Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w23 Nuwamba pp. 20-25
  • Jehobah Zai Amsa Adduꞌoꞌina Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Zai Amsa Adduꞌoꞌina Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MENE NE JEHOBAH ZAI YI MANA?
  • MENE NE JEHOBAH YAKE SO MU YI?
  • ME YA SA ZA MU IYA BUKACI MU CANJA ABIN DA MUKA ROƘA?
  • Yadda Jehobah Yake Amsa Adduꞌoꞌinmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Me Ya Sa Allah Ba Ya Amsa Dukan Addu’o’i?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Yadda Za Mu Inganta Adduꞌoꞌinmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
w23 Nuwamba pp. 20-25

TALIFIN NAZARI NA 49

Jehobah Zai Amsa Adduꞌoꞌina Kuwa?

“Za ku yi kira gare ni, ku juyo, ku yi adduꞌa gare ni, ni zan kuwa ji ku.”—IRM. 29:12.

WAƘA TA 41 Allah Ka Ji Roƙona

ABIN DA ZA A TATTAUNAa

1-2. Mene ne zai sa mu ji kamar Jehobah ba ya amsa adduꞌoꞌinmu?

“MAI da Yahweh dalilin farin cikinka, zai kuwa biya bukatar zuciyarka.” (Zab. 37:4) Wannan alkawari ne mai ban shaꞌawa! Amma zai dace mu sa rai cewa duk abin da muka roƙa ne Jehobah zai ba mu? Me ya sa wannan tambayar take da muhimmanci? Bari mu yi laꞌakari da wasu misalai. Wata ꞌyarꞌuwa da ba ta yi aure ba ta roƙi Jehobah ya ba ta dama ta je Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki. Amma shekaru da yawa sun wuce kuma har ila ba a gayyace ta ba. Wani ɗanꞌuwa matashi ya roƙi Jehobah ya warkar da shi daga cuta mai tsanani da yake fama da ita don ya iya yin ayyuka a ikilisiya fiye da waɗanda yake yi. Amma bai warke ba. Wasu iyaye da Kiristoci ne sun roƙi Jehobah ya sa yaronsu ya ci-gaba da bauta masa. Amma yaronsu ya yanke shawarar daina bauta wa Jehobah.

2 Wataƙila kai ma ka roƙi Jehobah ya ba ka wani abu, amma har yanzu ba ka samu ba. Mai yiwuwa hakan zai sa ka ga kamar Jehobah ba ya amsa adduꞌoꞌinka amma yana amsa na wasu mutane. Ko ka yi tunanin cewa ka yi wani abu marar kyau shi ya sa. Tunanin da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Janiceb ta yi ke nan. Ita da maigidanta sun roƙi Jehobah ya sa su je Bethel. Ta ce: “Na gama sa rai cewa za a kira mu Bethel nan ba da daɗewa ba.” Amma shekaru da yawa sun wuce kuma har ila ba a kira su ba. Janice ta ce: “Abin ya dame ni kuma na rikice. Ban san me na yi da ya ɓata wa Jehobah rai ba. Na yi adduꞌa sosai kuma na gaya masa cewa ina so in je Bethel. Me ya sa ya ƙi amsa adduꞌata?”

3. Me za mu tattauna a talifin nan?

3 A wasu lokuta za mu iya yin shakka ko Jehobah yana jin adduꞌoꞌinmu. A dā, har da bayin Jehobah masu aminci sun yi shakkar hakan. (Ayu. 30:20; Zab. 22:2; Hab. 1:2) Mene ne zai tabbatar maka cewa Jehobah zai ji adduꞌoꞌinka? (Zab. 65:2) Don mu ga amsar tambayar nan, bari mu fara da amsa tambayoyin nan: (1) Mene ne Jehobah zai yi mana? (2) Mene ne Jehobah yake so mu yi? (3) Me ya sa za mu iya bukaci mu canja abin da muka roƙa?

MENE NE JEHOBAH ZAI YI MANA?

4. Bisa ga abin da ke Irmiya 29:​12, mene ne Jehobah ya ce zai yi mana?

4 Jehobah ya yi alkawarin cewa zai ji adduꞌoꞌinmu. (Karanta Irmiya 29:12.) Jehobah yana ƙaunar bayinsa masu aminci sosai, don haka ba zai taɓa yin watsi da adduꞌoꞌinsu ba. (Zab. 10:17; 37:28) Amma hakan ba ya nufin cewa zai ba mu dukan abubuwan da muka roƙa. Sai mun shiga sabuwar duniya ne za mu iya samun wasu abubuwan da muka roƙa.

5. Mene ne Jehobah yake dubawa saꞌad da yake jin adduꞌoꞌinmu? Ka bayyana.

5 Jehobah yakan duba ko abin da muka roƙa ya jitu da nufinsa. (Isha. 55:​8, 9) Nufin Jehobah ne ya sa duniya ta cika da mutane masu aminci da suke bauta masa da farin ciki. Amma Shaiɗan ya ce ꞌyan Adam za su fi jin daɗi idan suka mulki kansu. (Far. 3:​1-5) Don Jehobah ya nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne, ya ƙyale mutane su yi mulki. Amma mulkin ꞌyan Adam shi ne ya jawo matsaloli da yawa da muke fuskanta a yau. (M. Wa. 8:​9, Mai Makamantu[n] Ayoyi) Mun san cewa Jehobah ba zai cire dukan matsalolin da muke fuskanta a yanzu ba. Domin idan ya yi hakan, marasa imani ga Allah za su ga kamar ꞌyan Adam ne suke magance matsalolin, don haka mulkinsu ba laifi.

6. Me ya sa muke bukatar mu kasance da tabbacin cewa Jehobah yana yin abin da ya dace a kowane lokaci?

6 Mutane za su iya roƙan abu ɗaya amma Jehobah ya amsa musu a hanyoyi dabam-dabam. Misali, saꞌad da Sarki Hezekiya yake rashin lafiya sosai, ya roƙi Jehobah ya warkar da shi. Jehobah ya ji adduꞌar kuma ya warkar da shi. (2 Sar. 20:​1-6) Amma manzo Bulus ya roƙi Jehobah ya cire masa “ƙaya a jiki,” kuma mai yiwuwa wani rashin lafiya mai tsanani ne, amma Jehobah bai warkar da shi ba. (2 Kor. 12:​7-9) Ka kuma ga misalin manzo Yakub da Bitrus. Sarki Hiridus ya so ya kashe su biyun. ꞌYanꞌuwa sun yi adduꞌa a madadin Bitrus, kuma da alama sun yi hakan a madadin Yakub shi ma. Amma Hiridus ya kashe Yakub, Bitrus kuma malaꞌika ya cece shi. (A. M. 12:​1-11) Muna iya cewa, ‘Me ya sa Jehobah ya ceci Bitrus, amma bai ceci Yakub ba?’ Littafi Mai Tsarki bai gaya mana dalilin ba.c Mun dai san cewa Jehobah “mai adalci ne.” (M. Sha. 32:4) Kuma mun san cewa Jehobah yana ƙaunar Bitrus da Yakub. (R. Yar. 21:14) A wasu lokuta, Jehobah zai iya amsa adduꞌarmu a hanyar da ba mu zata ba. Amma da yake mun gaskata cewa a kowane lokaci Jehobah yana yin abin da ya dace, ba za mu ce yadda ya amsa adduꞌarmu bai dace ba.—Ayu. 33:13.

7. Mene ne ya kamata mu guje wa, kuma me ya sa?

7 Zai dace mu guji gwada yanayinmu da na wasu mutane. Alal misali, muna iya roƙon Jehobah ya ba mu wani abu, amma sai mu ga cewa ba mu samu abin ba. Sai daga baya mu ji cewa wani ya roƙi irin abin da muka roƙa, kuma kamar Jehobah ya amsa adduꞌarsa. Abin da ya faru da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Anna ke nan. Ta roƙi Jehobah ya warkar da maigidanta mai suna Matthew daga cutar kansa. A lokacin, akwai wasu ꞌyanꞌuwa mata da tsofaffi ne da suke fama da cutar kansa. Anna ta yi adduꞌa sosai a madadin Matthew da kuma ꞌyanꞌuwa matan. ꞌYanꞌuwa matan sun warke amma Matthew ya rasu. Da farko, Anna ta yi tunanin cewa ꞌyanꞌuwan sun warke ne don Jehobah ya taimaka musu. Idan haka ne, to me ya sa bai amsa adduꞌarta kuma ya warkar da maigidanta ba? Ba za mu iya faɗan dalilin da ya sa ꞌyanꞌuwa matan suka warke ba. Mun dai san cewa a nan gaba Jehobah zai cire dukan matsalolin da muke fuskanta kuma yana marmarin ta da amintattun bayinsa a nan gaba.—Ayu. 14:15.

8. (a) Bisa ga Ishaya 43:​2, ta yaya Jehobah yake taimaka mana? (b) Ta yaya yin adduꞌa yake taimaka mana mu jimre matsaloli? (Ka duba bidiyon nan Yin Adduꞌa Yana ba Mu Ƙarfin Jimrewa.)

8 Jehobah zai taimaka mana a kowane lokaci. Jehobah Ubanmu mai ƙauna ne, don haka ba ya so ya ga muna shan wahala. (Isha. 63:9) Duk da haka, ba ya cire dukan wahalolin da muke sha. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta wahalolin nan da koguna da wuta. (Karanta Ishaya 43:2.) Kuma Jehobah ya yi alkawari cewa zai taimaka mana mu “bi ta” cikin kogunan da wutar, wato zai taimaka mana mu jimre wahalolin da muke sha. Kuma ba zai bar matsalolin da muke fuskanta su hana mu bauta masa ba. Ƙari ga haka, Jehobah yana ba mu ruhu mai tsarki don ya taimaka mana mu jimre. (Luk. 11:13; Filib. 4:13) Don haka, muna da tabbacin cewa Jehobah zai ba mu ainihin abin da muke bukata don mu iya jimre matsalolinmu, kuma mu bauta masa da aminci.d

MENE NE JEHOBAH YAKE SO MU YI?

9. Bisa ga Yakub 1:​6, 7, me ya sa muke bukatar mu gaskata cewa Jehobah zai taimaka mana?

9 Jehobah yana so mu dogara gare shi. (Ibran. 11:6) A wasu lokuta, za mu ji kamar wahalolin da muke sha sun fi ƙarfin mu. Za ma mu iya soma shakkar cewa Jehobah zai taimaka mana. Amma Littafi Mai Tsarki ya ba mu tabbacin cewa Jehobah zai taimaka mana mu “tsallake kowace katanga.” (Zab. 18:29) Don haka, maimakon mu soma yin shakka, zai dace mu kasance da bangaskiya, mu yi adduꞌa kuma mu gaskata cewa Jehobah zai amsa adduꞌoꞌinmu.—Karanta Yakub 1:​6, 7.

10. Ka ba da misalin yadda za mu yi abubuwan da suka jitu da adduꞌarmu.

10 Jehobah yana so mu yi abubuwan da za su jitu da adduꞌarmu. Alal misali, wani ɗanꞌuwa zai iya roƙan Jehobah ya taimaka masa ya sami izini daga wurin aiki don ya iya zuwa taron yanki. Ta yaya Jehobah zai amsa adduꞌar nan? Jehobah zai iya ba wa ɗanꞌuwan ƙarfin zuciya don ya iya zuwa ya sami shugaban aikinsa. Amma ɗanꞌuwan ne da kansa zai je ya nemi izinin. Mai yiwuwa zai bukaci ya roƙi shugaban aikinsa sau da yawa. Zai ma iya gaya masa cewa zai yi aikin a wata rana dabam. Idan da bukata, zai iya ce a cire kuɗin da ya kamata a biya shi a ranakun da zai je taron yanki daga albashinsa.

11. Me ya sa ya kamata mu ci-gaba da yin adduꞌa a kan damuwoyinmu?

11 Jehobah yana son mu ci-gaba da yin adduꞌa a kan damuwoyinmu. (1 Tas. 5:17) Yesu ya bayyana cewa ba za a ba mu wasu abubuwan da muka roƙa nan take ba. (Luk. 11:9) Don haka, kada mu gaji da yin adduꞌa. Mu yi adduꞌa da dukan zuciyarmu, kuma mu yi hakan babu fasawa. (Luk. 18:​1-7) Idan muka ci-gaba da yin adduꞌa game da wani abu, Jehobah zai ga cewa abin yana da muhimmanci a gare mu. Ƙari ga haka, zai nuna cewa mun san Jehobah zai taimaka mana.

ME YA SA ZA MU IYA BUKACI MU CANJA ABIN DA MUKA ROƘA?

12. (a) Saꞌad da muke roƙon abu, wace tambaya ce ya kamata mu yi wa kanmu, kuma me ya sa? (b) Ta yaya za mu tabbata cewa abubuwan da muke roƙa suna daraja Jehobah? (Ka duba akwatin nan “Abubuwan da Nake Roƙa Suna Daraja Jehobah?”)

12 Idan ba mu samu abin da muka roƙa ba, zai dace mu yi wa kanmu tambayoyin nan: Na ɗaya, ‘Abin da nake adduꞌa a kai ya dace kuwa?’ A yawancin lokuta, mukan ɗauka cewa mun san abin da ya dace da mu. Amma mai yiwuwa abubuwan da muka roƙa ba su ne za su amfane mu ba. Idan muna fuskantar matsala, mai yiwuwa ba abin da muka roƙi Jehobah ya yi mana ne zai warware matsalar ba. Kuma ƙila wasu abubuwan da muka roƙa ba su jitu da nufin Jehobah ba. (1 Yoh. 5:14) Alal misali, ka tuna iyayen da muka ambata ɗazu. Sun roƙi Jehobah ya sa yaronsu ya ci-gaba da bauta masa. Za mu iya ganin cewa roƙo mai kyau ne suka yi. Amma Jehobah ba ya tilasta mana mu bauta masa. Yana so dukanmu har da yaranmu mu bauta masa da son ranmu. (M. Sha. 10:​12, 13; 30:​19, 20) Don haka, abin da ya kamata iyayen su roƙa shi ne, Jehobah ya taimaka musu su iya ratsa zuciyar yaronsu don ya ƙaunace Shi kuma ya bauta masa.—K. Mag. 22:6; Afis. 6:4.

Abubuwan da Nake Roƙa Suna Daraja Jehobah?

Jehobah Uba ne mai ƙauna kuma yana so ya amsa adduꞌoꞌinmu. Ban da haka, shi Mahaliccinmu ne kuma muna bukatar mu daraja shi. (R. Yar. 4:11) Saꞌad da kake yin adduꞌa, ta yaya za ka nuna cewa kana daraja Ubanmu na sama?

  • Ka tabbata cewa abubuwan da kake roƙa sun jitu da nufin Allah kuma kana roƙon su ne da dalili mai kyau. (1 Yoh. 5:14) Zai dace mu guji mai da hankali ga abubuwan da muke so ko waɗanda muke bukata kawai a adduꞌoꞌinmu. Yakub ya gargaɗi Kiristoci a ƙarni na farko cewa, Jehobah ba zai amsa adduꞌoꞌinsu ba idan suka yi adduꞌar da “mugun nufi,” wato son zuciya.—Yak. 4:3.

  • Kada ka yi kamar kana tilasta wa Allah. (Mat. 4:7) Ka gaskata cewa Jehobah ya san hanyar da ta fi dacewa ya amsa adduꞌarka. Kuma a wasu lokuta, yadda ya amsa adduꞌar, zai yi dabam da yadda ka yi tsammani.—Afis. 3:20.

  • A kowace rana, ka riƙa gode masa don abubuwan da ya tanada maka. Jehobah zai yi farin ciki sosai idan ka gaya masa yadda kake godiya don taimakonsa.—Kol. 3:15; 1 Tas. 5:​17, 18.

13. Bisa ga Ibraniyawa 4:​16, a wane lokaci ne Jehobah zai taimaka mana? Ka bayyana.

13 Tambaya ta biyu ita ce, ‘Wannan ne lokacin da ya dace Jehobah ya amsa adduꞌata?’ Muna iya ganin cewa ya kamata a amsa adduꞌarmu nan-da-nan. Amma gaskiyar ita ce, Jehobah ne ya san ainihin lokacin da ya dace ya amsa adduꞌarmu. (Karanta Ibraniyawa 4:16.) Idan ba mu sami abin da muka roƙa nan-da-nan ba, za mu ga kamar Jehobah ba ya so ya amsa roƙonmu. Amma ƙila abin da Jehobah yake gaya mana shi ne, ‘Lokaci bai yi ba tukuna.’ Alal misali, ka yi tunanin ɗanꞌuwa matashi da ya roƙi Jehobah ya warkar da shi daga cutarsa. Da Jehobah ya warkar da shi, da Shaiɗan ya gaya wa Jehobah cewa ɗanꞌuwan ya ci-gaba da bauta masa ne don ya warkar da shi. (Ayu. 1:​9-11; 2:4) Ƙari ga haka, Jehobah ya riga ya shirya lokacin da zai warkar da mu daga dukan cututtuka. (Isha. 33:24; R. Yar. 21:​3, 4) Kafin wannan lokacin, ba zai dace mu sa rai cewa Jehobah zai warkar da mu daga cututtukanmu ta hanyar muꞌujiza ba. Don haka, ɗanꞌuwan zai iya roƙon Jehobah ya ba shi ƙarfi da kwanciyar hankali, don ya iya jimre matsalarsa kuma ya ci-gaba da bauta masa da aminci.—Zab. 29:11.

14. Mene ne ka koya daga abin da ya faru da Janice?

14 Ka tuna da labarin Janice, wadda ta yi adduꞌa game da yin hidima a Bethel. Sai bayan shekaru biyar ne ta fahimci yadda Jehobah ya amsa adduꞌarta. Ta ce: “Jehobah ya yi amfani da lokacin nan don ya koya min abubuwa da yawa, kuma ya taimaka mini in kasance da halaye masu kyau. Ina bukatar in ƙara dogara gare shi. Ina bukatar in inganta yadda nake yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Kuma ina bukatar in san cewa zan iya yin farin ciki ko da wace hidima nake yi.” Daga baya, Janice da maigidanta sun soma hidimar mai kula da daꞌira. Da Janice ta tuna abin da ya faru, ga abin da ta ce: “Jehobah ya amsa adduꞌata amma ba a hanyar da na yi tsammani ba. Ya ɗauke ni dogon lokaci kafin na ga yadda ya amsa adduꞌata, amma ina godiya don ƙaunarsa da kuma alherin da ya yi min.”

Kananan hotuna: 1. Wasu ꞌyanꞌuwa mata guda biyu suna cika fom na Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki. Kowannensu ta yi adduꞌa kafin ta aika fom din. 2. Daya daga cikin matan tana nuna gayyata na makarantar da aka tura mata ma ꞌyanꞌuwa a Majamiꞌar Mulki har da dayan ꞌyanꞌuwar da ita ma ta cika fom din. 3. ꞌYarꞌuwar da ba a gayyace ta ba ta yi adduꞌa ga Jehobah, sai ta yi adduꞌa bayan hakan. Bayan wasu lokuta, ta soma waꞌazi a kasar waje, kuma tana yin aiki a inda ake gina.

Idan kana ganin Jehobah bai amsa adduꞌarka ba, za ka iya roƙan wasu abubuwa dabam (Ka duba sakin layi na 15)f

15. Me ya sa wani lokaci gwamma kar mu nace a kan abu ɗaya kawai? (Ka kuma duba hoton.)

15 Tambaya ta uku ita ce, ‘Ko in roƙi wani abu dabam ne?’ Ko da yake yana da kyau mu faɗi ainihin abin da muke bukata, amma wani lokaci, gwamma kar mu nace a kan abu ɗaya kawai. Ta hakan, za mu iya sanin abin da Jehobah yake so ya yi mana. Ka yi laꞌakari da misalin ꞌyarꞌuwar da ba ta yi aure ba, wadda ta roƙi Jehobah ya sa ta je Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki. Tana so ta je makarantar ne don ta iya zuwa hidima a inda ake da bukata. Yayin da take roƙan Jehobah ya sa ta je makarantar, tana iya roƙan sa ya sa ta ga wasu hanyoyin da za ta iya faɗaɗa hidimarta. (A. M. 16:​9, 10) Bayan haka, sai ta yi abubuwan da suka jitu da adduꞌarta. Tana iya tambayar mai kula da daꞌirarsu ya gaya mata ko akwai ikilisiyar da ke bukatar majagaba. Ko kuma ta tambayi ofishinmu ta ji inda ake bukatar masu shela.e

16. Wane tabbaci ne muke da shi?

16 Kamar yadda muka koya, muna da tabbacin cewa Jehobah zai amsa adduꞌoꞌinmu a hanyar da ta dace. (Zab. 4:3; Isha. 30:18) A wasu lokuta, ba za a amsa adduꞌoꞌinmu yadda muka yi tsammani ba. Amma Jehobah ba zai ƙi jin adduꞌoꞌinmu ba. Yana ƙaunar mu sosai. Kuma ba zai taɓa yin watsi da mu ba. (Zab. 9:10) Don haka, ka ci-gaba da “dogara ga Allah kullum” kuma ka riƙa gaya masa abin da ke zuciyarka saꞌad da kake adduꞌa.—Zab. 62:8.

GAME DA ADDUꞌOꞌINMU, . . .

  • mene ne za mu iya sa rai cewa Jehobah zai yi?

  • mene ne Jehobah yake so mu yi?

  • me ya sa za mu iya bukaci mu canja abin da muka roƙa?

WAƘA TA 43 Adduꞌar Godiya

a Wannan talifin zai bayyana dalilin da ya sa za mu iya kasance da tabbacin cewa Jehobah zai amsa adduꞌoꞌinmu a hanyar da ta dace.

b An canja wasu sunayen.

c Ka duba talifin nan “Kana Yarda da Matakan da Jehobah Yake Ɗaukawa?” da ke Hasumiyar Tsaro ta watan Fabrairu, 2022, sakin layi na 3-6.

d Don ka ga ƙarin bayani a kan yadda Jehobah yake taimaka mana mu jimre matsaloli, ka kalli bidiyon nan Yin Adduꞌa Yana ba Mu Ƙarfin Jimrewa da ke jw.org/ha.

e Idan kana so ka san yadda za ka je hidima a wata ƙasa dabam, ka duba littafin nan Organized to Do Jehovahꞌs Will, darasi na 10, sakin layi na 6-9.

f BAYANI A KAN HOTUNA: ꞌYanꞌuwa mata guda biyu suna adduꞌa kafin su cika fom na Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki. Daga baya, an gayyaci ɗayan ꞌyarꞌuwar, ɗayan kuma ba a gayyace ta ba. Maimakon ꞌyarꞌuwar da ba a gayyata ba ta yi baƙin ciki, ta roƙi Jehobah ya taimaka mata ta ga wasu hanyoyi dabam da za ta iya faɗaɗa hidimarta. Sai ta rubuta wa reshen ofishinsu saƙo kuma ta gaya musu cewa za ta so ta yi hidima a inda ake da bukata.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba