18, 19) Idan kana so ka kasance da halaye masu kyau na Kirista, ka mai da hankali ga yadda hakan zai kyautata dangantakarka da mutane. (Kol. 3:14) Kana iya rubuta duka dalilan da suka sa kake so ka cim ma maƙasudinka. Kuma ka riƙa duba dalilan a kullum. Ƙari ga haka, ka yi abokantaka da waɗanda za su ƙarfafa ka ka cim ma maƙasudinka. (K. Mag. 13:20) Gaskiyar ita ce, a wasu lokuta yakan yi wa dukanmu wuya mu kasance da niyya. Amma hakan yana nufin cewa ba za mu iya yin ƙoƙari mu cim ma maƙasudinmu ba? Aꞌa. Za mu iya yin ƙoƙarin cim ma burinmu ko da ba mu da niyya. Ko da yake yin hakan bai da sauƙi, amma za mu yi farin ciki idan muka iya cim ma su. w23.05 27-28 sakin layi na 5-8

Laraba, 4 ga Yuni

Duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba.—Gal. 6:7.

Idan muka san cewa laifinmu ne, hakan zai sa mu tuba, mu gyara halinmu kuma mu guji maimaita abin da muka yi. Idan muka yi abubuwan nan, za mu ci-gaba da yin tsere don mu sami rai na har abada. Idan ka riga ka yi abin da bai dace ba, me zai taimaka maka? Kar ka yi ta ƙoƙarin ba da hujja, ko kuma ka yi ta damuwa cewa laifinka ne, ko kuma ka ce laifin wasu ne. A maimakon haka, ka yarda cewa ka yi laifi kuma ka yi iya ƙoƙarinka ka yi gyara. Idan abin da ka yi yana damunka, ka yi adduꞌa ga Jehobah, ka gaya masa laifin da ka yi kuma ka roƙi gafara. (Zab. 25:11; 51:​3, 4) Ka ba waɗanda ka yi musu laifi haƙuri, kuma idan da bukata, ka nemi taimakon dattawa. (Yak. 5:​14, 15) Ka ɗauki darasi daga kuskuren da ka yi kuma ka guji maimaita shi. Idan ka yi hakan, ba shakka Jehobah zai yi maka jinƙai kuma zai taimake ka.—Zab. 103:​8-13. w23.08 28-29 sakin layi na 8-9

Alhamis, 5 ga Yuni

Yowash ya aikata abin da ya yi daidai a idon Yahweh, saboda Yehoyida firist yana koya masa.—2 Sar. 12:2.

Yehoyida ya taimaka wa Yowash ya zama mutumin kirki. Don haka da Sarki Yowash yake ƙarami, ya so yin abin da zai faranta wa Jehobah rai. Amma bayan rasuwar Yehoyida, sai Yowash ya bi shawarar dattawan Israꞌila da ba sa ƙaunar Jehobah. (2 Tar. 24:​4, 17, 18) Abin ya ɓata wa Jehobah rai sosai har ya yi ta “aika musu da annabawa su ja musu kunne, duk da haka mutanen suka ƙi ji.” Har ma sun ƙi jin annabi Zakariya ɗan Yehoyida. Zakariya kuwa firist ne a lokacin, kuma shi ɗan ꞌyarꞌuwar mahaifin Yowash ne. Har Sarki Yowash ya sa an kashe Zakariya. (2 Tar. 22:11; 24:​19-22) Yowash bai ci-gaba da jin tsoron Jehobah ba. Dā ma Jehobah ya ce: “Waɗanda suke rena ni za su sha wulaƙanci.” (1 Sam. 2:30) Daga baya sojojin Suriya da ba su da yawa ma, sun ci Yowash da yaƙi, duk da cewa yana tare da sojoji “masu yawan gaske.” Sun kuma bar shi da “rauni mai tsanani sosai.” (2 Tar. 24:​24, 25) Bayin Yowash suka kashe shi don kisan da ya yi wa Zakariya. w23.06 18-19 sakin layi na 16-17

Jumma’a, 6 ga Yuni

Dā kuna a duhu, amma a yanzu, kun sami haske.—Afis. 5:8.

Manzo Bulus ya ɗauki lokaci sosai yana waꞌazi a Afisa. (A. M. 19:​1, 8-10; 20:​20, 21) Bulus yana ƙaunar ꞌyanꞌuwan da ke Afisa sosai, kuma yana so ya taimaka musu su riƙe amincinsu ga Jehobah. Kafin su zama Kiristoci, ꞌyanꞌuwan da ke Afisa sun gaskata da ayyukan sihiri, kuma suna bin koyarwar addinin ƙarya. An san mutanen Afisa da yin lalata da kuma iskanci. Yawancin wasanni da bukukuwan addini da ake yi a manyan wuraren wasa da ke birnin, game da jimaꞌi ne. (Afis. 5:3) Yawancin mutanen garin, akwai su da “rashin kunya,” wato, suna yin abubuwa marasa kyau kuma zuciyarsu ba ta damun su. (Afis. 4:​17-19) Kafin ꞌyanꞌuwan nan da ke Afisa su san abin da ya dace da wanda bai dace ba, su ma suna yin abubuwa marasa kyau, kuma zuciyarsu ba ta damun su. Shi ya sa manzo Bulus ya ce, “Zuciyarsu cike da duhu take. An raba su kuma da rai wanda Allah yake bayarwa.” Amma, wasu mutanen Afisa ba su ci-gaba da kasancewa cikin duhu ba. w24.03 20 sakin layi na 2, 4; 21 sakin layi na 5-6

Asabar, 7 ga Yuni

Masu sa zuciya ga Yahweh za a sabonta ƙarfinsu . . . ba za su gaji ba.—Isha. 40:31.

A matsayinsa na Alƙali, Gideyon yana bukatar ya yi aiki sosai. Saꞌad da Gideyon yake yaƙi da sojojin Midiya da tsakar dare, sojojin sun gudu. Sai Gideyon ya bi su daga Kwarin Jezreel har zuwa Kogin Urdun. (Alƙa. 7:22) Shin Gideyon ya tsaya a Kogin Urdun ne? Aꞌa! Ko da yake ya gaji, shi da mutanensa guda 300 sun tsallake kogin kuma suka ci-gaba da bin su. A ƙarshe, sun kama Midiyanawan kuma suka kakkashe su. (Alƙa. 8:​4-12) Gideyon ya kasance da tabbacin cewa Jehobah zai ƙarfafa shi kuma abin da ya faru ke nan. (Alƙa. 6:​14, 34) Akwai lokacin da Gideyon da mutanensa suke bin sarakunan Midiya da ƙafa, sarakunan kuma suna gudu a kan raƙuma. (Alƙa. 8:​12, 21) Amma da taimakon Jehobah, Israꞌilawan sun kama su kuma suka ci yaƙin. Dattawa ma za su iya dogara ga Jehobah a kowane lokaci, wanda “ba ya gajiya ko ƙarfi ya kāsa masa.” Zai ƙarfafa su a lokacin da suke bukatar hakan.—Isha. 40:​28, 29. w23.06 6 sakin layi na 14, 16

Lahadi, 8 ga Yuni

[Jehobah] ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.—M. Sha. 31:6.

Zuciyarmu za ta iya kafuwa daram, komen matsalolin da muke fama da su. Don haka, ka dogara ga Jehobah. Barak ya yi nasara sosai domin ya bi umurnin Jehobah. Duk da cewa a duk faɗin ƙasar, babu garkuwa ko mashi, Jehobah ya ce ya je ya yaƙi sojojin Kanꞌana da suke ƙarƙashin ja-gorancin Sisera. Sojojin Sisera kuwa suna da kayan yaƙi sosai. (Alƙa. 5:8) Annabiya Deborah ta ce wa Barak ya gangara zuwa filin da Sisera yake. Sisera yana tare da karusansa guda 900. A filin, zai yi wa Israꞌilawa wuya su yaƙi mutanen da ke karusan, domin karusan suna gudu sosai. Barak ya san da hakan, amma ya yi biyayya. Da Israꞌilawan suke gangarawa daga Tudun Tabor, sai Jehobah ya sa aka yi ruwan sama sosai. Hakan ya sa karusan suka maƙale a taɓo, kuma Jehobah ya sa Barak ya ci yaƙin. (Alƙa. 4:​1-7, 10, 13-16) Mu ma Jehobah zai sa mu yi nasara idan muka dogara gare shi kuma muka bi umurnin da yake ba mu ta ƙungiyarsa. w23.07 19 sakin layi na 17-18

Litinin, 9 ga Yuni

Wanda ya jimre har zuwa ƙarshe, zai tsira.—Mat. 24:13.

Muna bukatar mu zama masu haƙuri don mu sami ceto. Kamar yadda bayin Jehobah masu aminci suka yi a dā, mu ma muna bukatar mu yi haƙuri yayin da muke jiran Allah ya cika alkawuransa. (Ibran. 6:​11, 12) Littafi Mai Tsarki ya kwatanta mu da manomi. (Yak. 5:​7, 8) Manomi yakan yi aiki sosai don ya shuka iri kuma ya yi ban ruwa, amma bai san lokacin da irin zai yi girma ba. Don haka, manomin yakan yi haƙuri kuma ya jira da tabbaci cewa zai girbi abin da ya shuka. Haka ma, muna yin ayyukan ibada da ƙwazo duk da cewa ‘ba mu san ranar da Ubangijinmu zai dawo ba.’ (Mat. 24:42) Muna haƙuri kuma muna jira da tabbaci cewa Jehobah zai cika alkawuran da ya yi a lokacin da ya dace. Idan muka daina haƙuri za mu gaji da jira, kuma hakan zai sa mu daina bauta wa Jehobah a hankali a hankali. Ƙari ga haka, za mu iya soma neman abubuwa da muke ganin za su sa mu farin ciki yanzu. Amma idan muna da haƙuri, za mu iya jimre har zuwa ƙarshe kuma mu sami ceto.—Mik. 7:7. w23.08 22 sakin layi na 7

Talata, 10 ga Yuni

An yi yatsun ƙafafun da baƙin ƙarfe gauraye da laka.—Dan. 2:42.

Da muka gwada abin da ke Daniyel 2:​41-43 da wasu annabce-annabce da ke littafin Daniyel da kuma Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna, mun ga cewa Mulkin Burtaniya da Amurka ne ake nufi da tafin ƙafafun gunkin, kuma mulkin ne ya fi iko a duniya a yau. Da yake zancen wannan mulkin, Daniyel ya ce “zai kasance gauraye da ƙarfi da rashin ƙarfi.” Me zai jawo rashin ƙarfin? Mutanen mulkin da aka kwatanta da laƙa, za su hana mulkin amfani da ikon da yake da shi. Abin da Daniyel ya faɗa game da gunkin nan ya koya mana abubuwa da yawa. Mulkin Burtaniya da Amurka ya nuna cewa yana da iko sosai a wasu hanyoyi. Misali, Burtaniya da Amurka suna cikin ƙasashe da suka ci Yaƙin Duniya na 1 da na 2. Sai dai wani abin da ke rage ƙarfin wannan mulkin shi ne yadda talakawansa suke gwagwarmaya da juna kuma suke adawa da gwamnatin. Na biyu, wannan mulkin shi ne zai zama mulki na ƙarshe da zai yi mulkin duniya kafin Mulkin Allah ya halaka dukan mulkokin ꞌyan Adam. w23.08 10-11 sakin layi na 12-13

Laraba, 11 ga Yuni

A cikin damuwata na yi kira ga Yahweh, na yi kukan neman taimako ga Allahna. Daga haikalinsa ya ji muryata.—Zab. 18:6.

Akwai lokutan da Dauda ya gaji sosai saboda matsalolin da yake fuskanta. (Zab. 18:​4, 5) Amma yadda Jehobah ya kula da shi ya sabunta ransa. Kamar dai Jehobah ya bi da abokinsa “wuraren kiwo masu ɗanyar ciyawa” ne da “gefen tafkunan ruwa masu gudu a hankali” don ya samu ya huta. Hakan ya sa Dauda ya sake samun ƙarfin ci-gaba da bauta wa Jehobah da aminci. (Zab. 18:​28-32; 23:2) A yau ma, “ƙaunar Jehobah marar canjawa ne ya sa ba mu halaka ba” duk da matsalolin da muke fuskanta a rayuwa. (Mak. 3:​22, New World Translation; Kol. 1:11) Akwai lokuta da yawa da aka so a kashe Dauda kuma ya yi fama da maƙiya sosai. Amma ya san cewa Jehobah zai kāre shi domin yana ƙaunar sa. Dauda ya san cewa Jehobah yana tare da shi a kowane lokaci, hakan ya ƙarfafa shi. Shi ya sa ya ce: “[Jehobah] ya kuɓutar da ni daga dukan tsorona.” (Zab. 34:4) Ko da yake akwai lokutan da Dauda ya ji tsoro sosai, Ya shawo kan wannan tsoro domin ya san cewa Jehobah yana ƙaunar sa. w24.01 30 sakin layi na 15-17

Alhamis, 12 ga Yuni

Idan masu zunubi sun jarrabce ka, kada ka yarda.—K. Mag. 1:10.

Ka koyi darasi daga shawarwari marasa kyau da Yowash ya yanke. Bayan Babban Firist Yehoyida ya mutu, Yowash ya soma bin abokan banza. (2 Tar. 24:​17, 18) Ya bi shawarar dattawan Yahuda waɗanda ba sa ƙaunar Jehobah. Ya kamata Yowash ya guji mugayen mutanen nan, ko ba haka ba? A maimako, ya bi shawarwari marasa kyau da suka ba shi. Har Yowash ya sa an kashe Zakariya wanda danginsa ne, domin ya ja masa kunne. (2 Tar. 24:​20, 21; Mat. 23:35) Wannan wawanci ne da kuma mugunta! Da farko, Yowash yana ƙaunar Jehobah, amma daga baya ya daina bauta ma Jehobah kuma ya zama mai kisa. A ƙarshe, bayinsa sun kashe shi. (2 Tar. 24:​22-25) Da a ce ya ci gaba da bin umurnan Jehobah, da na waɗanda suke ƙaunar Jehobah, da ba haka rayuwarsa ta ƙare ba! w23.09 9 sakin layi na 6

Jumma’a, 13 ga Yuni

Kada ka ji tsoro.—Luk. 5:10.

Yesu ya san cewa Bitrus zai iya bauta ma Jehobah da aminci. Don haka, Yesu ya gaya wa Bitrus cewa “kada ka ji tsoro.” Yadda Yesu ya yarda da Bitrus ya taimaka wa Bitrus har iya rayuwarsa. Daga baya, Bitrus da ɗanꞌuwansa Andarawus sun bar kamun kifi, kuma sun soma yin waꞌazi tare da Yesu. Don haka, Jehobah ya albarkace su a hanyoyi da dama. (Mar. 1:​16-18) Bitrus ya shaida abubuwa da dama yayin da yake bin Yesu. Ya ga yadda Yesu ya warkar da marasa lafiya, ya kori aljanu, har ma ya ta da matattu. (Mat. 8:​14-17; Mar. 5:​37, 41, 42) Bitrus ya kuma ga wahayi mai ban mamaki game da yadda Yesu zai yi mulki a Mulkin Allah. Bitrus bai manta da abin da ya gani ba har iya rayuwarsa. (Mar. 9:​1-8; 2 Bit. 1:​16-18) Bitrus ya ga abubuwa da dama, da a ce bai bi Yesu ba, da bai gan su ba. Ba mamaki, Bitrus ya yi farin ciki sosai domin ya iya daina tunani marar kyau da yake yi game da kansa, kuma ya iya shaida waɗannan abubuwa! w23.09 21 sakin layi na 4-5

Asabar, 14 ga Yuni

Yesu ya ce masa, “Ba sau bakwai ba, amma dai bakwai sau sabaꞌin.”—Mat. 18:22.

A wasiƙar manzo Bitrus ta fari, Bitrus ya ce: “Ƙauna ta ainihi” takan sa mu “yafe laifofi masu ɗumbun yawa.” (1 Bit. 4:8) Wataƙila Bitrus ya tuna abin da Yesu ya koya masa game da yafewa shekarun baya shi ya sa. A lokacin, Bitrus ya zata shi mutumin kirki ne sosai da ya ce zai yafe wa ɗanꞌuwansa “sau bakwai.” Amma Yesu ya koya masa da mu ma a yau, cewa mu yafe, “ba sau bakwai ba, amma dai bakwai sau sabaꞌin,” wato ba iyaka. (Mat. 18:21) Idan yana maka wuya ka yi hakan, kada ka karaya! Duka bayin Allah ajizai ne, kuma akwai lokacin da bai yi musu sauƙi su yafe ba. Abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne ka yi duk abin da za ka iya don ka yafe ma ɗanꞌuwanka kuma ku zauna lafiya. w23.09 29 sakin layi na 12

Lahadi, 15 ga Yuni

A cikin wahalata na yi kira ga Yahweh, ya kuwa amsa mini.—Yona 2:2.

Saꞌad da Yunana yake cikin kifin, ya tuba kuma ya san cewa Jehobah zai ji adduꞌarsa ya kuma cece shi. Jehobah ya kuwa ceci Yunana, kuma Yunana ya kuɗiri niyyar yin aikin da Jehobah ya ba shi. (Yona 2:10–3:4) Wani lokaci kakan kasa yin adduꞌa ga Jehobah saboda tsananin matsalar da kake ciki? Matsalar takan gajiyar da kai har ka kasa yin nazari? Jehobah ya san irin yanayin da kake ciki. Don haka, ko da gajeriyar adduꞌa ce ka yi, Jehobah zai ba ka ƙarfin da kake bukata. (Afis. 3:20) Idan zafin da kake ji a ranka ya sa ka kasa yin karatu ko nazari, za ka iya sauraran karatun Littafi Mai Tsarki ko kuma na littattafanmu. Wani abu kuma da zai iya taimaka maka shi ne jin waƙoƙinmu, ko ka kalli wani bidiyo a dandalinmu. Jehobah yana so ya ba ka ƙarfin jimrewa. Zai ba ka wannan ƙarfin idan ka yi adduꞌa, kuma ka karanta Littafi Mai Tsarki da sauran abubuwa da yake mana tanadin su. w23.10 13 sakin layi na 6; 14 sakin layi na 9

Litinin, 16 ga Yuni

Ruhu Mai Tsarki yana nuna cewa hanyar shiga ainihin Wuri Mai Tsarki bai buɗu ba tukuna muddin wancan Tenti na farko yana nan tsaye.—Ibran. 9:8.

Yadda aka gina mazauni da haikali da aka gina daga baya kusan irin ɗaya ne. Dukansu suna da ɗakuna biyu, wato “Wuri Mai Tsarki” da “Wuri Mafi Tsarki,” kuma akwai labulen da ya raba tsakaninsu. (Ibran. 9:​2-5; Fit. 26:​31-33) A cikin wuri Mai Tsarki, akwai fitila, da bagaden ƙona turare, da teburi don ajiye gurasa. Firistoci “waɗanda aka keɓe” ne kawai suke da izinin shiga wuri Mai Tsarki don su yi hidima. (L. Ƙid. 3:​3, 7, 10) A cikin wuri Mafi Tsarki kuma, akwai akwatin yarjejeniya (sanduƙin alkawari) wanda yake nuna cewa Jehobah yana wurin. (Fit. 25:​21, 22) Babban firist ne kaɗai zai iya shiga wuri Mafi Tsarki a ranar Dauƙar Alhakin Zunubi. (L. Fir. 16:​2, 17) Yana shiga wurin da jinin dabbobi don ya roƙi gafarar zunubansa da na mutanen. Daga baya, Jehobah ya bayyana maꞌanar abubuwan da ke cikin mazaunin.—Ibran. 9:​6, 7. w23.10 27 sakin layi na 12

Talata, 17 ga Yuni

Ku ƙaunaci juna.—Yoh. 15:17.

Sau da yawa, Kalmar Allah ta yi ta ba mu umurnin nan cewa: “Ku ƙaunaci juna.” (Yoh. 15:12; Rom. 13:8; 1 Tas. 4:9; 1 Bit. 1:22; 1 Yoh. 4:11) Amma ba a iya ganin ƙauna da ido domin a zuciya take. Tun da haka ne, ta yaya za mu nuna wa ꞌyanꞌuwanmu cewa muna ƙaunar su? Ta furucinmu da ayyukanmu ne. Akwai hanyoyi dabam-dabam da za mu iya nuna wa ꞌyanꞌuwanmu cewa muna ƙaunar su. Misali, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowannenku ya dinga faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya.” (Zak. 8:16) “Ku yi zaman lafiya da juna.” (Mar. 9:50) “Kowa ya yi saurin girmama wani fiye da kansa.” (Rom. 12:10) “Ku karɓi juna hannu biyu-biyu.” (Rom. 15:7) Mu dinga “gafarta wa juna.” (Kol. 3:13) “Ku taimaki juna ta wajen ɗaukar wahalar juna.” (Gal. 6:2) “Ku ƙarfafa juna, ku yi ta gina juna.” (1 Tas. 5:11) Ku “yi wa juna adduꞌa.”—Yak. 5:16. w23.11 9 sakin layi na 7-8

Laraba, 18 ga Yuni

Ku yi farin ciki a cikin sa zuciyarku.—Rom. 12:12.

Kowace rana, muna yanke shawarwarin da suke bukatar mu nuna bangaskiya sosai. Alal misali, muna yanke shawarwari game da abokanmu, da nishaɗin da za mu yi, da makaranta, da aure, da renon yara, da aikinmu. Zai dace mu tambayi kanmu cewa: ‘Shin shawarwarina suna nuna ina da tabbaci cewa nan ba da daɗewa ba, Allah zai mai da duniya ta zama aljanna? Ko dai ina yin abubuwa yadda waɗanda ba su gaskata cewa za su yi rayuwa har abada ba suke yi?’ (Mat. 6:​19, 20; Luk. 12:​16-21) Idan muka ƙarfafa bangaskiyarmu cewa nan ba da daɗewa ba sabuwar duniya za ta zo, hakan zai taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau. Ƙari ga haka, muna fuskantar matsalolin da suke bukatar mu nuna bangaskiya sosai. Mukan yi fama da tsanantawa da rashin lafiya mai tsanani ko kuma wasu abubuwan da za su sa mu yi sanyin gwiwa. Da farko, za mu ga kamar za mu iya jimre matsalar nan. Amma idan matsalar ta ƙi tafiya, sai da bangaskiya sosai ne za mu iya jimre ta kuma mu ci-gaba da bauta wa Jehobah da farin ciki.—1 Bit. 1:​6, 7. w23.04 27 sakin layi na 4-5

Alhamis, 19 ga Yuni

Ku yi ta yin adduꞌa babu fasawa.—1 Tas. 5:17.

Jehobah yana so mu yi abubuwan da za su jitu da adduꞌarmu. Alal misali, wani ɗanꞌuwa zai iya roƙan Jehobah ya taimaka masa ya sami izini daga wurin aiki don ya iya zuwa taron yanki. Ta yaya Jehobah zai amsa adduꞌar nan? Jehobah zai iya ba wa ɗanꞌuwan ƙarfin zuciya don ya iya zuwa ya sami shugaban aikinsa. Amma ɗanꞌuwan ne da kansa zai je ya nemi izinin. Mai yiwuwa zai bukaci ya roƙi shugaban aikinsa sau da yawa. Zai ma iya gaya masa cewa zai yi aikin a wata rana dabam ko ya ce a cire kuɗin da ya kamata a biya shi a ranakun daga albashinsa. Jehobah yana son mu ci-gaba da yin adduꞌa a kan damuwoyinmu. Yesu ya bayyana cewa ba za a ba mu wasu abubuwan da muka roƙa nan take ba. (Luk. 11:9) Don haka, kada mu gaji da yin adduꞌa. Mu yi adduꞌa da dukan zuciyarmu, kuma mu yi hakan babu fasawa. (Luk. 18:​1-7) Idan muka yi haka, Jehobah zai ga cewa abin yana da muhimmanci a gare mu. Ƙari ga haka, zai nuna cewa mun san Jehobah zai taimaka mana. w23.11 22 sakin layi na 10-11

Jumma’a, 20 ga Yuni

Sa zuciyar nan ba za ta zama abin banza ba ko kaɗan.—Rom. 5:5.

Jehobah ya yi wa Ibrahim alkawari cewa ta wurin sa, dukan ƙabilun duniya za su samu albarka. (Far. 15:5; 22:18) Da yake Ibrahim mutum ne mai bangaskiya sosai, ya gaskata cewa alkawarin Jehobah zai cika. Amma, har lokacin da Ibrahim ya kai shekaru ɗari kuma shekarun matarsa sun kai casaꞌin, Ibrahim bai samu ɗa ba. (Far. 21:​1-7) Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “[Ibrahim] ya ci gaba da sa zuciya, yana ba da gaskiya har ya zama ‘uban kabilu masu yawa.’ Wannan kuwa bisa ga alkawarin da aka yi masa ne.” (Rom. 4:18) Hakika, ka san cewa abin da Ibrahim ya sa zuciyarsa a kai ya faru. A-kwana-a-tashi Ibrahim ya samu ɗa mai suna Ishaku. Amma, me ya tabbatar wa Ibrahim cewa Jehobah zai cika alkawarin nan? Da yake Ibrahim aminin Jehobah ne, ‘ya kasance da cikakken tabbaci’ cewa Allah zai cika alkawarinsa. (Rom. 4:21) Saboda bangaskiyar Ibrahim, Jehobah ya amince da shi kuma ya ce shi mai adalci ne.—Yak. 2:23. w23.12 8 sakin layi na 1-2

Asabar, 21 ga Yuni

Wanda ya isa a amince da shi a ƙaramin abu, za a iya amince da shi a babban abu ma. Wanda yake marar gaskiya a ƙaramin abu, zai iya zama marar gaskiya ma a babban abu.—Luk. 16:10.

Saurayin da za a iya yarda da shi yana yin ayyukan da aka ba shi da kyau kuma da himma. Ka yi laꞌakari da misalin Yesu. Bai taɓa yin wasa da aikin da aka ba shi ba. A maimakon haka, ya yi dukan ayyukan da Jehobah ya ba shi ko a lokacin da yin hakan yake da wuya. Yana ƙaunar mutane, musamman mabiyansa, har ya ba da ransa a madadin su. (Yoh. 13:1) Ka yi koyi da Yesu kuma ka yi iya ƙoƙarinka ka yi dukan aikin da aka ba ka. Idan kana shakkar yadda za ka yi aikin, ka nuna sauƙin kai kuma ka roƙi ꞌyanꞌuwan da suka manyanta su taimaka maka. Kada ka ce daidai abin da ake bukata ne kawai za ka yi. (Rom. 12:11) A maimakon haka, ka yi aikin gabaki ɗaya kuma ka yi shi ‘kamar ga Ubangiji ne kake yi wa, ba ga mutum ba.’ (Kol. 3:23) Hakika, kai ma za ka iya yin kuskure, don haka ka san kasawarka kuma ka amince da kurakuranka.—K. Mag. 11:2. w23.12 26 sakin layi na 8

Lahadi, 22 ga Yuni

Mai albarka ne wanda yake dogara ga Yahweh.—Irm. 17:7.

Muna farin ciki sosai idan muka ga wasu sun yi baftisma kuma suka zama ꞌyan iyalin Jehobah, domin babban gata ne mutum ya kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Shi ya sa mun yarda da abin da Dauda ya rubuta cewa: ‘Masu albarka ne waɗanda [Jehobah] ya zaɓa, waɗanda ya jawo su kusa su kasance a filin Gidansa.’ (Zab. 65:4) Amma ba kowa ne Jehobah yake jawowa gare shi ba. Waɗanda suke kusantar Jehobah ne shi ma yake kusanta. (Yak. 4:8) Idan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma, za ka iya kasance da tabbacin cewa zai ‘zubo maka albarku masu yawan gaske.’ (Mal. 3:10; Irm. 17:8) Idan mutum ya yi baftisma, ya fara amfani da rayuwarsa a hidimar Jehobah ke nan. Kana bukatar ka yi iya ƙoƙarinka ka cika alkawarin da ka yi ma Jehobah kuma ka riƙe amincinka gareshi ko da kana fuskantar jarrabawa ko kana fama da tsanantawa. (M. Wa. 5:​4, 5) Tun da ka zama mabiyin Yesu, kana bukatar ka yi koyi da halayensa kuma ka yi iya ƙoƙarinka ka bi umurninsa.—Mat. 28:​19, 20; 1 Bit. 2:21. w24.03 8 sakin layi na 1-3

Litinin, 23 ga Yuni

Mutum zai bar babansa da mamarsa ya manne wa matarsa.—Far. 2:24.

Amma idan ba kwa jin daɗin kasancewa tare kuma fa? Me za ku yi? Ga misali, idan aka hura wuta, ba nan take ne wutar take fara ci sosai ba. Akan soma ne da ƙananan itace. A hankali sai a dinga ƙara manyan itace har wutar ta fara ci sosai. Haka ma, zai fi alheri idan kuka soma da yin abubuwa tare na ɗan ƙanƙanin lokaci kowace rana. Ku dai tabbata cewa abu ne da ku biyun kuke son yi. (Yak. 3:18) Idan kuka soma da-kaɗan-da-kaɗan, ƙila ku ga ƙaunar da kuke yi wa juna ta ƙaru. Bangirma yana da muhimmanci a zaman aure. Kamar iska yake. Idan babu iska, wuta za ta mutu. Haka ma, idan maꞌaurata ba sa girmama juna, ƙaunar da take tsakaninsu za ta yi saurin yin sanyi. Amma idan maꞌaurata suna ƙoƙari su girmama juna, hakan zai taimaka musu su ci-gaba da ƙaunar juna. Amma fa, ba kai ne za ka ce kana girmama matarka ba, ko ki ce kina girmama mijinki ba. Abin shi ne, matarka ko mijinki yana ji cewa kina girmama shi kuwa? w23.05 22 sakin layi na 9; 24 sakin layi na 14-15

Talata, 24 ga Yuni

Saꞌad da damuwoyi sukan yi mini yawa, taꞌaziyarka takan ƙarfafa raina.—Zab. 94:19.

A Littafi Mai Tsarki, akwai wasu bayin Allah masu aminci da suka faɗi lokutan da suka damu kuma suka ji tsoro don maƙiyansu da dai sauransu. (Zab. 18:4; 55:​1, 5) Mu ma muna iya fuskantar hamayya daga ꞌyan makarantarmu ko ꞌyan iyalinmu ko kuma hukumomin gwamnati. Za mu iya jin tsoro cewa za mu mutu saboda cutar da muke fama da ita. A irin wannan yanayi, mukan zama kamar yaro kuma mu rasa na yi. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana a irin wannan yanayin? Yana taꞌazantar da mu kuma ya ƙarfafa mu. Don haka, ka riƙa yin adduꞌa ga Jehobah da kuma karanta Kalmarsa. (Zab. 77:​1, 12-14) Hakan zai sa ka yi saurin neman taimakonsa saꞌad da kake cikin matsala. Ka gaya masa damuwarka, da kuma abin da kake jin tsoron sa. Bayan haka, ka saurare shi ta wajen karanta Kalmarsa, saꞌan nan za ka ga yadda zai ƙarfafa ka.—Zab. 119:28. w24.01 24-25 sakin layi na 14-16

Laraba, 25 ga Yuni

Allah shi ne yake . . . sa ku yi niyya ku kuma yi aiki bisa ga kyakkyawan nufinsa.—Filib. 2:13.

Yana da muhimmanci sosai ka kasance da niyyar cika maƙasudinka. Idan kana da niyya, za ka yi iya ƙoƙarinka don ka cika maƙasudin. Kuma idan muna da niyya sosai, zai taimaka mana mu iya cim ma maƙasudinmu. To, mene ne za ka iya yi don ka daɗa kasancewa da niyya? Ka roƙi Allah ya ƙara maka niyya. Jehobah zai ba ka ruhunsa mai tsarki don ya taimaka maka ka iya cim ma maƙasudinka. A wasu lokuta, mukan kafa maƙasudi domin mun san cewa abu ne da ya kamata mu yi kuma ya dace. Amma mai yiwuwa ba mu da niyyar cika maƙasudin. Ka yi tunani a kan abubuwan da Jehobah ya yi maka. (Zab. 143:5) Manzo Bulus ya yi tunani a kan alherin da Jehobah ya yi masa kuma hakan ya ƙarfafa shi ya daɗa yin iya ƙoƙarinsa a hidimarsa ga Jehobah. (1 Kor. 15:​9, 10; 1 Tim. 1:​12-14) Haka ma, idan ka ci-gaba da yin tunani a kan abubuwan da Jehobah ya yi maka, za ka kasance da niyya.—Zab. 116:12. w23.05 27 sakin layi na 3-5

Alhamis, 26 ga Yuni

Yabi Sunan Yahweh!—Zab. 113:1.

Za mu sa Jehobah farin ciki idan muka yabi sunansa. (Zab. 119:108) Amma hakan yana nufin cewa Jehobah yana kamar ꞌyan Adam ne da suke so a yaba musu domin su sami ƙarfafa? Aꞌa. Idan muka yabi Ubanmu na sama, muna taimaka wajen nuna cewa abin da Shaiɗan ya faɗa game da mu ƙarya ne. Shaiɗan ya ce babu ɗan Adam da zai goyi bayan Jehobah da gaske. Ya ce ba ko ɗayanmu da zai riƙe amincinsa idan ya fuskanci jarrabawa. Wato idan muka ga cewa daina bauta wa Allah zai amfane mu, dukanmu za mu daina bauta masa. (Ayu. 1:​9-11; 2:4) Amma Ayuba ya nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. Kai ma za ka riƙe amincinka ga Allah kamar Ayuba? Dukanmu za mu iya ɗaukaka Ubanmu na sama kuma mu sa shi farin ciki ta wurin bauta masa da aminci. (K. Mag. 27:11) Yin hakan babban gata ne. w24.02 8-9 sakin layi na 3-5

Jumma’a, 27 ga Yuni

Ku gaskata da annabawansa, za ku ci nasara.—2 Tar. 20:20.

Bayan zamanin su Musa da Joshua, Jehobah ya naɗa alƙalai su ja-goranci mutanensa. Da Israꞌilawan suka soma samun sarakuna, Jehobah ya naɗa annabawa da za su riƙa yi musu ja-goranci. Sarakuna masu aminci sun bi ja-gorancin annabawan. Alal misali, Sarki Dauda ya bi gargaɗin da annabi Nathan ya yi masa. (2 Sam. 12:​7, 13; 1 Tar. 17:​3, 4) Sarki Yehoshafat ya bi shawarar da annabi Yahaziyel ya ba shi, kuma ya ƙarfafa mutanen su “gaskata da annabawan [Allah].” (2 Tar. 20:​14, 15) Da Sarki Hezekiya yake cikin yanayi mai wuya, ya nemi shawarar annabi Ishaya. (Isha. 37:​1-6) A duk lokacin da sarakunan suka bi ja-gorancin Jehobah, suna samun albarka kuma hakan na kāre alꞌummar. (2 Tar. 20:​29, 30; 32:22) Alamun nan su sa mutanen su gaskata cewa Jehobah yana amfani da annabawa don ya yi musu ja-goranci. w24.02 21 sakin layi na 8

Asabar, 28 ga Yuni

Kada ku haɗa kai da su.—Afis. 5:7.

Shaiɗan yana so mu yi abokantaka da mutanen da za su sa ya yi mana wuya mu bi ƙaꞌidodin Jehobah. Ya kamata mu fi ꞌyanꞌuwan nan da suke Afisa yin hattara, domin a yau za mu iya yin abokantaka da mutane ta dandalin sada zumunta ba sai muna tare da su a zahiri ba. Ya kamata mu yi hattara don kar mu yi irin tunanin mutanen duniyar nan, cewa yin lalata ba laifi ba ne. Don mun san cewa zunubi ne babba. (Afis. 4:​19, 20) Zai dace kowannenmu ya tambayi kansa cewa: ‘Ina guje wa yin abokantaka da waɗanda muke aiki tare, ko ꞌyan ajinmu, ko duk wani mutum da ba ya bin ƙaꞌidodin Jehobah? Nakan tsaya kafa biyu kuma in yi abin da Jehobah yake so ko da mutane za su ce na cika nacewa a kan abin da ba kome ba ne?’ Kuma kamar yadda 2 Timoti 2:​20-22 sun ce, muna bukatar mu yi hankali saꞌad da muke zaɓan waɗanda za mu yi abokantaka da su ko a cikin Ikilisiya. Mu tuna cewa akwai wasu a ikilisiya da ba za su taimaka mana mu riƙe amincinmu ba. w24.03 22-23 sakin layi na 11-12

Lahadi, 29 ga Yuni

Ubangiji mai jinƙai ne.—Yak. 5:11.

Ka taɓa tunanin yadda Jehobah yake? Ko da yake ba ma iya ganin Jehobah, Littafi Mai Tsarki ya kwatanta mana yadda yake a hanyoyi da yawa. Alal misali, an kwatanta shi da ‘haske’ da ‘garkuwa’ da kuma ‘wuta mai cinyewa.’ (Zab. 84:11; Ibran. 12:29) An kuma kwatanta shi da dutsen saffaya mai daraja, da ƙarfen da aka goge kuma yana ƙyalli, da kuma bakan gizo da ke haskakawa. (Ezek. 1:​26-28) Da yake ba mu taɓa ganin Jehobah ba, ƙila yana yi mana wuya mu yarda cewa yana ƙaunar mu. Wasu kuma abin da ya taɓa faruwa a rayuwarsu ne ya sa suke ganin ba zai yiwu Jehobah ya ƙaunace su ba. Jehobah ya san dukan abubuwan nan kuma ya san cewa zai iya yi mana wuya mu yarda da ƙaunarsa a gare mu. Shi ya sa ya gaya mana halayensa masu kyau a Littafi Mai Tsarki. Hali mafi girma da Jehobah yake da shi, shi ne ƙauna. Littafi Mai Tsarki ya ce “Allah ƙauna ne.” (1 Yoh. 4:8) Duk abin da Jehobah yake yi saboda ƙaunarsa ne. Allah yana da ƙauna sosai shi ya sa yake nuna ƙauna ga kowa, har da waɗanda ba sa ƙaunar sa.—Mat. 5:​44, 45. w24.01 26 sakin layi na 1-3

Litinin, 30 ga Yuni

Ya yi musu magana daga ƙunshin girgije.—Zab. 99:7.

Jehobah ya naɗa Musa ya ja-goranci alꞌummar Israꞌila saꞌad da suke barin ƙasar Masar kuma ya tanada musu ƙunshin girgije da rana da kuma ƙunshin wuta da dare don ya tabbatar musu cewa zai yi musu ja-goranci. (Fit. 13:21) Musa ya bi wannan ƙunshin girgije, kuma girgijen ya ja-gorance shi da Israꞌilawan zuwa Jar Teku. Mutanen sun ji tsoro sosai da suka ga cewa babu hanyar da za su bi, kuma ga sojojin Masar a bayansu. Amma hakan ba kuskure ba ne. Domin Jehobah da kansa ne ya yi amfani da Musa don ya ja-goranci mutanensa zuwa Jar Tekun. (Fit. 14:2) Sai Allah ya cece su a hanya mai ban alꞌajibi. (Fit. 14:​26-28) Musa ya yi shekaru 40 yana bin girgijen nan don ya ja-goranci alꞌummar Israꞌila saꞌad da suke tafiya a cikin daji. (Fit. 33:​7, 9, 10) Jehobah yakan yi magana da Musa daga ƙunshin girgijen, sai Musa kuma ya gaya wa mutanen abin da Jehobah ya faɗa. Akwai abubuwa da yawa da ya kamata su tabbatar wa Israꞌilawan cewa Jehobah ne yake amfani da Musa ya yi musu ja-goranci. w24.02 21 sakin layi na 4-5

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba