Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w24 Maris pp. 2-7
  • Ka Yi Shirin Yin Alkawarin Bauta wa Jehobah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Shirin Yin Alkawarin Bauta wa Jehobah?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ME AKE NUFI DA ALKAWARIN BAUTA WA JEHOBAH?
  • ME YA SA YA KAMATA KA YI ALKAWARIN BAUTA WA JEHOBAH?
  • KA YI SHIRIN YIN ALKAWARIN BAUTA WA JEHOBAH DA KUMA BAFTISMA?
  • ABIN DA YA SA WASU SUKE JINKIRI
  • KA CI-GABA DA KUSANTAR JEHOBAH
  • Ka Ci-gaba da Bin Yesu Bayan Ka Yi Baftisma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Me Ya Sa Za Ka Yi Alkawarin Bauta wa Allah?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
w24 Maris pp. 2-7

TALIFIN NAZARI NA 9

WAƘA TA 75 ‘Ga Ni! Ka Aike Ni’

Ka Yi Shirin Yin Alkawarin Bauta wa Jehobah?

“Me zan ba Yahweh saboda dukan alheransa gare ni?”—ZAB. 116:12.

ABIN DA ZA MU KOYA

Wannan talifin zai iya taimaka maka ka ƙara kusantar Jehobah don ka yi niyyar yin alkawarin bauta masa kuma ka yi baftisma.

1-2. Mene ne mutum yake bukatar ya yi kafin ya yi baftisma?

A CIKIN shekaru biyar da suka wuce, mutane fiye da miliyan ɗaya sun yi baftisma sun zama Shaidun Jehobah. Da yawa daga cikinsu tun suna ƙanana ne aka koya musu game da Jehobah, kamar yadda aka yi wa Timoti. (2 Tim. 3:14, 15) Wasu kuma sai da suka gama girma ne suka soma bauta ma Jehobah, wasu ma sai da suka tsufa. Alal misali, a ꞌyan shekaru da suka shige, wata mata da aka yi nazari da ita ta yi baftisma saꞌad da take shekara 97!

2 Idan ana nazarin Littafi Mai Tsarki da kai ko kuma iyayenka Shaidun Jehobah ne, za ka so ka yi baftisma kuwa? Idan haka ne, kana da kyakkyawan buri. Amma kafin ka yi baftisma, kana bukatar ka yi alkawarin bauta wa Jehobah. A talifin nan, za a bayyana abin da wannan alkawarin yake nufi. Bayan haka, za mu ga dalilin da ya sa bai kamata ka yi jinkirin yin alkawarin bauta wa Jehobah da yin baftisma ba idan ka yi shirin yin haka.

ME AKE NUFI DA ALKAWARIN BAUTA WA JEHOBAH?

3. Ka ba da misalin mutanen da suka yi alkawarin bauta wa Jehobah.

3 A Littafi Mai Tsarki, irin alkawarin nan yana nufin mutum ya keɓe kansa don yin wani abu na musamman. Israꞌilawa gabaki-ɗaya sun yi alkawarin bauta wa Jehobah. Amma har ila, a cikinsu akwai waɗanda aka keɓe su don yin wata hidima ta musamman. Alal misali, Haruna yana da wani ƙaramin allo na zinariya a gaban hularsa. Allon alama ce cewa “an keɓe shi da tsarki.” Yana nuna cewa Jehobah ya zaɓe shi ya yi hidima ta musamman, wato ya zama babban firist na Israꞌila. (L. Fir. 8:9) Masu hidimar Ba-nazari su ma sun keɓe kansu ga Jehobah a hanya ta musamman. Kalmar nan “Nazarit,” ta samo asali ne daga kalmar nan nazirʹ a Ibrananci, kuma tana nufin “wanda aka ware” ko aka “keɓe.” A dokar Musa akwai dokokin da Jehobah ya bayar musamman don masu hidimar Ba-nazari.—L. Ƙid. 6:2-8.

4. (a) Idan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah, mene ne zai zama farko a rayuwarka? (b) Idan aka ce ka ‘ƙi kanka,’ me ake nufi? (Ka kuma duba hoton.)

4 Idan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah, kana nufin ka zaɓi ka zama mabiyin Yesu kuma ka sa yin nufin Jehobah farko a rayuwarka. Mene ne hakan ya ƙunsa? Yesu ya ce: “Duk mai so ya bi ni, sai ya ƙi kansa.” (Mat. 16:24) A Hellenanci idan aka ce mutum ya “ƙi kansa,” ana nufin ba zai yi rayuwa don kansa ba. Idan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah, kana bukatar ka ƙi yin duk wani abin da zai ɓata masa rai. (2 Kor. 5:14, 15) Hakan na kuma nufin cewa za ka ƙi ‘ayyukan da halin mutuntaka yake haifarwa,’ kamar halin lalata. (Gal. 5:19-21; 1 Kor. 6:18) Hana kanka yin abubuwan nan zai hana ka jin daɗin rayuwa ne? Aꞌa. Idan kana ƙaunar Jehobah kuma ka san cewa dokokin nan don amfaninka ne, ba za ka yi wannan tunanin ba. (Zab. 119:97; Isha. 48:17, 18) Wani ɗanꞌuwa mai suna Nicholas ya ce: “Mutum zai iya ganin dokokin Jehobah kamar ƙofar kurkuku da ke hana shi fita ya yi abin da yake so, ko kuma kamar ƙofar da aka rufe ɗakin zakoki da ita don kar zakokin su fita su yi masa illa.”

Wani danꞌuwa yana kallon zakoki da aka tsare a wani daki.

Yaya kake ganin dokokin Jehobah? Kamar ƙofar kurkuku ne da ke hana ka fita ka yi abin da kake so, ko kamar ƙofar da aka rufe ɗakin zakoki da ita don kar zakokin su fita su yi maka illa? (Ka duba sakin layi na 4)


5. (a) Idan kana so ka yi alkawarin bauta wa Jehobah, ta yaya za ka yi hakan? (b) Mene ne bambancin yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma yin baftisma? (Ka kuma duba hoton.)

5 Idan kana so ka yi alkawarin bauta wa Jehobah, ta yaya za ka yi hakan? Adduꞌa za ka yi. A cikin adduꞌar, ka yi masa alkawari cewa za ka bauta masa shi kaɗai kuma za ka sa yin nufinsa farko a rayuwarka. Idan ka yi hakan, kana ma Jehobah alkawari ne cewa za ka ƙaunace shi “da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.” (Mar. 12:30) Wannan alkawarin tsakaninka da Jehobah ne kawai. Amma lokacin da za ka yi baftisma, kowa zai gani kuma ya san cewa ka yi alkawarin bauta wa Jehobah. Alkawarin bauta wa Jehobah ba ƙaramin abu ba ne. Ya kamata ka kasance da burin cika wannan alkawarin. Abin da Jehobah yake bukata daga gare ka ke nan.—M. Wa. 5:4, 5.

Maza da mata, kowannensu yana yin adduꞌa ga Jehobah.

Yin alkawarin bauta wa Jehobah yana nufin ka yi alkawari cewa za ka bauta masa shi kaɗai kuma za ka sa yin nufinsa farko a rayuwarka (Ka duba sakin layi na 5)


ME YA SA YA KAMATA KA YI ALKAWARIN BAUTA WA JEHOBAH?

6. Me ke sa mutum ya yi alkawarin bauta wa Jehobah?

6 Babban dalilin da ya sa ya kamata ka yi alkawarin bauta wa Jehobah shi ne domin kana ƙaunar sa. Ba haka kawai ka soma ƙaunar Jehobah ba. Amma abubuwan da ka koya game da shi da kuma “sanin nufinsa” ne suka sa ka soma ƙaunar sa. (Kol. 1:9) Binciken Littafi Mai Tsarki da ka yi ya tabbatar maka da cewa (1) akwai Allah, (2) Littafi Mai Tsarki maganarsa ce, kuma (3) yana amfani da ƙungiyarsa ya cika nufinsa.

7. Mene ne ya kamata mutum ya riƙa yi kafin ya yi alkawarin bauta wa Jehobah?

7 Waɗanda suke yin alkawarin bauta wa Jehobah suna bukatar su san muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki kuma su bi ƙaꞌidodin Allah a rayuwarsu. Suna yin iya ƙoƙarinsu su gaya wa mutane abubuwan da suka yi imani da su. (Mat. 28:19, 20) Suna ƙaunar Jehobah sosai, kuma babban burinsu shi ne su bauta masa shi kaɗai. Kai ma ba abin da ke zuciyarka ba ke nan? Idan kana ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarka, ba za ka yi alkawarin bauta masa kuma ka yi baftisma don kawai kana so ka faranta ran wanda yake yin nazari da kai, ko iyayenka, ko kuma don kawai ka ga abokanka suna hakan ba.

8. Me zai taimaka maka ka yi alkawarin bauta wa Jehobah? (Zabura 116:12-14)

8 Idan ka yi tunanin yawan alherin da Jehobah ya yi maka, za ka so ka yi masa godiya kuma ka yi alkawarin bauta masa. (Karanta Zabura 116:12-14.) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa, “kowace baiwa mai kyau, da kowace cikakkiyar kyauta” daga wurin Jehobah suke. (Yak. 1:17) Kuma kyauta mafi girma da Allah ya ba mu ita ce hadayar Ɗansa. Wannan ba ƙaramin alheri ba ne! Fansar Yesu ce ta buɗe maka hanyar zama aminin Jehobah. Ban da haka, Jehobah ya ba ka damar yin rayuwa har abada. (1 Yoh. 4:9, 10, 19) Don haka, wata babbar hanyar da za ka nuna godiyarka ga Jehobah don fansar da sauran albarkun da Jehobah ya yi maka ita ce, ta wurin yin alkawarin bauta masa. (M. Sha. 16:17; 2 Kor. 5:15) An bayyana abin da ya sa zai yi kyau ka nuna godiyarka ta wannan hanyar a littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Darasi na 46, batu na 4, inda ake da bidiyon nan mai jigo, Ku Ba da Kyauta ga Allah.

KA YI SHIRIN YIN ALKAWARIN BAUTA WA JEHOBAH DA KUMA BAFTISMA?

9. Me ya sa bai kamata mutum ya yi alkawarin bauta wa Jehobah da garaje don ya ga wasu suna hakan ba?

9 Mai yiwuwa kana bukatar ka yi wasu canje-canje a rayuwarka don ka iya bin ƙaꞌidodin Jehobah. Ko kuma kana bukatar ƙarin lokaci don ka ƙarfafa bangaskiyarka. (Kol. 2:6, 7) Wasu ɗalibai sukan fi wasu saurin kusantar Jehobah, kuma shekarun da matasa sukan kai kafin su yi alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma ba ɗaya ba ne. Don haka, ka yi ƙoƙari ka san inda kake bukatar yin gyara kuma ka yi gyaran. Kada ka gwada kanka da kowa.—Gal. 6:4, 5.

10. Idan ka ga cewa ba ka yi shirin yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma ba, me ya kamata ka yi? (Ka kuma duba akwatin nan, “Don Waɗanda Iyayensu Shaidun Jehobah Ne.”)

10 Ko da ka ga cewa ba ka yi shirin yin alkawarin bauta wa Jehobah yanzu ba, ka ci-gaba da yin wannan burin. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka yi duk wani gyaran da kake bukata. (Filib. 2:13; 3:16) Kuma ka kasance da tabbacin cewa Jehobah zai ji adduꞌarka ya kuma taimake ka.—1 Yoh. 5:14.

Don Waɗanda Iyayensu Shaidun Jehobah Ne

Talifin nan “Young People Ask . . . Should I Get Baptized?” da ke da kashi uku a jw.org zai taimaka wa matasa da iyayensu Shaidun Jehobah ne.

Don ƙarin bayani ka duba talifofin nazari biyu da ke Hasumiyar Tsaro na Maris, 2016. Talifofin su ne, “Yara da Matasa, Kun Yi Shirin Yin Baftisma Kuwa?” da kuma “Yara da Matasa, Ta Yaya Za Ku Yi Shirin Yin Baftisma?”

Za ka amfana sosai idan ka ɗau lokaci ka yi nazarin talifofin nan kuma ka yi tunani mai zurfi a kan abin da suka ce.

ABIN DA YA SA WASU SUKE JINKIRI

11. Wane taimako ne Jehobah yake yi wa bayinsa don su ci-gaba da bauta masa da aminci?

11 Wasu sun gama yin shirin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma amma suna jan jiki. Me ya sa? Domin suna ganin idan suka yi zunubi mai tsanani bayan sun yi baftisma za a yi musu yankan zumunci. Idan abin da kake tsoro ke nan, ka san cewa Jehobah zai ba ka dukan abin da kake bukata don ka ‘yi tafiyar da ta cancanta da masu bin Ubangiji, kuma ka faranta masa rai.’ (Kol. 1:10) Jehobah zai kuma ba ka ƙarfin yin abin da ya dace. Zai iya yin hakan domin ya riga ya taimaka wa mutane da yawa su yi abin da ya dace. (1 Kor. 10:13) Shi ya sa mutane kaɗan ne kawai ake yi wa yankan zumunci. Hakika, Jehobah yana taimaka wa mutanensa su bauta masa da aminci.

12. Me zai taimaka mana kar mu yi zunubi mai tsanani?

12 Dukanmu ajizai ne kuma muna fuskantar jarrabobi. (Yak. 1:14) Amma, kai ne za ka zaɓa ko za ka faɗa ma jarrabar ko aꞌa. Gaskiyar ita ce, yadda za ka yi rayuwarka a hannunka yake. Wasu suna ganin ba za mu iya kame kanmu ba, amma hakan ba gaskiya ba ne, za ka iya shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau. Idan an jarrabce ka da yin abin da ba shi da kyau, za ka iya ƙin yin sa. Akwai abubuwan da za su taimaka maka ka guji yin zunubi. Alal misali, ka riƙa yin adduꞌa kowace rana, ka riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki a-kai-a-kai, ka riƙa zuwa taro, kuma ka riƙa yin waꞌazi. Idan ka ci-gaba da yin abubuwan nan, za ka iya riƙe amincinka ga Jehobah. Ban da haka ma, ka tuna cewa Jehobah zai taimake ka.—Gal. 5:16.

13. Wane gurbi mai kyau ne Yusufu ya bar mana?

13 Zai fi maka sauƙi ka riƙe amincinka ga Jehobah idan ka shirya abin da za ka yi tun kafin ka fuskanci jarraba. Akwai labaran wasu da suka yi hakan a Littafi Mai Tsarki, duk da cewa su ajizai ne. Alal misali, matar Fotifar ta yi ta ƙoƙari ta sa Yusufu ya kwana da ita. Amma, Yusufu ya riga ya shirya abin da zai yi. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa, Yusufu “ya ƙi,” kuma ya ce: “Don me zan yi wannan babbar mugunta, in yi wa Allah zunubi?” (Far. 39:8-10) Hakika, Yusufu ya riga ya shirya matakin da zai ɗauka tun kafin ta zo masa da wannan jarrabar. Shi ya sa da ta zo bai yi masa wuya ya ƙi ba.

14. Me za mu yi don mu iya ƙin yin zunubi idan aka jarrabce mu?

14 Ta yaya kai ma za ka riƙe amincinka kamar Yusufu? Tun yanzu, ka shirya abin da za ka yi idan ka shiga cikin jarraba. Ka koyi yadda za ka ƙi abubuwan da Jehobah ba ya so ba tare da ɓata lokaci ba, ko tunaninsu ma kada ka yi. (Zab. 97:10; 119:165) Idan ka yi hakan, ba za ka faɗa wa jarraba ba don ka riga ka san abin da za ka yi.

15. Ta yaya mutum zai nuna cewa yana neman Jehobah da gaske? (Ibraniyawa 11:6)

15 Mai yiwuwa ka riga ka ga cewa wannan ita ce ƙungiyar da ke koyar da gaskiya, kuma kana so ka bauta ma Jehobah da dukan zuciyarka. Amma har ila, kana ganin ba ka yi shirin yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma ba. Idan haka ne, ka yi koyi da Sarki Dauda. Ka yi adduꞌa ka gaya wa Jehobah cewa: “Ya Allah, bincike ni, za ka kuwa san zuciyata, gwada ni, za ka kuwa san tunanina. Duba, ko a rayuwata akwai wata hanyar da nake ɓata maka rai, ka kuma bi da ni cikin hanya ta rai na har abada.” (Zab. 139:23, 24) Yin adduꞌa kamar haka zai nuna cewa kana neman taimakon Jehobah kuma kana yin iya ƙoƙarinka don ka cancanci yin baftisma. Jehobah yakan taimaka ma “waɗanda suke nemansa” da gaske.—Karanta Ibraniyawa 11:6.

KA CI-GABA DA KUSANTAR JEHOBAH

16-17. Ta yaya Jehobah yake jawo waɗanda iyayensu Shaidun Jehobah ne su bauta masa? (Yohanna 6:44)

16 Yesu ya ce Jehobah ne yake jawo mutane su bi shi. (Karanta Yohanna 6:44.) Hakan abin ban ƙarfafa ne sosai! Ko ba haka ba? Domin kafin Jehobah ya jawo mutum gare shi, akwai wani hali mai kyau da ya ga cewa mutumin yana da shi. Jehobah yakan ɗauki mutumin da daraja domin ya zama nasa. (M. Sha. 7:6) Yadda Jehobah yake ganin ka ke nan.

17 Mai yiwuwa kuma kai matashi ne, kuma iyayenka Shaidun Jehobah ne. Don haka, mai yiwuwa yana maka kamar bin su kawai kake yi, ba Jehobah ne ya jawo ka wurinsa ba. Amma fa, Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Ka yi kusa da Allah, shi kuwa zai yi kusa da kai.’ (Yak. 4:8; 1 Tar. 28:9) Idan ka ɗauki matakin kusantar Jehobah, shi ma zai kusace ka. Ba a matsayin iyali ne Jehobah yake jan mutane su zo su bauta masa ba. A maimakon haka, kowane mutumin da ke iyalin ne Jehobah yakan lura da shi kuma ya jawo shi. Don haka, idan ka ɗauki matakin yin kusa da Jehobah, Jehobah ma zai yi kusa da kai, kamar yadda Yakub 4:8 ta ce.—Ka kuma duba 2 Tasalonikawa 2:13.

18. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba? (Zabura 40:8)

18 Idan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma, kana bin halin Yesu ke nan, domin Yesu ya ba da kansa cewa zai yi nufin Ubansa. (Karanta Zabura 40:8; Ibran. 10:7) A talifi na gaba, za mu tattauna abin da zai taimaka maka ka ci-gaba da bauta ma Jehobah bayan ka yi baftisma.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ake nufi da yin alkawarin bauta wa Jehobah?

  • Me ya sa godiya don alherin Jehobah zai sa ka yi alkawarin bauta masa?

  • Me zai taimaka maka kar ka yi zunubi mai tsanani?

WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba