Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w15 9/15 pp. 23-27
  • Ta Yaya Za Mu Nuna Cewa Muna Kaunar Jehobah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya Za Mu Nuna Cewa Muna Kaunar Jehobah?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA GODE WA JEHOBAH DON TANADIN DA YAKE YI MANA
  • KA YI BIMBINI A KAN ABUBUWAN DA JEHOBAH YAKE KOYA MAKA
  • KA KARƁI SHAWARA DA KUMA HORO DA ALLAH YAKE YI MANA
  • KA DOGARA GA JEHOBAH DON YA TAIMAKE KA KUMA YA KĀRE KA
  • Ka Ƙaunaci Allah Da Yake Ƙaunarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • “Wajibi Ne Ka Ƙaunaci Jehobah Allahnka”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙauna Ta Gina Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Kada Ku Bar Ƙaunar da Kuke wa Juna ta yi Sanyi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
w15 9/15 pp. 23-27
1. Wani dan’uwa yana yi wa wani mutum da ke zauna a wurin shakatawa wa’azi; 2. Wani mahaifi yana karanta wa dansa littafin nan Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki; 3. Wata ’yar’uwa tana koya wa wasu game da Jehobah

Ta Yaya Za Mu Nuna Cewa Muna Kaunar Jehobah?

“Muna kauna, domin shi ne ya fara kaunarmu.”—1 YOH. 4:19, Littafi Mai Tsarki.

WAKOKI: 56, 138

YAYA KAKE JI GAME DA JEHOBAH IDAN KA YI LA’AKARI DA . . .

  1. yadda yake biyan bukatunmu?

  2. koyarwar gaskiya da Jehobah yake tanadar mana?

  3. shawararsa da kuma horo da yake mana?

1, 2. Kamar yadda manzo Yohanna ya ce, yaya Allah ya koya mana mu kaunace shi?

HANYA mafi kyau da Uba zai koyar da yaransa ita ce ta kafa misali mai kyau. Manzo Yohanna ya rubuta cewa: “Muna kauna, domin shi ne [Allah] ya fara kaunarmu.” (1 Yoh. 4:19, LMT) Saboda haka, a bayyane yake cewa Jehobah Uba ne mai kauna da ya kafa mana misali mafi kyau da zai taimaka mana mu kaunace shi.

2 A wace hanya ce Allah ya ‘fara kaunar mu’? Manzo Bulus ya ce: “Allah yana shaidar kaunarsa gare mu, da yake, tun muna masu-zunubi tukuna, Kristi ya mutu sabili da mu.” (Rom. 5:8) Jehobah ya nuna cewa yana kaunar mu da gaske ta wajen ba da Ɗansa hadaya a madadinmu. Irin wannan kaunar ta kunshi bayarwa da kuma sadaukarwa. Mun amfana daga wannan gagarumar sadaukarwa, kuma hakan ya sa mun kusace shi.—1 Yoh. 4:10.

3, 4. Ta yaya za mu nuna cewa muna kaunar Allah?

3 A cikin halayen Jehobah, kauna ce ta fi muhimmanci. Shi ya sa Yesu ya ce dokar Allah mafi muhimmanci ita ce: “Ka yi kaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka, da dukan karfinka.” (Mar. 12:30) Kalmomin Yesu ya nuna cewa Jehobah yana son mu kaunace shi da dukan zuciyarmu. Saboda haka, Jehobah ba zai ji daɗi ba idan ba mu bauta masa da dukan zuciyarmu ba. Hakan ya nuna cewa za mu kaunace shi da dukan karfinmu da ranmu da kuma azancinmu. Abin da annabi Mikah ya ce Jehobah yake bukata a gare mu ke nan.—Karanta Mikah 6:8.

4 Ta yaya za mu nuna cewa muna kaunar Ubanmu na sama da gaske? Ya kamata mu kaunace shi da dukan ranmu da mallakarmu. Kamar yadda Yesu ya nuna, hakan ya kunshi karfinmu da tunaninmu da halinmu. A talifin da ya gabata, mun tattauna hanyoyi huɗu da Jehobah ya nuna kaunarsa ga ’yan Adam. Bari mu tattauna yadda za mu nuna cewa muna kaunar Jehobah da kuma kyautata kaunarmu a gare shi.

KA GODE WA JEHOBAH DON TANADIN DA YAKE YI MANA

5. Wane mataki ne za mu ɗauka saboda dukan abubuwan da Jehobah ya yi mana?

5 Mene ne za ka yi idan aka ba ka kyauta? Babu shakka, za ka gode wa wanda ya ba ka kyautar. Kari ga haka, za ka ɗauki kyautar da tamani kuma za ka yi amfani da ita a hanyar da ta dace. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowace kyakkyawar baiwa da kowace cikakkiyar kyauta daga bisa ta ke, tana saukowa daga wurin Uban haskoki, wanda sakewa ba ta yiwuwa gareshi, ba kuwa inuwa ta juyawa.” (Yak. 1:17) Jehobah ba ya fasa yi mana tanadin abin da muke bukata don mu rayu kuma mu yi farin ciki. Hakan ne ya sa muke kaunar sa.

6. Mene ne Isra’ilawa suke bukata su yi idan suna so su ci gaba da samun albarkar Jehobah?

6 Isra’ilawa sun yi shekaru da yawa suna jin daɗin abubuwan da Jehobah ya tanadar musu. Ya ba su dokokinsa da kuma abubuwan da suke bukata don su rayu. (K. Sha. 4:7, 8) Amma wajibi ne su rika bin dokokin Allah don su ci gaba da jin daɗin waɗannan abubuwan. Waɗannan dokokin sun haɗa da ba da hadayar “nunan fāri” ta kasar. (Fit. 23:19) Ta hakan, za su nuna cewa suna godiya ga Jehobah saboda kaunarsa da kuma albarkar da ya yi musu.—Karanta Kubawar Shari’a 8:7-11.

7. Ta yaya za mu yin amfani da ‘wadatarmu’ don mu nuna kaunarmu ga Jehobah?

7 Mu kuma fa? Ko da yake ba a bukatar mu mika irin wannan hadayu a yau, ya dace mu nuna muna kaunar Allah ta wajen girmama shi da ‘wadatarmu.’ (Mis. 3:9) A waɗanne hanyoyi ne za mu iya yin hakan? Hakika, muna iya yin amfani da wadatarmu don mu tallafa wa wa’azin bisharar Mulki a yankinmu da kuma a faɗin duniya. Wannan hanya ce mai kyau ta nuna kaunarmu ga Jehobah ko da muna da wadata ko a’a. (2 Kor. 8:12) Da akwai wasu hanyoyi kuma da za mu nuna kaunarmu ga Jehobah.

8, 9. Ta yaya dogara ga Jehobah zai nuna cewa muna kaunarsa? Ka ba da misali.

8 Yesu ya gaya wa almajiransa kada su yi alhini game da abinci da tufafi amma su ci gaba da saka ayyukan Mulki kan gaba a rayuwarsu. Ya daɗa cewa Ubanmu ya san ainihin abin da muke bukata. (Mat. 6:31-33) Saboda haka, mun dogara ga Jehobah don mun san cewa zai cika wannan alkawarin. Da yake muna amincewa da waɗanda muke kauna, idan muka dogara ga Jehobah sosai za mu kara kaunarsa. (Zab. 143:8) Saboda haka, ya dace mu tambayi kanmu: ‘Shin makasudina da salon rayuwata suna nuna cewa ina kaunar Jehobah da gaske? Shin abubuwan da nake yi yau da kullum sun nuna cewa na dogara da shi ya biya bukatuna?’

9 Wani Kirista mai suna Mike ya nuna cewa yana kaunar Jehobah kuma ya dogara gare shi. Sa’ad da yake matashi, Mike yana da makasudin yin hidima a wata kasa. Sai ya yi aure kuma suka haifi yara biyu. Duk da haka bai daina tunanin hidima a wata kasa ba. Sa’ad da Mike da iyalinsa suka karanta labaran ’yan’uwa da suke hidima a wata kasa, sai suka tsai da shawara su saukaka rayuwarsu. Suka sayar da gidansu kuma suka koma karamin gida. Mike ya rage yawan aiki da yake yi. Sai shi da iyalinsa suka kaura zuwa wata kasa, kuma sun yi shakaru biyu suna jin daɗin hidima a kasar, sai Mike ya ce: “Mun shaida cewa abin da Yesu ya faɗa a Matta 6:33 gaskiya ne.”

KA YI BIMBINI A KAN ABUBUWAN DA JEHOBAH YAKE KOYA MAKA

10. Me ya sa ya dace mu rika yin bimbini a kan abubuwan da muka koya game da Jehobah kamar yadda Sarki Dauda ya yi?

10 Shekaru 3,000 da suka shige, Sarki Dauda ya lura da abubuwan da ke sararin sama kuma hakan ya motsa shi. Ya rubuta cewa: “Sammai suna bayyanawar ɗaukakar Allah; sararin sama kuma yana nuna aikin hannuwansa.” Kari ga haka, ya yi tunani game da Dokar Allah kuma ya ce: “Shari’a ta Ubangiji cikakkiya ce, tana mayar da rai: Shaidar Ubangiji tabbataciya ce, tana sa marar-sani ya zama mai-hikima.” Mene ne sakamakon irin wannan bimbini? Dauda ya ci gaba: “Bari batutuwan bakina, da tunanin zuciyata, su zama abin karɓa a gareka, Ya Ubangiji, dutsena da mai-fansana.” Hakan ya sa Dauda ya kulla dangantaka ta kud da kud da Allah.—Zab. 19:1, 7, 14.

11. Idan muna kaunar Allah, mene ne ya kamata mu yi da koyarwar Littafi Mai Tsarki da Jehobah yake tanadarwa a yau? (Ka duba hoton da ke shafi na 23.)

11 A yau Jehobah yana koya mana abubuwa da yawa game da kansa da nufinsa da halittunsa da kuma Kalmarsa. Mutanen duniya sun ɗauki biɗan ilimi a jami’a da kuma manyan makarantu da muhimmanci sosai. Amma mutane da yawa da suka je irin waɗannan makarantun sun yi rashin bangaskiya kuma sun daina kaunar Allah. Amma, Jehobah yana son mu sami ilimi da hikima da kuma fahimi, wato yana son mu yi amfani da abin da muka koya daga gare shi don mu taimakawa kanmu da kuma wasu. (Mis. 4:5-7) Nufin Allah shi ne “dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:4) Muna nuna kaunarmu ga Jehobah ta wajen yin wa’azin bishara da kuma taimakon mutane su fahimci nufin Allah ga ’yan Adam.—Karanta Zabura 66:16, 17.

12. Ta yaya wata matashiya ta nuna godiya ga tanadin da Jehobah yake yi?

12 Matasa ma za su iya nuna cewa suna kaunar Jehobah ta wajen nuna godiya don abubuwan da ya yi tanadinsu. Wata yarinya mai suna Shannon ta ce, sa’ad da take ’yar shekara 11, da ita da kanwarta ’yar shekara 10 sun halarci wani Taron Gunduma na “Godly Devotion” (Ibada ga Allah) tare da iyayensu. Sa’ad da ake ba da wani jawabi, an gaya wa matasa su zauna a wani bangare na musamman da aka keɓe. Ta ɗan yi fargaba. Amma ta yi farin ciki sosai sa’ad da aka ba kowane matashi kyautar wani littafi mai jigo Questions Young People Ask—Answers That Work. Ta yaya wannan kyautar ya sa Shannon ta ji game da Jehobah Allah? Ta ce: “A lokacin ne na san cewa Jehobah ya wanzu da gaske kuma yana kaunata sosai.” Shannon ta daɗa cewa: “Muna farin ciki matuka cewa Jehobah Allah ya ba mu wannan kyakkyawar kyauta!”

KA KARƁI SHAWARA DA KUMA HORO DA ALLAH YAKE YI MANA

13, 14. Mene ne ya kamata mu yi sa’ad da Jehobah ya yi mana horo kuma me ya sa?

13 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wanda Ubangiji yake kauna shi yake tsauta wa: kamar yadda uba yakan yi wa ɗan da yake jin daɗinsa.” (Mis. 3:12) Mene ne ya kamata mu yi sa’ad da aka ba mu gargaɗi? Manzo Bulus ya ce: “Kowane irin horo ana ganinsa ba abin faranta zuciya ba, amma abin ban ciwo ne.” Hakan ba ya nufin cewa Bulus yana rage muhimmanci ko kuma amfanin horo, don ya ci gaba da cewa: “Amma daga baya yakan ba da amfani mai salama watau na adalci ke nan ga waɗanda sun wāsu ta wurinsa.” (Ibran. 12:11) Idan muna kaunar Jehobah, ba za mu yi fushi idan ya yi mana horo ba kuma ba za mu guji shawararsa ba. Ko da yake, hakan ba zai yi wa wasu sauki ba, amma kaunarmu ga Allah za ta taimaka mana.

14 A kwanakin Malakai, Yahudawa da yawa ba su saurari Jehobah ba. Bai dame su ba cewa hadayunsu ba sa faranta wa Jehobah rai. Saboda haka, Jehobah ya yi musu gargaɗi sosai. (Karanta Malakai 1:12, 13.) Yanayin ya yi muni sosai don Jehobah ya ce: “Zan aukar muku da la’ana, zan la’antar da albarkunku. Ko yanzu ma na riga na la’antar da su domin ba ku rike umurnina a zuciyarku ba.” (Mal. 2:1, 2, LMT) Hakika, kin bin dokokin Jehobah da gangan zai kawo mugun sakamako.

Wata ’yar’uwa tana kallon tufafi da ake yayinsu a duniya da ke wani shago

Ka bi shawarar Allah maimakon ka’idodin wannan duniyar (Ka duba sakin layi na 15)

15. Wane hali ne ya wajaba mu guje wa a wannan duniya?

15 Duniyar Shaiɗan tana karfafa mutane su zama masu fahariya da kuma son kai. Mutane da yawa ba sa son karɓan shawara ko kuma a gaya musu abin da za su yi. Wasu da suke karɓan shawara suna yin hakan don ya zama dole. Amma, an gargaɗi Kiristoci kada su “kamantu bisa ga kamar wannan zamani.” Ya kamata mu san kuma mu bi “nufin nan na Allah mai-kyau.” (Rom. 12:2) Jehobah yana ba mu shawara a kan kari ta wurin kungiyarsa a kan batutuwa da yawa, kamar yadda maza da mata za su bi da juna da abokanmu da kuma nishaɗin da muke yi. Idan muka bi waɗannan shawarwarin, muna nuna cewa muna godiya kuma muna kaunar Jehobah da dukan zuciyarmu.—Yoh. 14:31; Rom. 6:17.

KA DOGARA GA JEHOBAH DON YA TAIMAKE KA KUMA YA KĀRE KA

16, 17. (a) Me ya sa ya kamata mu nemi ja-gorar Jehobah sa’ad da muke tsai da shawarwari? (b) Mene ne Isra’ilawa suka yi maimakon su dogara ga Jehobah?

16 Idan yara suka hango masifa, sukan nemi taimakon iyayensu. Yayin da suke girma, sai su soma tsai da shawarwari da kansu don suna gani cewa sun waye. Hakan ba abin mamaki ba ne don suna girma. Amma, waɗanda suke da dangantaka ta kud da kud da iyayensu sukan nemi shawararsu kafin su tsai da shawara. Hakazalika, Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki kuma yana taimaka mana mu so nufinsa kuma mu aikata. Saboda haka, idan muna ɗaukan wasu matakai ba tare da neman shawararsa ba, hakan zai nuna cewa ba ma kaunarsa.—Filib. 2:13.

17 A zamanin Sama’ila, Filistiyawa sun ci Isra’ila da yaki. A maimakon su nemi ja-gora daga wurin Jehobah game da matakin da ya kamata su ɗauka, sai suka tsai da shawara: “Bari mu je mu ɗauki sanduki na alkawarin Ubangiji daga cikin Shiloh, mu kawo shi wurinmu, domin ya shigo a tsakaninmu, ya cece mu daga hannun abokan gabanmu.” Mene ne sakamakon? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Aka yi babbar kisa kwarai: gama na wajen Isra’ila mutum zambar talatin [30,000], dakarai, suka fāɗi. Kuma aka kama sanduki na Allah.” (1 Sam. 4:2-4, 10, 11) Isra’ilawan suna gani cewa Jehobah zai kasance tare da su idan suka ɗauki sanduki zuwa bakin dāga. Amma a gaskiya, ba su nemi ja-gorar Jehobah ba, sun bi nasu ra’ayin kuma hakan ya haifar da mugun sakamako.—Karanta Misalai 14:12.

18. Mene ne ya kamata mu yi idan muna kaunar Jehobah?

18 Wani marubucin zabura da yake kaunar Jehobah sosai ya ce: “Ka kafa bege ga Allah: gama duk da haka zan yabe shi saboda taimakon fuskarsa. Ya Allahna, raina yana tagumi a cikina: Domin wannan ina tunawa da kai.” (Zab. 42:5, 6) Kamar wannan marubucin zabura, kana kaunar Ubanmu wanda yake sama kuma kana dogara gare shi kuwa? Ko da ka ce e, za ka iya kara dogara gare shi da dukan zuciyarka bisa wannan shawarar da ke Littafi Mai Tsarki: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.”—Mis. 3:5, 6.

19. A waɗanne hanyoyi ne kake son ka yi kokari ka nuna kana kaunar Jehobah?

19 Da yake Jehobah ne ya fara kaunarmu, ya koya mana yadda za mu nuna muna kaunar sa. Bari mu ci gaba da yin bimbini a kan abubuwan da ya yi mana da kuma yadda yake kaunar mu sosai. Kari ga haka, bari mu nuna cewa muna kaunar sa ‘da dukan zuciyarmu, da dukan ranmu, da dukan azancinmu, da dukan karfinmu.’—Mar. 12:30.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba