Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • th darasi na 11 p. 14
  • Ka Yi Magana da Kuzari

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Magana da Kuzari
  • Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Makamantan Littattafai
  • Maganarka ta Ratsa Zuciya
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Yin Koyarwa da Himma
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Ka Nuna Kauna da Tausayi
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Mutane Su Koyi Darasi Daga Jawabin
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
Dubi Ƙari
Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
th darasi na 11 p. 14

DARASI NA 11

Ka Yi Magana da Kuzari

Nassin da aka rubuta

Romawa 12:11

ABIN DA ZA KA YI: Ka ƙarfafa masu sauraronka ta wurin yin magana da himma.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka fahimci batun da kyau. A lokacin da kake shiri, ka yi tunani sosai a kan muhimmancin saƙon. Ka san batun sosai domin ka iya bayyana shi daga zuciyarka.

  • Ka yi tunani a kan masu sauraronka. Ka yi tunani a kan yadda masu sauraro za su amfana daga abin da za ka karanta ko kuma koyar. Ka yi tunani a kan hanyoyin da za ka gabatar da saƙon da kyau don masu sauraronka su amfana.

  • Ka sa jawabin ya yi daɗi. Ka yi magana da himma. Motsin hannayenka, da yanayin fuskarka su nuna yadda kake ji game da batun da kake tattaunawa.

    Shawara mai amfani

    Kada ka riƙa motsa hannayenka a hanya ɗaya yayin da kake magana, don hakan zai ɗauke hankalin masu sauraronka. Ka motsa hannayenka yadda zai jitu da abin da kake faɗa. Yayin da kake koyar da muhimman darussa ko kana ƙarfafa masu sauraronka su ɗauki wani mataki, ka yi magana da himma. Idan ka fara jawabinka da babbar murya daga farko har ƙarshe, masu sauraro za su gaji da jawabin.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba