TALIFIN NAZARI NA 6
Kana Yarda da Matakan da Jehobah Yake Ɗaukawa?
“Dutse ne shi, aikinsa cikakke ne, kuma dukan hanyoyinsa gaskiya ne. Allah mai aminci ne, ba ya ruɗu, mai adalci ne shi, mai gaskiya kuma.”—M. SHA. 32:4.
WAƘA TA 3 Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1-2. (a) Me ya sa yake yi wa mutane da yawa wuya su amince da masu ja-goranci? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
YANA yi wa mutane da yawa wuya su yarda da mutanen da suke yi musu ja-goranci, domin sun lura cewa dokokin gwamnati suna kāre masu arziki ne da masu iko, amma suna wulaƙanta talakawa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Waɗansu sukan sami mulki, waɗansu kuwa su sha wuya a ƙarƙashinsu.” (M. Wa. 8:9, Mai Makamantu Ayoyi) Ƙari ga haka, wasu shugabannin addinai suna yin abubuwa marasa kyau. Hakan ya sa wasu mutane sun daina dogara ga Allah. Don haka, idan mutum ya amince ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mu, za mu bukaci mu taimaka masa ya koyi yadda zai dogara ga Jehobah da kuma waɗanda Jehobah ya naɗa su su yi mana ja-goranci.
2 Ba ɗalibanmu ba ne kaɗai suke bukatar su koyi yadda za su dogara ga Jehobah da waɗanda yake yin amfani da su don yi mana ja-goranci. Ko da mun yi shekaru da yawa muna bauta wa Jehobah, dole ne mu riƙa tuna cewa dukan abubuwan da Jehobah yake yi daidai ne. A wasu lokuta, wasu abubuwa suna iya faruwa da za su iya gwada bangaskiyarmu ga Jehobah. A talifin nan za mu tattauna hanyoyi uku da za a iya jarraba bangaskiyarmu: (1) sa’ad da muke karanta wasu labarai a Littafi Mai Tsarki, (2) sa’ad da ƙungiyar Jehobah ta ba mu umurni, da kuma (3) sa’ad da muka fuskanci matsaloli a nan gaba.
KA DOGARA GA JEHOBAH SA’AD DA KAKE KARANTA LITTAFI MAI TSARKI
3. Ta yaya wasu labarai a Littafi Mai Tsarki za su iya jarraba bangaskiyarmu?
3 Sa’ad da muke karanta Littafi Mai Tsarki, za mu iya tunanin me ya sa Jehobah ya bi da wasu mutane a wata hanya, kuma ya ɗauki wasu matakai. Alal misali, a Littafin Ƙidaya, mun karanta cewa Jehobah ya yanke ma wani Ba’isra’ile hukuncin kisa domin ya je ɗiba itace a ranar Assabaci. A littafin Sama’ila na biyu, mun karanta cewa Jehobah ya gafarta wa Sarki Dauda bayan ya yi zina da kisa. (L. Ƙid. 15:32, 35; 2 Sam. 12:9, 13) Muna iya yin tunani cewa, ‘Me ya sa Jehobah ya gafarta wa Dauda bayan ya yi zina da kisa, amma ya yanke wa mutumin da yake kwasan itace a ranar Assabaci hukuncin kisa?’ Don mu sami amsar tambayar, bari mu tattauna abubuwa uku da muke bukatar mu tuna da su yayin da muke karanta Littafi Mai Tsarki.
4. Ta yaya Farawa 18:20, 21 da Maimaitawar Shari’a 10:17 suka ƙarfafa mu mu ci gaba da amincewa da hukuncin da Jehobah ya yanke?
4 Ba a kowane lokaci ba ne Littafi Mai Tsarki yake ba mu cikakken bayani game da kowane batu. Alal misali, mun san cewa Dauda ya tuba da gaske. (Zab. 51:2-4) Amma wanda ya taka dokar Assabaci wane irin mutum ne shi? Ya yi da-na-sani don abin da ya yi? Ya taka dokar Jehobah a dā ne? Ya taɓa ƙin gargaɗi? Littafi Mai Tsarki bai ba mu amsoshin tambayoyin nan ba. Amma mun tabbata cewa Jehobah “mai adalci ne.” (M. Sha. 32:4) Yana yanke hukunci bisa gaskiya, ba abin da aka gaya masa ba, ko wariya, ko kuma duk wani abin da yake hana ’yan Adam yanke hukunci mai kyau. (Karanta Farawa 18:20, 21; Maimaitawar Shari’a 10:17.) Yayin da muke daɗa sanin Jehobah da ƙa’idodinsa, za mu daɗa amincewa da hukuncinsa. Ko da mun karanta wani abu a Littafi Mai Tsarki da ba mu fahimta dalla-dalla ba, mun san cewa Allahnmu “mai gaskiya ne cikin dukan hanyoyinsa.”—Zab. 145:17.
5. Ta yaya ajizanci yake shafan yadda muke yanke hukunci? (Ka duba akwatin nan “Ajizancinmu Yana Hana Mu Fahimtar Batu da Kyau.”)
5 Da yake mu ajizai ne, a wasu lokuta ba za mu iya yanke hukunci yadda ya kamata ba. Allah ya halicce mu cikin kamanninsa, saboda haka, muna so a nuna wa kowa adalci. (Far. 1:26) Amma da yake mu ajizai ne, za mu iya yanke hukuncin da bai dace ba ko da muna ganin mun san batun da kyau. Alal misali, yadda Jehobah ya nuna wa mutanen Nineba jinƙai ya sa Yona fushi. (Yona 3:10–4:1) Amma ka yi tunanin abin da ya faru domin Jehobah ya nuna musu jinƙai. Mutanen Nineba fiye da 120,000 sun tsira. A ƙarshe, Yona ne ya yi kuskure, ba Jehobah ba.
6. Me ya sa Jehobah ba ya bukatar ya gaya mana dalilan da suka sa ya ɗauki wasu matakai?
6 Jehobah ba ya bukatar ya gaya wa ’yan Adam dalilan da suka sa ya ɗauki wasu matakai. Gaskiya ne cewa a dā, Jehobah ya ba wasu bayinsa dama su faɗi ra’ayinsu game da wasu matakan da ya ɗauka ko yake so ya ɗauka. (Far. 18:25; Yona 4:2, 3) Kuma a wasu lokuta yakan bayyana dalilin da ya sa yake so ya ɗau wani mataki. (Yona 4:10, 11) Amma Jehobah ba ya bukatar ya gaya mana dalilan da suka sa ya yanke wasu shawarwari. A matsayin Mahaliccinmu, ba ya bukatar amincewarmu kafin ya ɗau wani mataki ko kuma bayan ya yi hakan.—Isha. 40:13, 14; 55:9.
KA DOGARA GA JEHOBAH SA’AD DA AKA BA KA UMURNI
7. Mene ne zai iya yi mana wuya, kuma me ya sa?
7 Ba ma shakka cewa Jehobah yana yin abin da ya dace a kullum. Amma za mu iya amincewa da umurnin waɗanda Jehobah ya naɗa su yi mana ja-goranci? A wasu lokuta, za mu iya gani kamar suna yanke shawara bisa ga nasu ra’ayi ne. Ra’ayin da wasu mutane suke da shi a zamanin dā ke nan. Ka yi la’akari da misalin da ke sakin layi na 3. Mai yiwuwa ’yan’uwan mutumin da ya taka dokar Assabaci ba su amince cewa Musa ya tuntuɓi Jehobah kafin ya yanke wa mutumin hukuncin kisa ba. Kuma ƙila wani abokin Uriya mutumin Hitti wanda matarsa ta yi zina da Dauda, zai iya tunanin cewa Dauda ya yi amfani da matsayinsa na sarki ne don ya guje wa hukuncin da ya kamata a yi masa. Gaskiyar ita ce, Jehobah ya amince da waɗanda ya naɗa su su yi ja-goranci a ƙungiyarsa da kuma ikilisiya. Saboda haka, idan ba mu yarda da su ba, ba za mu iya cewa mun amince da Jehobah ba.
8. Wace alaƙa ce ke tsakanin abin da ke Ayyukan Manzanni 16:4, 5 da yadda ake yi wa ikilisiyoyinmu a yau ja-goranci?
8 Jehobah yana yin amfani da “bawan nan mai aminci, mai hikima” don ya yi wa ƙungiyarsa ja-goranci. (Mat. 24:45) Kamar yadda hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a ƙarni na farko ta yi, haka ma bawan nan yana kula da mutanen Allah a duniya, kuma yana yi wa dattawa a ikilisiya ja-goranci. (Karanta Ayyukan Manzanni 16:4, 5.) Dattawa kuma za su tabbata cewa sun bi umurninsu. Za mu nuna cewa mun amince da yadda Jehobah yake yin abubuwa ta bin umurnin ƙungiyarsa da na dattawa.
9. A wane lokaci ne zai yi mana wuya mu bi shawarar da dattawa suka yanke, kuma me ya sa?
9 A wasu lokuta, yana iya yi mana wuya mu bi shawarar da dattawa suka yanke. Alal misali, a shekarun baya-bayan nan, an canja tsarin ikilisiyoyi da da’irori. A wasu wurare, dattawa sun gaya wa wasu ’yan’uwa su koma wata ikilisiya dabam domin ikilisiyar ta cika. Idan aka ce mu ƙaura zuwa wata ikilisiya, yana iya yi mana wuya mu bar abokanmu da iyalinmu a baya. Shin Jehobah ne yake gaya wa dattawa ikilisiyar da za su tura mai shela? A’a. Hakan yana iya sa ya yi mana wuya mu bi umurninsu. Amma Jehobah ya yarda dattawa su yanke wannan shawarar, mu ma muna bukatar mu amince da su.b
10. Me ya sa ya kamata mu ba wa dattawa haɗin kai? (Ibraniyawa 13:17)
10 Me ya sa ya kamata mu goyi bayan shawarar da dattawa suka yanke ko da ba ma son shawarar? Domin yin hakan zai sa mutanen Allah su ci gaba da kasancewa da haɗin kai. (Afis. 4:2, 3) Ikilisiya za ta amfana idan kowa ya bi shawarar da dattawa suka yanke. (Karanta Ibraniyawa 13:17.) Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne, za mu nuna wa Jehobah cewa mun amince da mutanen da ya naɗa su yi mana ja-goranci.—A. M. 20:28.
11. Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da bin umurnin da dattawa suka ba mu?
11 Za mu daɗa amincewa da umurnin da dattawa suka ba mu idan muka tuna cewa suna yin addu’a kafin su tattauna batun ikilisiya. Suna bincika ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma suna karanta umurnin da ƙungiyar Jehobah ta bayar. Burinsu shi ne su faranta ran Jehobah, kuma su kula da mutanensa yadda ya dace. Sun san cewa za su ba Jehobah lissafin yadda suka bi da ikilisiya. (1 Bit. 5:2, 3) Ka yi tunanin wannan: A wannan duniyar da mutane ba su da haɗin kai domin bambancin launin fata ko addini ko kuma siyasa, bayin Jehobah suna bauta masa tare cikin haɗin kai. Ruhun Jehobah ne kaɗai yake sa hakan ya faru!
12. Mene ne dattawa za su yi tunaninsa idan suna so su san ko mutum ya tuba da gaske?
12 Jehobah ya ba dattawa aikin tabbatar da cewa ikilisiya tana da tsabta. Idan wani Kirista ya yi zunubi mai tsanani, Jehobah ya ba dattawa hakkin tantance ko ya cancanci ya ci gaba da kasancewa a ikilisiya. Ɗaya daga cikin abubuwan da za su yi shi ne su duba ko mutumin ya yi nadama domin abin da ya yi. Mutumin zai iya cewa ya tuba, amma ya tsani abin da ya yi kuwa? Ya ƙuduri niyyar guje wa sake yin laifin? Idan abokansa ne suka sa shi yin zunubin, ya ɗauki matakin yanke abokantakar? Dattawa za su yi addu’a ga Jehobah, su karanta abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da batun, kuma su mai da hankali ga yadda mai zunubin yake ji don abin da ya yi. Bayan hakan, za su yanke shawara ko za a bar mai zunubin a ikilisiya. A wasu lokuta, za a bukaci a yi masa yankan zumunci.—1 Kor. 5:11-13.
13. Me za mu iya yin tunani a kai idan aka yi ma wani abokinmu ko danginmu yankan zumunci?
13 Me zai iya hana mu yarda da dattawa? Idan mutumin da aka yi wa yankan zumunci ba abokinmu ko danginmu ba ne, za mu iya amincewa da hukuncin da dattawa suka yanke. Amma idan mutumin danginmu ko abokinmu ne fa? Za mu iya tunanin ko dattawa sun bincika abin da ya faru sosai ko kuma mu yi tunanin wataƙila ba su yi shari’ar yadda Jehobah zai yi ba. Mene ne zai taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace a wannan batun?
14. Mene ne zai taimaka mana idan shawarar da dattawa suka yanke game da wani mai zunubi ta shafe mu?
14 Zai dace mu tuna cewa Jehobah ne ya kafa tsarin yin yankan zumunci domin kowa a ikilisiya ya amfana har da mai zunubi. Idan aka bar mai zunubi da ya ƙi tuba ya ci gaba da kasancewa a ikilisiya, zai iya rinjayar wasu ’yan’uwa su yi abin da yake yi. (Gal. 5:9) Ban da haka, wanda ya yi zunubi ba zai san cewa abin da ya yi yana da muni ba. Saboda haka, ba zai so ya canja halinsa da ayyukansa don ya sami amincewar Jehobah ba. (M. Wa. 8:11) Zai dace mu kasance da tabbaci cewa dattawa suna ɗaukan hakkinsu na yin yankan zumunci da muhimmanci sosai. Kamar alƙalai a zamanin Isra’ila ta dā, dattawa sun san cewa ‘shari’ar da suke yi ba ta mutum ba ce, amma ta Yahweh’ ce.—2 Tar. 19:6, 7.
DOGARA GA JEHOBAH YANZU ZAI IYA SA MU DOGARA GARE SHI A GABA
Me zai taimaka mana mu yarda da umurnan da za a ba mu a lokacin ƙunci mai girma kuma mu bi su? (See paragraph 15)
15. Me ya sa muke bukatar mu amince da umurnin da Jehobah yake ba mu a yanzu fiye da yadda muke yi a dā?
15 Yayin da ƙarshen wannan zamanin yake kusatowa, za mu bukaci mu daɗa amincewa da yadda Jehobah yake yin abubuwa. Me ya sa? Domin a lokacin ƙunci mai girma, za a ba mu umurnai masu wuya. Jehobah ba zai yi mana magana kai tsaye ba. Mai yiwuwa zai ba mu umurnai ta wurin waɗanda ya naɗa su yi mana ja-goranci. A lokacin, ba zai dace mu soma shakkar umurnansu, ko mu soma tunanin cewa sun yanke shawara bisa ra’ayinsu ba. Za ka dogara ga Jehobah da ƙungiyarsa a wannan lokaci na musamman? Yadda kake bin umurnin waɗanda Jehobah ya naɗa su yi mana ja-goranci a yanzu zai taimaka maka ka amsa wannan tambayar. Idan kana bin umurnin da aka ba ka a yau, zai yi maka sauƙi ka bi umurnin da za a ba mu a lokacin ƙunci mai girma.—Luk. 16:10.
16. Mene ne zai faru nan ba da daɗewa ba da zai nuna ko muna amincewa da hukuncin Jehobah?
16 Yanzu ne ya kamata mu soma tunanin yadda za mu ɗauki hukuncin da Jehobah zai yanke a ƙarshen muguwar duniyar nan. Yanzu, muna sa rai cewa mutane da yawa da ba sa bauta wa Jehobah har da danginmu, za su soma bauta masa. Amma a yaƙin Armageddon, Jehobah ne zai yi amfani da Yesu don ya yanke musu hukunci. (Mat. 25:31-33; 2 Tas. 1:7-9) Ba mu ne za mu zaɓi waɗanda Jehobah zai yi musu jinƙai ba. (Mat. 25:34, 41, 46) Za mu amince da hukuncin da Jehobah ya yanke, ko kuma za mu daina bauta masa domin ba mu amince ba? Hakika muna bukatar mu dogara ga Jehobah sosai yanzu domin mu iya dogara gare shi a nan gaba.
17. Ta yaya za mu amfana daga hukuncin da Jehobah zai yi a ƙarshen duniyar nan?
17 Ka yi tunanin yadda za mu ji a sabuwar duniya bayan mun ga sakamakon hukuncin da Jehobah ya yanke. Za a hallaka addinan ƙarya, da tsarin kasuwanci na wannan duniyar, da kuma gwamnatocin da suka yi shekaru suna wahalar da mutane. Mutane ba za su yi rashin lafiya ko tsufa ko su mutu kamar yadda ake yi a yau ba. Za a ɗaure Shaiɗan da aljanunsa na shekaru dubu. Za a kawar da mugayen abubuwan da suke faruwa sanadiyyar tawayen da suka yi. (R. Yar. 20:2, 3) Za mu yi farin ciki sosai a lokacin domin mun amince da yadda Jehobah yake yin abubuwa!
18. Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga Isra’ilawa kamar yadda yake a Littafin Ƙidaya 11:4-6 da kuma 21:5?
18 Shin akwai abubuwan da za su faru a sabuwar duniya da za su nuna ko muna dogara ga Jehobah? Ka yi la’akari da abin da ya faru jim kaɗan bayan an ceto Isra’ilawa daga bauta a ƙasar Masar. Wasu daga cikinsu sun soma gunaguni domin sun yi kewar abubuwan da suka saba ci a ƙasar, kuma suka tsani manna da Jehobah ya ba su. (Karanta Littafin Ƙidaya 11:4-6; 21:5.) Shin mu ma za mu yi irin wannan tunanin bayan ƙunci mai girma? Ba mu san yawan aikin da za mu yi don mu tsabtacce duniya kuma mu mai da ita aljanna ba. Da alama za mu yi aiki sosai kuma wataƙila hakan ba zai kasance mana da sauƙi ba. Za mu yi gunaguni domin abubuwan da Jehobah yake yi mana tanadin su a lokaci ne? Idan muna nuna godiya don abubuwan da Jehobah yake ba mu a yanzu, za mu iya nuna godiya don abubuwan da zai ba mu a nan gaba.
19. Ta yaya za ka taƙaita muhimman batutuwa da muka tattauna a wannan talifin?
19 A kowane lokaci, yadda Jehobah yake yin abubuwa daidai ne. Muna bukatar mu tabbata da hakan. Ƙari ga haka, muna bukatar mu amince da waɗanda Jehobah ya naɗa su yi mana ja-goranci. Kada ka manta da abin da Jehobah ya faɗa ta bakin annabinsa Ishaya, ya ce: “Cikin kwanciyar hankali da dogara gare ni za ku sami ƙarfi.”—Isha. 30:15.
WAƘA TA 98 Nassosi Hurarre Ne Daga Allah
a Talifin nan zai taimake mu mu daɗa dogara ga Jehobah, da kuma waɗanda yake amfani da su don yi mana ja-goranci. Ƙari ga haka, za mu ga yadda yin hakan zai amfane mu a yanzu kuma ya shirya mu don matsalolin da za mu fuskanta a gaba.
b A wasu lokuta, akwai wani yanayin da zai iya sa a bukaci iyali ko kuma mutum ya zauna a ikilisiyar da yake. Ka duba “Question Box” da ke Hidimarmu ta Mulki ta Nuwamba, 2002 a Turanci.