Ka Yi Biyayya Ga Kristi Da Kuma Amintaccen Bawansa
“Ubangijinsa. . . za ya sanya shi bisa dukan abin da ya ke da shi.”—MATTA 24:45-47.
1, 2. (a) Wanene Nassosi ya ce shi ne Shugabanmu? (b) Menene ya nuna cewa Kristi yana ja-gorar ikilisiyar Kirista da kyau?
“KADA kuma a kira ku ‘Shugabanni,’ domin shugaba ɗaya ne gare ku, wato Almasihu.” (Matta 23:10, Littafi Mai Tsarki) Da waɗannan kalmomin, Yesu ya bayyana wa mabiyansa sarai cewa ba wani mutum a duniya da zai zama shugabansu. Shugabansu zai zama Yesu Kristi. Allah ne ya naɗa Yesu ya zama shugaba. Jehobah “ya tashe shi daga cikin matattu . . . ya sanya shi kuma shi zama kai a bisa abu duka ga ikilisiya jikinsa ke nan.”—Afisawa 1:20-23.
2 Tun da Yesu ne “kai a bisa abu duka” ga ikilisiya, yana nuna ikonsa bisa dukan abubuwan da ke faruwa a cikin ikilisiya. Yana ganin duka abubuwan da suke faruwa a cikin ikilisiya. Yana lura da ruhaniyar kowane Kirista ko kuma ikilisiya. An fahimci wannan a Wahayin da aka ba manzo Yohanna a ƙarshen ƙarni na farko. Yesu ya gaya wa ikilisiyoyi guda bakwai sau biyar cewa ya san ayyukansu, da ƙwazonsu da kasawarsu, kuma ya ba su shawara da gargaɗi yadda ya kamata. (Ru’ya ta Yohanna 2:2, 9, 13, 19; 3:1, 8, 15) Mun tabbata cewa Yesu ya san ruhaniyar ikilisiyoyin da suke Asiya Ƙarama, Falasɗinu, Suriya, Babila, Helas, Italiya, da sauran wurare. (Ayukan Manzanni 1:8) Yau kuma fa?
Bawa Mai Aminci
3. Me ya sa zai dace a kwatanta Kristi da kai, ikilisiyarsa kuma da jiki?
3 Bayan tashinsa daga matattu kafin ya je wurin Ubansa a sama, Yesu ya gaya wa almajiransa cewa: “Dukan hukunci a cikin sama da ƙasa an bayas gareni.” Ya kuma ce: “Ga shi kuwa ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.” (Matta 28:18-20) Zai ci gaba da zama shugabansu. A wasiƙunsa zuwa ga Kiristoci a Afisus da Kolossi, manzo Bulus ya kwatanta ikilisiyar Kirista da “jiki,” wanda Yesu ne kansa. (Afisawa 1:22, 23; Kolossiyawa 1:18) Littafin nan The Cambridge Bible for Schools and Colleges ya ce wannan furci “ba wai kawai yana nuna cewa haɗin kai tsakanin mabiyan da Shugaban na da muhimmanci ba, amma shugaban ne ke yi musu ja-gora. Sune mutanen da yake amfani da su.” Su wanene Kristi ya yi amfani da su tun da aka naɗa shi Sarki a shekara ta 1914?—Daniel 7:13, 14.
4. In ji annabcin Malakai, menene Jehobah da Yesu suka gani sa’ad da suka zo binciken haikali na ruhaniya?
4 Annabcin Malakai ya ce Jehobah “Ubangiji” na gaske tare da Ɗansa da aka naɗa “mala’ikan alkawari,” wato Yesu Kristi, za su zo su bincika ‘haikalinsa,’ ko kuma gidan bauta ta alama. “Lokaci ya yi” da za a fara ‘shari’a a gidan Allah’ a shekara ta 1918.a (Malachi 3:1; 1 Bitrus 4:17) An bincika waɗanda suke da’awar cewa suna wakiltar Allah da bautarsa ta gaskiya a duniya sosai. An ƙi cocin Kiristendom da tun ƙarnuka da yawa suke koyarwa da ba ya daraja Allah kuma suka sa hannu a cikin kisan da aka yi a Yaƙin Duniya na Ɗaya. An gwada amintattun shafaffun Kiristoci na ruhu da suka rage, an gyara su, kuma an amince da su “su miƙa ma Ubangiji hadayu cikin adalci.”—Malachi 3:3.
5. In ji annabcin Yesu game da ‘zuwansa,’ wanene ya zama ‘bawan’ nan mai aminci?
5 Daidai da annabci na Malakai, alamar da Yesu ya ba almajiransa don su fahimci lokacin ‘zuwansa da cikar zamaninsa,’ ta haɗa da fahimtar rukunin “bawa.” Yesu ya ce: “Wanene fa bawan nan mai-aminci, mai-hikima wanda ubangijinsa ya sanya shi bisa iyalin gidansa, domin shi ba su abincinsu a lotonsa? Wannan bawa mai-albarka ne, wanda ubangijinsa sa’anda ya zo za ya iske shi yana yin haka. Hakika, ina ce muku, za ya sanya shi bisa dukan abin da ya ke da shi.” (Matta 24:3, 45-47) A shekara ta 1918 sa’ad da ya “zo” don ya bincika ‘bawan,’ Yesu ya sami almajiransa shafaffu na ruhu da suka rage waɗanda tun a shekara ta 1879 suna amfani da wannan jarida da waɗansu littattafai da ke bisa Littafi Mai Tsarki su yi tanadin “abincinsu a lotonsa.” Ya amince da su a matsayin abin da yake amfani da shi ko kuma ‘bawa,’ kuma a shekara ta 1919 ya ba su amanar mallakarsa ta duniya.
Kula da Mallakar Kristi da Suke Duniya
6, 7. (a) Waɗanne kalamai ne Yesu ya yi amfani da su sa’ad da yake magana game da ‘bawansa’ mai aminci? (b) Menene Yesu yake nufi sa’ad da ya yi amfani da kalmar nan “wakili”?
6 Watanni kaɗan kafin Yesu ya ba da annabcinsa game da alamar zuwansa, da kuma kasancewar ‘bawan’ da zai wakilce shi a duniya, ya yi amfani da wani furci dabam sa’ad da yake magana game da wannan “bawa,” kuma hakan ya nuna aikin da bawan zai yi. Yesu ya ce: “Wanene fa wakili mai-aminci, mai-azanci, wanda ubangijinsa za ya sanya shi bisa iyalin gidansa, domin shi raba musu abincinsu a lotonsa? Ina ce maku, Hakika za ya sanya shi bisa abin da ya ke da shi duka.”—Luka 12:42, 44.
7 A nan an kira bawan wakili, kalmar da aka fassara daga kalmar Helenanci mai nufin “mai kula da gida.” Wakilin nan ba rukunin mutane masu ilimi da suke bayyana abubuwa a cikin Littafi Mai Tsarki ba ne. Ƙari ga tanadin abinci na ruhaniya a “lotonsa,” za a naɗa “wakili mai-aminci” ya kula da dukan mabiyan Kristi da kuma “abin da ya ke da shi” a duniya. Menene dukan abin da Yesu yake da shi?
8, 9. Menene “abin da [Kristi] ya ke da shi” da ya ba bawan nan ya kula da shi?
8 Ayyukan da bawan nan zai yi sun ƙunshi kula da abubuwan da mabiyan Yesu suke amfani da shi don tafiyar da ayyukansu na Kirista, kamar su hedkwata da kuma ofishin reshe na Shaidun Jehobah, da kuma wuraren bautarsu kamar su Majami’un Mulki da Majami’un Babban Taro a dukan duniya. Abu mafi muhimmanci shi ne, bawan nan yana lura da tsarin nazarin Littafi Mai Tsarki da suke ƙarfafa ruhaniya a taro na mako-mako da kuma babban taro da taron gunduma. A waɗannan taron, ana ba da bayani game da cikawar annabci na Littafi Mai Tsarki, da kuma yadda za a yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a rayuwa na yau da kullum.
9 Ayyukan wakilin kuma ya ƙunshi kula da duka ayyukan wa’azin “bishara kuwa ta mulki” da kuma “almajirtadda dukan al’ummai.” Wannan ya ƙunshi koyar da mutane su kiyaye dukan abubuwan da Kristi, wato shugaban ikilisiya ya ba da umurni a yi a wannan lokaci na ƙarshe. (Matta 24:14; 28:19, 20; Ru’ya ta Yohanna 12:17) Wannan aikin wa’azi da koyarwa sun sa an samu abokan shafaffu, wato “taro mai-girma.” Wannan “muradin dukan dangogi” suna cikin “abin da [Kristi] ya ke da shi” wanda amintaccen bawa yake kula da shi.—Ru’ya ta Yohanna 7:9; Haggai 2:7.
Hukumar Mulki da Suke Wakiltar Rukunin Bawa
10. Wane rukuni ne aka naɗa su riƙa tsai da shawara a ƙarni na farko, kuma ta yaya wannan ya shafi ikilisiyoyi?
10 Babu shakka, ayyukan wannan bawan mai aminci zai ƙunshi tsai da shawara da yawa. A ikilisiyar Kirista ta farko, manzanni da dattawa a Urushalima sun wakilci rukunin bawa, ta wurin tsai da shawara da ta shafi dukan ikilisiyar Kirista. (Ayukan Manzanni 15:1, 2) An aika wa ikilisiyoyi shawarar da hukumar mulki na ƙarni na farko ta yi ta wurin wasiƙu da kuma masu kula masu ziyara. Kiristoci na farko sun yi farin cikin samun wannan bayanin, kuma yadda suka haɗa kai da hukumar mulki ya kawo salama da haɗin kai.—Ayukan Manzanni 15:22-31; 16:4, 5; Filibbiyawa 2:2.
11. Su wanene Kristi yake amfani da su a yau don su ja-goranci ikilisiya, kuma ta yaya ya kamata mu ɗauki waɗannan amintattun Kiristoci?
11 A farkon zamanin Kiristoci, ƙaramin rukunin masu kula na shafaffu na ruhu ne suka zama Hukumar Mulki na mabiyan Kristi a duniya a yau. Ta “hannunsa na dama” na nuna iko, Yesu, wato shugaban ikilisiya yana ja-gorar waɗannan amintattun maza yayin da suke kula da aiki na Mulki. (Ru’ya ta Yohanna 1:16, 20) A cikin tarihin rayuwarsa, Albert Schroeder, da yake cikin Hukumar Mulki da daɗewa wanda ya gama aikinsa na duniya kwanan nan, ya ce: “Hukumar Mulki tana yin taro a kowace Laraba, tana soma taron da addu’a don roƙon ruhun Jehobah ya ja-gorance ta. Tana ƙoƙari sosai ta ga cewa kowane abu da aka aikata da kuma shawarar da aka tsai da ya yi daidai da Kalmar Allah Littafi Mai Tsarki.”b Mun amince da waɗannan amintattu shafaffun Kiristoci. Musamman game da su, ya kamata mu yi biyayya da abin da manzo Bulus ya ce: “Ku yi biyayya da waɗanda ke shugabannanku, ku sarayadda kanku garesu: gama suna yin tsaro sabili da rayukanku.”—Ibraniyawa 13:17.
Ka Daraja Bawan nan Mai Aminci
12, 13. Waɗanne dalilai ne muke da su na daraja rukunin bawa?
12 Wani dalili na musamman na yin biyayya ga bawa mai aminci shi ne cewa ta yin haka muna yin biyayya ga Shugaban Yesu Kristi. Bulus ya rubuta game da amintattu: “Hakanan kuma shi wanda aka kira, yana ɗa, bawan Kristi ne. Da tamani aka saye ku.” (1 Korinthiyawa 7:22, 23; Afisawa 6:6) Saboda haka, idan muka yi biyayya ga ja-gorar bawan nan mai aminci da kuma Hukumar Mulki, muna yin biyayya ne ga Kristi Shugaban bawan. Wata hanya da za mu “shaida Yesu Kristi Ubangiji ne, zuwa darajar Allah Uba,” ita ce ta wurin daraja mutanen da Kristi yake yin amfani da su su kula da mallakarsa ta duniya.—Filibbiyawa 2:11.
13 Wani dalili na nuna daraja ga bawa mai aminci shi ne cewa an kwatanta shafaffun Kiristoci na duniya da ‘haikalin’ da Jehobah ya mallaka ta wurin “ruhu.” Saboda haka su ‘tsarkakku’ ne. (1 Korinthiyawa 3:16, 17 Afisawa 2:19-22) Wannan haikali mai tsarki ne Yesu ya ba wa mallakarsa ta duniya, hakan yana nufin cewa wasu ayyuka da hakki na ikilisiyar Kirista yana hannun rukunin bawan. Saboda haka, duka waɗanda suke cikin ikilisiya sun yarda cewa aiki ne mai tsarki su bi kuma su tallafa wa umurnin da ke zuwa daga bawan nan mai aminci da kuma Hukumar Mulki. Hakika, “waɗansu tumaki” suna ganin gata ne mai girma su taimaki rukunin bawan nan wajen kula da mallakar Shugabansu.—Yohanna 10:16.
Ka ba Su Cikakken Goyon Baya
14. Kamar yadda Ishaya ya annabta, ta yaya ne waɗansu tumaki suke bin bayan shafaffu rukunin bawa kamar masu “ɗawainiya”?
14 Annabci na Ishaya ya nuna yadda waɗansu tumaki suke yin biyayya ga Isra’ila ta Allah, ya ce: “Hakanan Ubangiji ya faɗi, Ɗawainiyar Masar, da kayan ciniki na Kush, da su Sabeanawa, dogayen mutane, duk za su ƙetaro su zo wurinka, su zama naka kuma; za su bi bayanka; a cikin sarƙoƙi za su ƙetaro: su fāɗi a gabanka, su yi roƙo a gareka, su ce, Hakika Allah yana cikinka; babu waninsa kuma, babu wani Allah.” (Ishaya 45:14) A alamance, waɗansu tumaki a yau suna bin ja-gorar rukunin bawa da Hukumar Mulki. Kamar masu “ɗawainiya,” waɗansu tumaki sun ba da kansu da dukiyarsu don goyon bayan aikin wa’azi da Yesu ya ba mabiyansa shafaffu su yi a duniya.—Ayukan Manzanni 1:8; Ru’ya ta Yohanna 12:17.
15. Ta yaya ne annabci na Ishaya 61:5, 6 suka annabta dangantakar da ke tsakanin waɗansu tumaki da Isra’ila ta Allah?
15 Waɗansu tumaki suna godiya kuma suna farin cikin yin hidima a ƙarƙashin ja-gorancin rukunin bawa da Hukumar Mulki. Sun fahimci cewa shafaffun su ne “Isra’ila na Allah.” (Galatiyawa 6:16) A alamance ‘baƙin’ da “baibayi” da suke tare da Isra’ila ta Allah, suna farin cikin yin hidima kamar ‘manoma’ da ‘masu-gyara gonakin anab’ a ƙarƙashin ja-gorancin shafaffu, wato ‘firist na Ubangiji’ da ‘masu-hidima na Allah.’ (Ishaya 61:5, 6) Suna ƙwazo a wa’azin bishara ta Mulki da kuma almajirantar da dukan al’umma. Suna taimakon rukunin bawa wajen kula da sababbin tumaki.
16. Menene ya motsa waɗansu tumaki su tallafa wa bawan nan mai aminci, mai hikima?
16 Waɗansu tumaki sun fahimci cewa sun amfana sosai daga ƙoƙarin da bawa mai aminci yake yi wajen yin tanadin abinci na ruhaniya a kan kari. Sun kuma fahimci cewa idan ba don bawan nan mai aminci mai hikima ba, da ba su fahimci gaskiya ta Littafi Mai Tsarki ba, kamar su ikon mallaka na Jehobah, da tsarkake sunansa, Mulki, sababbin sammai da sabuwar duniya, da kurwa, yanayin matattu, da ainihin wanene Jehobah, Ɗansa da kuma ruhu mai tsarki. Don su nuna godiya da kuma amincinsu, waɗansu tumaki suna tallafa wa shafaffun ’yan’uwan Kristi na duniya a wannan zamani na ƙarshe.—Matta 25:40.
17. Menene Hukumar Mulki ta ga ya dace ta yi, kuma menene za mu tattauna a talifi na gaba?
17 Saboda yadda suke raguwa, shafaffu ba za su iya kasancewa a duka ikilisiyoyi ba don su tabbatar da yadda ake kula da mallakar Kristi ba. Saboda haka, Hukumar Mulki ta naɗa maza daga cikin waɗansu tumaki a matsayin masu kula da ofishin reshe, gundumomi, da’irori, da kuma ikilisiyoyi na Shaidun Jehobah. Halin da muke nuna wa waɗannan da suke ƙarƙashin ja-gorar Kristi yana nuna cewa muna yin biyayya ga Kristi da bawansa mai aminci kuwa? Za mu tattauna wannan a talifi na gaba.
[Hasiya]
a Don ƙarin bayani game da wannan batu, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Maris, 2004, shafofi na 25 zuwa 30, da kuma 1 ga Disamba, 1992 shafi na 13 na Turanci.
b An buga talifin wannan jaridar a 1 ga Maris, 1988, shafofi na 10 zuwa 17 a Turanci.
Domin Maimaitawa
• Wanene Shugabanmu, kuma menene ya nuna cewa ya san abubuwan da suke faruwa a cikin ikilisiyoyi?
• A lokacin binciken “haikali,” su wanene aka samu suna aiki kamar bawa mai aminci, kuma wane mallaka ne aka ba su?
• Waɗanne dalilai na Nassosi ne ya sa ya kamata a tallafa wa bawan nan mai aminci?
[Hotuna a shafi na 23]
“Abin da [Yesu] ya ke da shi” da “wakili” yake lura da shi ya ƙunshi dukiya, da tsarin ayyuka na ruhaniya, da kuma aikin wa’azi
[Hoto a shafi na 25]
Waɗansu tumaki suna taimakon rukunin bawan nan mai aminci ta wajen aikin wa’azi