Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 12/15 pp. 15-19
  • Ka Ci Gaba Da Farin Ciki A Lokacin Wahala

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Ci Gaba Da Farin Ciki A Lokacin Wahala
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah “Allah Mai Farin Ciki”
  • Kasancewa Mai Hankali Yana da Muhimmanci
  • Ka So Yin Nufin Allah
  • “Masu-Farin Zuciya ne Mutane Waɗanda Ubangiji ne Allahnsu!”
  • Bari Jehobah Ya Sanyaya Zuciyarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Ka Dogara Ga Jehobah, “Allah Na Dukan Ta’aziyya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ta Yi Addu’a da Dukan Zuciyarta
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Yadda Za Mu Jimre Da Matsalolinmu Da Gaba Gaɗi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 12/15 pp. 15-19

Ka Ci Gaba Da Farin Ciki A Lokacin Wahala

“Dukan waɗanda su ka dogara gareka [Jehobah] su yi murna, bari su tada murya don farinciki kullum.”—ZAB. 5:11.

1, 2. (a) Waɗanne abubuwa ne suke jawo wahala a yau? (b) Ban da masifu da dukan mutane suke fuskanta a yau, menene Kiristoci na gaskiya za su fuskanta?

SHAIDUN JEHOBAH suna fuskantar masifun da ke faɗa wa dukan ’yan Adam. Mutanen Allah da yawa suna shaida aikata laifi, yaƙi, da kuma rashin adalci. Bala’o’i, talauci, rashin lafiya, da mutuwa suna jawo baƙin ciki sosai. Ya dace da manzo Bulus ya rubuta: “Mun sani dukan talikai suna nishi suna naƙuda tare da mu har yanzu.” (Rom. 8:22) Muna kuma fuskantar sakamakon ajizancinmu. Kamar Sarki Dauda na dā, muna iya cewa: “Kurakuraina sun sha kaina: kamar kaya mai-nauyi sun fi ƙarfina.”—Zab. 38:4.

2 Ban da masifu da dukan ’yan adam suke fuskanta, Kiristoci na gaskiya suna ɗauke da gungumen azaba na alama. (Luk 14:27) Hakika, kamar Yesu, an ƙi jinin almajiransa kuma an tsananta musu. (Mat. 10:22, 23; Yoh. 15:20; 16:2) Saboda haka, bin Kristi na bukatan fama sosai da kuma jimiri yayin da muke jiran albarkar sabuwar duniya.—Mat. 7:13, 14; Luk 13:24.

3. Yaya muka sani cewa Kiristoci ba sa bukatan su sha wahala a rayuwa don su faranta wa Allah rai?

3 Hakan yana nufin cewa Kiristoci na gaskiya ba sa murna da kuma farin ciki a rayuwarsu ne? Za mu riƙa yin baƙin ciki da makoki ne kaɗai a rayuwa har ƙarshe ya zo? Babu shakka, Jehobah yana son mu yi farin ciki yayin da muke jiran cikar alkawuransa. Sau da yawa, Littafi Mai Tsarki ya kwatanta masu bauta na gaskiya a matsayin mutane masu farin ciki. (Karanta Ishaya 65:13, 14.) “Dukan waɗanda su ka dogara gareka [Jehobah] su yi murna, bari su tada murya don farinciki kullum,” in ji Zabura 5:11. Hakika, zai yiwu mutum ya yi farin ciki, ya kasance da kwanciyar rai, da wadar zuci har a lokacin masifu. Bari mu maimaita yadda Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu fuskanci gwajinmu kuma har ila mu yi farin ciki.

Jehobah “Allah Mai Farin Ciki”

4. Yaya Allah ya ji sa’ad aka ƙi ikonsa?

4 Alal misali, ka yi la’akari da Jehobah. A matsayin Allah Maɗaukaki, yana da iko bisa dukan sararin samaniya. Ba ya rashin kome kuma ba ya bukatan taimakon kowa. Duk da cewa ba wanda ya kai shi iko, Jehobah ya yi baƙin ciki sa’ad da ɗaya daga cikin ’ya’yansa na ruhu ya yi tawaye kuma ya zama Shaiɗan. Allah ya yi baƙin ciki kuma sa’ad da wasu cikin mala’iku suka yi tawaye. Ka yi tunanin baƙin cikin da Allah ya yi sa’ad da Adamu da Hauwa’u, fanni na musamman na halittarsa a duniya suka juya masa baya. Tun daga lokacin, biliyoyin ’ya’yansu sun ƙi ikon Jehobah.—Rom. 3:23.

5. Menene musamman ya sa Jehobah baƙin ciki?

5 Har ila, tawayen da Shaiɗan ya soma yana daɗa samun ƙarfi. Shekaru 6,000 yanzu Jehobah yana ganin ayyuka na bautar gumaka, mugunta, kisa, da lalata. (Far. 6:5, 6, 11, 12) Bugu da ƙari, ya ji mugun ƙaryace-ƙaryace da kuma saɓo. Har masu bauta ta gaskiya ga Allah a wani lokaci sun ɓata masa rai. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta irin wannan yanayin da kalaman nan: “So nawa suka tayar masa a cikin jeji, suka ɓata masa rai a cikin hamada! Suka juya suka jarabci Allah, suka cakuni Mai-tsarki na Isra’ila.” (Zab. 78:40, 41) Babu shakka Jehobah ya yi baƙin ciki sosai sa’ad da mutanensa suka ƙi shi. (Irm. 3:1-10) A bayyane yake cewa mugayen abubuwa suna faruwa, kuma Jehobah yana baƙin ciki sosai sa’ad da suka faru.—Karanta Ishaya 63:9, 10.

6. Yaya Allah yake fuskantar yanayin da ke kawo baƙin ciki?

6 Abubuwan sa sanyin gwiwa da baƙin ciki da suka faru ba su hana Jehobah ɗaukan mataki ba. Sa’ad da matsala ta taso, Jehobah ya ɗauki mataki nan da nan don ya rage mugun sakamakon abin da ya faru. Ya kuma ɗauki matakai na dogon lokaci don nufinsa ya cika a ƙarshe. Domin waɗannan ayyuka masu kyau da ya yi, da farin ciki Jehobah yana sauraron kunita ikon mallakarsa da kuma albarka da hakan zai kawo ga waɗanda suke bauta masa da aminci. (Zab. 104:31) Hakika, duk da zargin da ake yi masa, Jehobah ya ci gaba da zama “Allah mai [“farin ciki,” NW].”—1 Tim. 1:11; Zab. 16:11.

7, 8. Sa’ad da abubuwa ba su faru yadda muke so ba, ta yaya za mu yi koyi da Jehobah?

7 Hakika, ba za mu iya gwada kanmu da Jehobah ba idan ya zo ga magance matsaloli. Har ila, muna iya yin koyi da Jehobah sa’ad da muke fuskantar matsaloli. Daidai ne mu yi baƙin ciki sa’ad da mugun abubuwa suka faru, amma bai kamata mu ci gaba da kasancewa a irin wannan yanayin ba. Domin an halicce mu a cikin surar Jehobah, muna da hankali da kuma hikima, waɗanda ke sa mu bincika matsalolinmu kuma mu ɗauki mataki mai kyau a duk lokacin da ya yiwu.

8 Wani abu mai muhimmanci da zai taimaka mana mu bi da matsaloli na rayuwa shi ne fahimtar cewa akwai wasu abubuwa da suka fi ƙarfinmu. Yawan damuwa game da irin waɗannan al’amura zai iya ƙara mana baƙin ciki kuma ya hana mu farin ciki da ke tattare da bauta ta gaskiya. Bayan mun ɗauki matakan da suka dace don mu magance wata matsala, ya fi kyau mu daina tunani ainun game da matsalolinmu kuma mu mai da hankali ga abubuwa da za su fi kawo amfani. Labaran da ke gaba da ke cikin Littafi Mai Tsarki sun nuna wannan batun da kyau.

Kasancewa Mai Hankali Yana da Muhimmanci

9. Ta yaya Hannatu ta nuna cewa ita mai hankali ce?

9 Ka yi la’akari da misalin Hannatu, wadda daga baya ta zama mahaifiyar annabi Sama’ila. Ta yi sanyin gwiwa domin ta kasa haihuwa. An yi mata gori domin ita bakararriya ce. A wasu lokatai, Hannatu takan yi sanyin gwiwa sosai har ta yi kuka kuma ta ƙi cin abinci. (1 Sam. 1:2-7) A wata ziyarar da ta kai wuri mai tsarki na Jehobah, Hannatu ta yi “ɓacin rai, ta yi addu’a ga Ubangiji, ta yi kuka kuma da zafi.” (1 Sam. 1:10) Bayan da Hannatu ta gaya wa Jehobah yadda take ji, Eli babban firist ya je ya same ta ya ce: “Je ki dai da salama: Allah kuwa na Isra’ila shi ba ki roƙonki da kika roƙa a gareshi.” (1 Sam. 1:17) A wannan lokacin, Hannatu ta fahimci cewa ta yi iyakar ƙoƙarinta. Ba za ta iya yin kome ba game da rashin haihuwarta. Hannatu ta nuna cewa ita mai hankali ce. Sai ta “kama hanyarta, ta kuwa ci, fuskarta ba ta ƙara nuna baƙinciki ba.”—1 Sam. 1:18.

10. Wane irin ra’ayi da ya dace ne Bulus ya nuna sa’ad da ya fuskanci wata matsala da ba zai iya magancewa ba?

10 Manzo Bulus ya nuna irin wannan halin sa’ad da ya fuskanci wahala. Yana da ciwo da ke sa shi baƙin ciki sosai. Ya kira shi “masuki cikin jiki.” (2 Kor. 12:7) Ko da wane irin ciwo ne, Bulus ya yi iyakar ƙoƙarinsa ya kawar da wannan damuwa, ya yi addu’a ga Jehobah don ya samu sauƙi. Sau nawa ne Bulus ya roƙi Jehobah game da wannan batun? Sau uku. Bayan na ukun, Allah ya bayyana wa Bulus cewa ba za a cire masa wannan “masuki cikin jiki” ta hanyar mu’ujiza ba. Bulus ya amince da hakan kuma ya mai da hankali ga bauta wa Jehobah sosai.—Karanta 2 Korantiyawa 12:8-10.

11. Wane hakki ne addu’a da roƙe-roƙe suke da shi wajen sa mu jimre da masifu?

11 Waɗannan misalan ba sa nufin cewa mu daina yin addu’a ga Jehobah game da batutuwan da ke damunmu. (Zab. 86:7) Akasin haka, Kalmar Allah ta roƙe mu: “Kada ku yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah.” Yaya Jehobah zai amsa irin waɗannan roƙe-roƙe da addu’o’i? Littafi Mai Tsarki ya daɗa: “Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku da tunaninku cikin Kristi Yesu.” (Filib. 4:6, 7) Hakika, mai yiwuwa Jehobah bai zai cire matsalarmu ba, amma zai amsa addu’o’inmu ta wajen tsare hankalinmu. Bayan mun yi addu’a game da wani batu, zuciyarmu za ta natsu kuma za mu fahimci haɗarin ƙyale alhini ya sha kanmu.

Ka So Yin Nufin Allah

12. Me ya sa yin sanyin gwiwa da daɗewa yake da lahani?

12 Misalai 24:10 ta ce: “Idan ka yi suwu cikin ranar ƙunci, ƙarfinka kaɗanna ne.” Wani karin magana ya ce: “Ta wurin ɓacin zuciya ruhu ya kan karai.” (Mis. 15:13) Wasu Kiristoci saboda karayar da suka yi, sun daina karanta Littafi Mai Tsarki kuma sun daina yin bimbini game da Kalmar Allah. Addu’o’insu sun zama sama-sama kawai, kuma suna iya ware kansu daga ’yan’uwa masu bi. A bayyane yake cewa kasancewa a yanayin baƙin ciki da daɗewa yana da lahani.—Mis. 18:1, 14.

13. Waɗanne ayyuka za su taimaka wajen kawar da sanyin gwiwa kuma su sa mu farin ciki?

13 A wani bangare kuma, kasancewa da ra’ayin da ya dace zai taimaka mana mu mai da hankali ga fannoni na rayuwarmu da za su sa mu farin ciki. Dauda ya rubuta: “Murna na ke yi in yi nufinka, ya Allahna.” (Zab. 40:8) Idan muna da damuwa a rayuwarmu, bai kamata mu daina yin bautarmu a kai a kai ba. Hakika, hanya mai kyau na yaƙar baƙin ciki ita ce yin ayyukan da ke kawo farin ciki. Jehobah ya gaya mana cewa za mu iya samun farin ciki wajen karanta Kalmarsa da kuma bincika ta a kai a kai. (Zab. 1:1, 2; Yaƙ. 1:25) Daga Nassosi Masu Tsarki da kuma taron Kirista, muna jin “maganar alheri” da take ƙarfafa mu kuma take faranta zuciyarmu.—Mis. 12:25; 16:24.

14. Wane tabbaci ne daga wurin Jehobah yake sa mu farin ciki a yanzu?

14 Allah ya ba mu dalilai da yawa na yin farin ciki. Alkawarinsa na ceto shi ne dalili na musamman na yin farin ciki. (Zab. 13:5) Mun san cewa ko da menene yake faruwa da mu a yanzu, a ƙarshe Allah zai saka wa waɗanda suke biɗansa. (Karanta Mai-Wa’azi 8:12.) Annabi Habakkuk ya furta irin wannan tabbaci da kyau sa’ad da ya rubuta: “Ko itacen ɓaure ba ya yi fure ba, ba kuwa ’ya’ya a cikin kuringar anab ba; wahalar zaitun ta zama banza, gonaki ba su bada abinci ba: Ko da tumaki ba su ribbababanya a garkensu ba, ba a iske kuma shanu a dangwalinsu ba; duk da haka zan yi murna cikin Ubangiji; zan yi murna a cikin Allah mai-cetona.”—Hab. 3:17, 18.

“Masu-Farin Zuciya ne Mutane Waɗanda Ubangiji ne Allahnsu!”

15, 16. Ka ambata wasu cikin kyautar Allah da za mu iya more yayin da muke jiran albarka ta nan gaba.

15 Yayin da muke jira nan gaba mai ban al’ajabi da aka shirya mana, nufin Jehobah shi ne mu more abubuwa masu kyau da ya ba mu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Na sani babu abin da ya fi masu, kamar su yi murna, su kāma aika nagarta dukan kwanakin ransu. Kowane mutum kuma shi ci, shi sha, shi ji daɗi cikin dukan aikinsa; wannan kyautar Allah ne.” (M. Wa. 3:12, 13) “Aika nagarta” ya ƙunshi yin nagargarun ayyuka domin wasu. Yesu ya ce bayarwa ta fi karɓa albarka. Ayyukan alheri ga abokiyar aurenmu, yaranmu, iyayenmu, da sauran dangi yana kawo gamsuwa mai yawa. (Mis. 3:27) Nuna juyayi, karɓan baƙi, da kuma gafarta wa ’yan’uwanmu na ruhaniya yana kawo farin ciki sosai, kuma yana faranta wa Jehobah rai. (Gal. 6:10; Kol. 3:12-14; 1 Bit. 4:8, 9) Kuma cika hidimarmu tare da halin sadaukar da kai yana kawo albarka ƙwarai.

16 Kalmomi da ke Mai-Wa’azi da aka yi ƙaulinsa a baya sun ambata annashuwa masu sauƙi ta rayuwa kamar cin abinci da abin sha. Hakika, har sa’ad da muke fuskantar gwaji, muna iya yin farin ciki a duk kyauta na zahiri da muka samu daga wajen Jehobah. Bugu da ƙari, ba ma biyan kome don mu more faɗuwar rana mai ban al’ajabi, tsarin ƙasa mai ban mamaki, halayen dabbobi masu ban dariya, da sauran halittu masu ban al’ajabi, duk da haka suna iya cika mu da mamaki kuma suna sa mu farin ciki. Yayin da muke tunani game da irin waɗannan abubuwa, ƙaunarmu ga Jehobah za ta ƙaru, don shi ne mai ba da dukan abubuwa masu kyau.

17. Menene zai kawo mana sauƙi gabaki ɗaya daga wahaloli, amma kafin lokacin, menene ke ƙarfafa mu?

17 A ƙarshe, ƙaunarmu ga Allah, yin biyayya ga umurninsa, da kuma bangaskiya ga hadayar fansa za su sa mu samu sauƙi gabaki ɗaya daga wahaloli na rayuwa ta ajizanci kuma su sa mu yi farin ciki na dindindin. (1 Yoh. 5:3) Kafin lokacin, muna samun ta’aziyya ta wajen sanin cewa Jehobah yana sane da dukan abubuwa da ke damunmu. Dauda ya rubuta: “Zan yi murna in yi farinciki cikin jinƙanka: Gama kā ga ƙuncina; Kā san masifun raina.” (Zab. 31:7) Ƙaunarsa a gare mu za ta motsa Jehobah ya cece mu daga masifa.—Zab. 34:19.

18. Me ya sa ya kamata farin ciki ya sha kan mutanen Allah?

18 Yayin da muke jiran cikar alkawarunsa, bari mu yi koyi da Jehobah, Allah mai farin ciki. Kada mu ƙyale baƙin ciki ya hana mu ci gaba a hidimarmu ga Allah. Sa’ad da matsaloli suka taso, bari tunanin kirki da hikima su yi mana ja-gora. Jehobah zai taimaka mana mu kame kanmu kuma mu ɗauka kowane matakai da za su yiwu don mu rage mugun sakamako na masifu. Bari mu yi murna cikin abubuwa masu kyau da yake yi mana tanadinsu, na zahiri da kuma na ruhaniya. Ta wajen kasance kusa ga Allah, za mu iya yin farin ciki domin “masu-farin zuciya ne mutane, waɗanda Ubangiji ne Allahnsu.”—Zab. 144:15.

Menene Ka Koya?

• Sa’ad da muke jimre da wahaloli, ta yaya za mu iya yin koyi da Jehobah?

• Ta yaya sauƙin hali zai taimaka mana mu jimre da wahaloli?

• A lokacin wahala, yaya za mu yi farin ciki wajen yin nufin Allah?

[Hotunan da ke shafi na 16]

Jehobah yana baƙin ciki don miyagun abubuwa da suke faruwa

[Inda aka Dauko]

© G.M.B. Akash/Panos Pictures

[Hotunan da ke shafi na 18]

Jehobah ya ba mu abubuwa da za su sa mu ci gaba da farin ciki

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba