Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w24 Maris pp. 8-13
  • Ka Ci-gaba da Bin Yesu Bayan Ka Yi Baftisma

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Ci-gaba da Bin Yesu Bayan Ka Yi Baftisma
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA CI-GABA DA BIN YESU KOMEN MATSALOLI DA JARRABAWA
  • ABUBUWAN DA ZA SU TAIMAKE KA KA CI-GABA DA BIN YESU
  • “KU GWADA KANKU . . . KU DINGA AUNA KANKU”
  • Ka Yi Shirin Yin Alkawarin Bauta wa Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Tuna Cewa Jehobah “Allah Mai Rai” Ne
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
w24 Maris pp. 8-13

TALIFIN NAZARI NA 10

WAƘA TA 13 Mu Riƙa Bin Misalin Yesu

Ka Ci-gaba da Bin Yesu Bayan Ka Yi Baftisma

“Duk mai so ya bi ni, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki [gungumen azabarsa] kowace rana, ya bi ni.”—LUK. 9:23.

ABIN DA ZA MU KOYA

Wannan talifin zai taimaka wa dukanmu mu ga yadda za mu cika alkawarin da muka yi na bauta wa Jehobah a dukan rayuwarmu. Zai kuma taimaka ma waɗanda ba su daɗe da yin baftisma ba su ci-gaba da riƙe amincinsu ga Jehobah.

1-2. Waɗanne albarku ne mutum zai samu bayan ya yi baftisma?

MUNA farin ciki sosai idan muka ga wasu sun yi baftisma kuma suka zama ꞌyan iyalin Jehobah, domin babban gata ne mutum ya kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Shi ya sa mun yarda da abin da Dauda ya rubuta cewa: ‘Masu albarka ne waɗanda [Jehobah] ya zaɓa, waɗanda ya jawo su kusa su kasance a filin Gidansa.’—Zab. 65:4.

2 Amma ba kowa ne Jehobah yake jawowa gareshi ba. Kamar yadda muka tattauna a talifin da ya gabata, waɗanda suke kusantar Jehobah ne shi ma yake kusanta. (Yak. 4:8) Idan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma, za ka kusaci Jehobah a hanya ta musamman. Kuma za ka iya kasance da tabbacin cewa zai ‘zubo maka albarku masu yawan gaske.’—Mal. 3:10; Irm. 17:7, 8.

3. Wane hakki mai nauyi ne Kiristoci da suka yi baftisma suke da shi? (Mai-Waꞌazi 5:4, 5)

3 Idan mutum ya yi baftisma, ya fara amfani da rayuwarsa a hidimar Jehobah ke nan. Domin bayan ka yi baftisma, kana bukatar ka yi iya ƙoƙarinka ka cika alkawarin da ka yi ma Jehobah kuma ka riƙe amincinka gareshi ko da kana fuskantar jarrabawa ko kana fama da tsanantawa. (Karanta Mai-Wa’azi 5:4, 5.) Tun da ka zama mabiyin Yesu, kana bukatar ka yi koyi da halayensa kuma ka yi iya ƙoƙarinka ka bi umurninsa. (Mat. 28:19, 20; 1 Bit. 2:21) Abin da wannan talifin zai taimaka maka ka yi ke nan.

KA CI-GABA DA BIN YESU KOMEN MATSALOLI DA JARRABAWA

4. Mene ne Yesu yake nufi da ya ce mabiyansa za su ɗauki gungumen azaba? (Luka 9:23)

4 Bayan ka yi baftisma, rayuwa ba za ta kasance maka da sauƙi ba. Yesu ya gaya mana cewa mabiyansa za su ɗauki gungumen azaba, ya ma ce za su yi hakan “kowace rana.” (Luk. 9:23) Shin Yesu yana nufin cewa mabiyansa za su sha wahala a kowane lokaci ne? Aꞌa. Abin da yake nufi shi ne, ban da albarkun da Jehobah zai yi mana, za mu fuskanci matsaloli dabam-dabam. Wasu matsalolin ma, za su ci mana tuwo a ƙwarya.—2 Tim. 3:12.

5. Wane alkawari ne Yesu ya yi ma waɗanda suka yi sadaukarwa dominsa?

5 Mai yiwuwa ka riga ka fuskanci tsanantawa daga wurin ꞌyan iyalinku ko kuma ka sadaukar da dukiya ko wani abu don ka fi mai da hankali a kan hidimarka ga Jehobah. (Mat. 6:33) Idan haka ne, ka kasance da tabbacin cewa Jehobah yana lura da dukan abubuwan da kake yi dominsa. (Ibran. 6:10) Yesu ya ce: “Gaskiya ina gaya muku, wanda ya bar gidansa, ko ꞌyanꞌuwansa, ko mamarsa, ko babansa, ko ꞌyaꞌyansa, ko gonakinsa, saboda ni da kuma saboda labari mai daɗi, abin da zai samu a zamanin nan ma, zai fi sau ɗari, na gidaje, da ꞌyanꞌuwa, da iyaye, da ꞌyaꞌya, da gonaki, amma tare da tsanani. Saꞌan nan a zamani mai zuwa, sai rai na har abada.” (Mar. 10:29, 30) Mai yiwuwa ka ga yadda waɗannan kalaman Yesu suka cika a rayuwarka. Hakika, albarkun da ka samu sun ma fi duk wata sadaukarwa da ka yi.—Zab. 37:4.

6. Me ya sa kake bukatar ka ci-gaba da guje wa “shaꞌawa ta jiki” bayan ka yi baftisma?

6 Ban da haka, bayan ka yi baftisma, kana bukatar ka dage don kar ka bi “shaꞌawa ta jiki.” (1 Yoh. 2:16) Domin kai ma ajizi ne kamar sauran mutane. Wasu lokuta ma, ƙila ka ji kamar manzo Bulus, wanda ya ce: “Gama a ciki-cikin zuciyata, na amince da Koyarwar Allah, amma a cikin gaɓoɓina ina ganin wata ƙaꞌida dabam wadda take yaƙi da ƙaꞌidar da hankalina ya ɗauka. Wannan kuwa ta ɗaure ni ga ƙaꞌidar nan ta zunubi wadda take zama a cikin gaɓoɓina.” (Rom. 7:22, 23) Hakika, guje wa abin da zai sa ka yi zunubi bai da sauƙi. Hakan yana iya sa ka karaya. Amma idan ka tuna da alkawarin da ka yi ma Jehobah, hakan zai taimaka maka ka ci-gaba da guje wa shaꞌawoyin nan. Ta yaya alkawarin bauta wa Jehobah da ka yi zai taimaka maka idan ka fuskanci jarrabawa?

7. Ta yaya alkawarin da ka yi na bauta wa Jehobah zai taimaka maka ka riƙe amincinka?

7 Idan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah, ka ƙi kanka ke nan. Hakan yana nufin za ka ƙi duk wani abu ko wata shaꞌawa da za ta ɓata wa Jehobah rai. (Mat. 16:24) Don haka, idan ka fuskanci wata jarraba, ba za ka ɓata lokaci kana tunanin abin da ya kamata ka yi ba, domin ka riga ka yanke shawara cewa za ka riƙe amincinka ga Jehobah. Ba za ka ja da baya ba amma za ka zama kamar Ayuba. Duk da cewa ya fuskanci matsaloli masu wuyan gaske, ya ce: “Har in mutu, ba zan rabu da amincina ba.”—Ayu. 27:5, New World Translation.

8. Ta yaya yin tunani a kan alkawarin bauta wa Jehobah da ka yi zai taimaka maka ka guje wa jarrabar yin zunubi?

8 Idan kana yawan tunani a kan alkawarin bauta wa Jehobah da ka yi, za ka sami ƙarfin guje wa jarrabawa. Alal misali, ba za ka yi abin da zai nuna cewa kana shaꞌawar matar wani ba, ko kina shaꞌawar mijin wata ba, domin kin riga ko ka riga ka yi wa Jehobah alkawari cewa ba za ka taɓa yin abu kamar haka ba. Kuma daga baya, ba za ka yi fama da wahalolin da shaꞌawoyin banza suke jawowa ba. Za ka “juya” daga “hanyar mugaye.”—K. Mag. 4:14, 15.

9. Ta yaya yin tunani a kan alkawarin bauta wa Jehobah da ka yi zai taimaka maka ka sa yin nufinsa farko a rayuwarka?

9 Idan ka samu aiki da zai sa ka riƙa fasa taro fa? Hakika, ka san abin da za ka yi. Tun kafin ka sami irin aikin nan, ka riga ka san cewa ba za ka yi aikin da zai hana ka zuwa taro ba. Don haka, ba za ka karɓi irin aikin nan kuma ka ce za ka yi ƙoƙarin sa nufin Jehobah farko a rayuwarka ba. Wani abin da zai taimaka maka shi ne misalin Yesu. Yesu yana so ya faranta wa Ubansa rai a kowane lokaci. Kamar Yesu, ka yi saurin ƙin duk wani abin da zai ɓata wa Allah rai domin ka riga ka yi masa alkawari.—Mat. 4:10; Yoh. 8:29.

10. Ta yaya Jehobah zai taimaka maka ka ci-gaba da bin Yesu bayan ka yi baftisma?

10 Gaskiyar ita ce, matsaloli da jarrabawa suna ba ka damar nuna cewa kana so ka ci-gaba da bin Yesu. Yayin da kake hakan, ka kasance da tabbacin cewa Jehobah zai taimaka maka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah mai aminci ne, ba zai bari a gwada ku fiye da ƙarfinku ba, amma game da gwajin, zai buɗe hanyar tsira yadda za ku iya jimrewa.”—1 Kor. 10:13.

ABUBUWAN DA ZA SU TAIMAKE KA KA CI-GABA DA BIN YESU

11. Waɗanne abubuwa ne za su taimaka maka ka ci-gaba da bin Yesu? (Ka kuma duba hoton.)

11 Yesu ya bauta wa Jehobah da dukan zuciyarsa, bai yi wasa da yin adduꞌa ba kuma hakan ya sa ya kusaci Jehobah sosai. (Luk. 6:12) Kai ma, wani abin da zai taimaka maka ka ci-gaba da bin Yesu bayan ka yi baftisma shi ne, ka riƙa yin abubuwan da za su sa ka kusaci Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duk inda muka kai, mu ci-gaba daga nan.” (Filib. 3:16) A wasu lokuta, za ka ji labaran ꞌyanꞌuwa maza da mata da suka ƙara ƙwazo a hidimarsu ga Jehobah. Mai yiwuwa sun je Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki ko kuma sun je inda ake bukatar masu shela. Wannan maƙasudi ne mai kyau da kai ma za ka iya kafawa idan zai yiwu. A kowane lokaci, bayin Jehobah suna neman hanyoyin da za su ƙara ƙwazo a hidimarsu. (A. M. 16:9) Amma, idan ba za ka iya yin hakan a yanzu ba fa? Kada ka ɗauka cewa waɗanda suke hakan sun fi ka daraja. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, ka ci-gaba da jimrewa. (Mat. 10:22) Ka riƙa tuna cewa abin da yake sa Jehobah farin ciki shi ne, hidimar da kake masa iya ƙarfinka. Hakan ne zai taimaka maka ka ci-gaba da bin Yesu bayan ka yi baftisma.—Zab. 26:1.

An gama yi ma wata matashiya baftisma kuma tana farin ciki. Kananan hotuna: 1. Tana waꞌazi. 2. Ta je Makarantar Masu Yada Bisharar Mulki. 3. Tana hada wayoyi a inda ake wani gini na kungiyarmu.

Bayan ka yi baftisma, ka riƙa yin abubuwan da za su sa ka ƙara kusantar Jehobah (Ka duba sakin layi na 11)


12-13. Mene ne za ka yi idan ƙwazon da kake yi ya soma raguwa? (1 Korintiyawa 9:16, 17) (Ka kuma duba akwatin nan, “Ka Ci-gaba da Yin Tseren.”)

12 Amma, me za ka yi idan ka lura cewa ba daga zuciyarka ne kake yin adduꞌa ba? Idan ba ka jin daɗin yin waꞌazi ko ba ka karanta Littafi Mai Tsarki kamar yadda kake yi a dā ba fa? Idan hakan ya faru da kai bayan ka yi baftisma kada ka ɗauka cewa ruhun Jehobah ba ya tare da kai. Da yake kai ajizi ne, yadda kake ji yakan canja a wasu lokuta. Idan ƙwazon da kake yi ya soma raguwa, ka yi tunani a kan misalin manzo Bulus. Ko da yake Bulus ya yi iya ƙoƙarinsa ya yi koyi da Yesu, ya san cewa a wasu lokuta ba zai yi marmarin yin abubuwan da ya kamata ya yi ba. (Karanta 1 Korintiyawa 9:16, 17.) Ya ce: “Da yake ba domin ganin dama nake yi ba, an ba ni amana ke nan.” Abin da Bulus ya faɗa ya nuna cewa yana da burin cika hidimarsa ko da ba da son ransa ba ne.

13 Kamar Bulus, kada ka yanke shawarwari bisa ga yadda kake ji a lokacin. Ka kasance da burin yin abin da ya dace ko da ba ka marmarinsa. Idan ka ci-gaba da yin abin da ya dace, a-kwana-a-tashi yadda kake ji zai canja. Amma kafin nan, ayyukan ibada da kake yi za su taimaka maka ka ci-gaba da bin Yesu. Ƙari ga haka, idan ꞌyanꞌuwa suka ga yadda kake ci-gaba da bauta wa Jehobah, hakan zai ƙarfafa su.—1 Tas. 5:11.

Ka Ci-gaba da Yin Tseren

Hotuna: 1. Wani dan tsere yana cin abinci mai gina jiki; wani karamin hoto ya nuna wani danꞌuwa yana karanta Littafi Mai Tsarki. 2. Dan tseren yana motsa jiki; karamin hoton ya nuna danꞌuwan yana yin kalami a taro. 3. Dan tseren yana gudu; karamin hoton ya nuna danꞌuwan yana waꞌazi da amalanke.

Idan har mai yin tsere yana so ya ci-gaba da yin tseren, yana bukatar ya yi abubuwan da za su gina jikinsa. Hakazalika, idan kana so ka ci-gaba da bauta wa Jehobah bayan ka yi baftisma, kana bukatar ka ci-gaba da yin abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarka da shi.

“KU GWADA KANKU . . . KU DINGA AUNA KANKU”

14. Mene ne ya kamata ka bincika a-kai-a-kai, kuma me ya sa? (2 Korintiyawa 13:5)

14 Bayan ka yi baftisma, zai dace ka riƙa bincika kanka a-kai-a-kai. (Karanta 2 Korintiyawa 13:5.) Ka riƙa dubawa ko har yanzu kana yin adduꞌa a kowace rana, da karanta Littafi Mai Tsarki, da zuwa taro, da kuma yin waꞌazi. Ka yi iya ƙoƙarinka ka inganta yadda kake yin abubuwan nan. Alal misali, ka yi wa kanka tambayoyin nan: ‘Zan iya bayyana wa mutane muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki? Akwai abubuwan da zan yi da za su sa in ƙara jin daɗin yin waꞌazi? Idan ina adduꞌa, nakan faɗi ainihin abin da nake bukata? Adduꞌata tana nuna cewa na dogara ga Jehobah? Ina zuwa taro a-kai-a-kai? Mene ne zan yi don in ƙara mai da hankali kuma in yi kalami a taro?’

15-16. Mene ne ka koya daga yadda wani ɗanꞌuwa ya guje wa jarraba?

15 Ƙari ga haka, yana da muhimmanci ka san inda kake da kasawa. Ga abin da wani ɗanꞌuwa mai suna Robert ya ce game da wannan batun. Ya ce: “Saꞌad da nake wajen shekara 20, akwai wani aiki da nake yi. Wata rana, wata da nake aiki da ita ta ce in zo gidanta. Ta ce mu kaɗai ne za mu kasance a gidan kuma za mu ‘ji daɗin kanmu.’ Da farko dai, na ji kunyar gaya mata gaskiya, sai na yi ta ba ta wasu hujjoji. Amma daga baya na gaya mata ba zan zo ba kuma na gaya mata dalilin da ya sa.” Robert ya guje wa jarrabawar nan, kuma muna yaba masa. Amma, daga baya ya yi tunani a kan abin da ya faru, kuma ya gano cewa akwai matsala a yadda ya bi da yanayin. Robert ya ce: “Ban gaya mata aꞌa kai-tsaye kuma da wuri kamar yadda Yusufu ya yi da matar Fotifar ba. (Far. 39:7-9) Na ma yi mamakin yadda guje mata ya yi min wuya. Abin da ya faru ya nuna min cewa ina bukatar in ƙara ƙarfafa dangantakata da Jehobah.”

16 Kamar Robert, kai ma za ka amfana idan kana bincika kanka a-kai-a-kai. Ko da ka guje wa wata jarraba, ka tambayi kanka, ‘Na guje wa jarrabar nan da nan?’ Idan ka ga cewa kana bukatar ka yi gyara, kada ka karaya. Ka gode wa Jehobah cewa yanzu ka san da wannan kasawar. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka, kuma ka ɗauki matakan da za su taimaka maka ka riƙa yin marmarin yi wa Jehobah biyayya.—Zab. 139:23, 24.

17. Me ya sa za mu ce abin da Robert ya yi ya ɗaukaka sunan Jehobah?

17 Akwai wani abu kuma da za mu koya daga labarin Robert. Ya ce: “Bayan da na gaya mata cewa ba zan zo ba, ta ce, ‘Ka ci jarrabawar!’ Sai na tambaye ta me take nufi, kuma ta gaya min cewa wata ƙawarta da Mashaidiya ce a dā, ta ce dukan matasa da Shaidun Jehobah ne suna yin abubuwa marasa kyau a ɓoye idan suka sami damar yin hakan. Saboda haka, ta gaya wa ƙawarta cewa za ta gwada ni don ta ga gaskiyar lamarin. Hakan ya sa na yi farin ciki don na ɗaukaka sunan Jehobah.”

18. Mene ne kake so ka ci-gaba da yi bayan ka yi baftisma? (Ka kuma duba akwatin nan “Talifofi Biyu da Za Su Amfane Ka.”)

18 Idan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma, kana nuna cewa za ka tsarkake sunansa ko da a wane yanayi kake ciki. Ka kasance da tabbacin cewa Jehobah ya san abubuwan da kake fuskanta da kuma jarrabobin da kake guje wa. Zai albarkace ka don kana ƙoƙari ka riƙe amincinka, kuma ka kasance da tabbacin cewa ruhunsa mai tsarki zai ba ka ƙarfin yin hakan. (Luk. 11:11-13) Da taimakon Jehobah, za ka ci-gaba da bin Yesu bayan ka yi baftisma.

Talifofi Biyu da Za Su Amfane Ka

Idan kai matashi ne a ikilisiya, za ka amfana sosai daga talifofin “Young People Ask . . . What Will I Need to Do After Baptism?” da ke jw.org. Kashi na 1 zai taimaka maka ka ci-gaba da yin ayyukan ibada. Kashi na 2 zai taimaka maka ka riƙe amincinka duk da matsaloli ko jarrabobin da kake fuskanta.

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya Kiristoci suke ɗaukan gungumen azaba “kowace rana”?

  • Mene ne zai taimaka maka don ka ci-gaba da bin Yesu bayan ka yi baftisma?

  • Ta yaya yin tunani a kan alkawarin bauta wa Jehobah da ka yi zai taimaka maka ka riƙe amincinka?

WAƘA TA 89 Mu Ji, Mu Yi Biyayya Don Mu Sami Albarka

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba