Bangaskiya Tana Sa Mu Kasance da Ƙarfin Zuciya
BANGASKIYA tana sa mu kasance da ƙarfi sosai. Alal misali, Shaiɗan yana so ya sa mu ɓata dangantakarmu da Jehobah, amma bangaskiya tana taimaka mana mu “kashe kibiyoyi na wutar Mugun nan.” (Afis. 6:16) Idan muna da bangaskiya, muna iya jimre matsaloli masu tsanani. Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa: “Idan kuna da bangaskiyar da ta yi ƙanƙanta kamar ƙwayar mastad, za ku iya ce wa tudun nan ya tashi daga nan zuwa can, kuma zai tashi.” (Mat. 17:20) Da yake mun san cewa bangaskiya tana iya sa dangantakarmu da Jehobah ta yi ƙarfi, muna bukatar mu yi tunani a kan waɗannan tambayoyin: Mene ne bangaskiya? Ta yaya ra’ayinmu yake shafar bangaskiyarmu? Ta yaya za mu iya ƙarfafa bangaskiyarmu? Kuma da waye ne ya kamata mu yi imani?—Rom. 4:3.
MENE NE BANGASKIYA?
Bangaskiya ba kawai amincewa da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce ba ne. Domin “ko aljanu ma sun gaskata” cewa Allah yana wanzuwa da gaske, kuma suna “rawar jiki.” (Yaƙ. 2:19) To mene ne bangaskiya take nufi?
Kamar yadda muka gaskata cewa a koyaushe za a yi dare da rana, mun gaskata cewa maganar Allah za ta cika
Littafi Mai Tsarki ya bayyana abin da bangaskiya take nufi. Na ɗaya, “bangaskiya ita ce kasancewa da tabbaci a kan abin da muka sa zuciya a kai.” (Ibran. 11:1a) Idan kana da bangaskiya, za ka yi imani cewa dukan abubuwan da Jehobah ya faɗa gaskiya ne kuma za su faru. Alal misali, Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa cewa: “Na kafa yarjejeniya tare da rana da dare cewa za su dinga bayyana a daidai lokacin da na shirya musu. Idan ka iya karya yarjejeniyar nan, to, za a iya karya yarjejeniyata da bawana Dawuda.” (Irm. 33:20, 21) Ka taɓa jin tsoro cewa gari ba zai waye ba ko kuma dare ba zai yi ba? Idan ba ka shakka cewa gari zai waye ko kuma dare zai yi, shin zai dace ka yi shakka cewa Mahaliccinmu ba zai cika alkawuransa ba? A’a!—Isha. 55:10, 11; Mat. 5:18.
Na biyu, bangaskiya ‘zaman tabbaci ne kuma game da abin da ba a iya gani.’ Littafi Mai Tsarki ya ce bangaskiya kasancewa da tabbaci ne cewa “abin da ba a iya gani” zai faru. (Ibran. 11:1b) Ta yaya? Alal misali, a ce wani yaro ya tambaye ka, ‘Me ya sa ka gaskata cewa akwai iska?’ Ko da yake ba ka taɓa ganin iska ba, za ka gaya wa yaron abubuwan da suka sa ka gaskata cewa akwai iska, kamar numfashi da yadda iska ke kaɗa abubuwa da dai sauransu. Sa’ad da yaron ya gaskata cewa waɗannan abubuwan suna wanzuwa, zai fahimci cewa mutum zai iya gaskata da abin da ba zai iya gani ba. Hakazalika, kafin mu kasance da bangaskiya muna bukatar mu yi imani cewa Allah zai cika dukan alkawuransa.—Rom. 1:20.
MU KASANCE DA RA’AYIN DA YA DACE
Da yake bangaskiya kasancewa da tabbaci ne, hakan yana nufin cewa kafin mutum ya zama mai bangaskiya, dole ne ya ‘san gaskiya’ game da Allah. (1 Tim. 2:4) Amma ba abin da mutum yake bukatar yi kaɗai ba ke nan! Manzo Bulus ya rubuta cewa: ‘Da zuciya ne akan ba da gaskiya.’ (Rom. 10:10) Ba kawai amincewa da gaskiya mutum yake bukatar ya yi ba, amma yana bukatar ya daraja gaskiyar. Yin hakan ne zai motsa mutum ya riƙa yin abubuwan da ke faranta wa Allah rai. (Yaƙ. 2:20) Mutumin da ba ya daraja gaskiya game da Allah zai ƙi tabbacin da yake gani, ya ƙi canja abin da ya yi imani da shi kuma ya ci gaba da yin abin da ya ga dama. (2 Bit. 3:3, 4; Yahu. 18) Shi ya sa a zamanin dā, ba dukan waɗanda suka ga mu’ujizai ne suka kasance da bangaskiya ba. (L. Ƙid. 14:11; Yoh. 12:37) Mutanen da suke son gaskiya ne kaɗai ruhun Allah yake taimaka wa su kasance da bangaskiya.—Gal. 5:22; 2 Tas. 2:10, 11.
YADDA DAUDA YA ZAMA MAI BANGASKIYA SOSAI
Sarki Dauda yana cikin mutane masu bangaskiya sosai. (Ibran. 11:32, 33) Amma ba kowa a iyalinsa ba ne yake da irin bangaskiyarsa ba. Alal misali, akwai lokacin da Eliyab yayan Dauda ya nuna rashin bangaskiya ta wajen tsauta wa Dauda domin yana so ya yaƙi Goliyat. (1 Sam. 17:26-28) Babu wanda aka haifa da bangaskiya kuma babu wanda ya gāji wannan halin. Don haka, Dauda ya kasance da bangaskiya ne domin ya ƙulla dangantaka da Allah.
A littafin Zabura ta 27, Dauda ya bayyana abin da ya taimaka masa ya kasance da bangaskiya. (Aya ta 1) Dauda ya yi tunani a kan abubuwan da ya fuskanta a dā da kuma yadda Jehobah ya taimaka masa ya yi nasara a kan maƙiyansa. (Ayoyi 2 da 3) Ya daraja haikalin Jehobah sosai. (Aya ta 4) Ya yi ibada tare da mutanen da ke bauta wa Allah. (Aya ta 6) Ya yi addu’a ga Jehobah da zuciya ɗaya. (Ayoyi 7 da 8) Dauda ya ce yana so Allah ya koya masa hanyoyinsa. (Aya ta 11) Dauda ya ɗauki bangaskiya da muhimmanci sosai, har ya ce da ba shi da bangaskiya, ba zai iya jimrewa ba.—Aya ta 13.
YADDA ZA MU ƘARFAFA BANGASKIYARMU
Za ka iya kasancewa da bangaskiya kamar Dauda idan ka yi koyi da halayen da aka bayyana a Zabura ta 27. Don mu kasance da wannan halin, muna bukatar mu riƙa nazarin Kalmar Allah da kuma littattafanmu sosai. (Zab. 1:2, 3) Ka yi tunani sosai a kan abin da ka yi nazari a kai. Idan muka yi tunani sosai a kan abin da muka yi nazarinsa, hakan zai sa mu daɗa daraja Jehobah. Da yake kana daraja Jehobah, za ka so kasancewa da bangaskiya ta wajen bauta masa a cikin ikilisiya da kuma yi wa mutane wa’azi. (Ibran. 10:23-25) Ƙari ga haka, muna nuna bangaskiya sa’ad da muka yi “addu’a kullum” kuma ba mu fasa yin hakan ba. (Luk. 18:1-8) Saboda haka, “ku yi ta yin addu’a babu fasawa” kuma ku gaskata cewa Jehobah “ne mai lura da ku.” (1 Tas. 5:17; 1 Bit. 5:7) Bangaskiya tana motsa mu mu riƙa yin abin da ya dace, kuma idan muna yin hakan, bangaskiyarmu za ta yi ƙarfi.—Yaƙ. 2:22.
KU YI IMANI DA YESU
A daren ƙarshe kafin Yesu ya mutu, ya gaya wa mabiyansa cewa: “Ku ba da gaskiya ga Allah, ku kuma ba da gaskiya gare ni.” (Yoh. 14:1) Don haka, muna bukatar mu yi imani ga Jehobah da kuma Yesu. Ta yaya za ka yi imani da Yesu? Bari mu tattauna hanyoyi uku.
Mene ne yin imani da Yesu yake nufi?
Na ɗaya, ka riƙa tuna cewa dominka ne Allah ya ba da kyautar fansa. Manzo Bulus ya ce: “Wannan rayuwa ta jikin da nake yi, rayuwa ce ta wurin dogara ga Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni har ya ba da ransa domina.” (Gal. 2:20) Idan ka yi imani da Yesu, za ka gaskata cewa hadayarsa ta shafe ka, ita ce za ta sa a gafarta zunubanka kuma hakan zai nuna cewa Allah yana ƙaunar ka. (Rom. 8:32, 38, 39; Afis. 1:7) Yin hakan zai taimaka maka ka daina damuwa don kurakuren da ka yi a dā.—2 Tas. 2:16, 17.
Na biyu, ka kusaci Jehobah ta addu’a wadda fansar Yesu ce ta sa hakan ya yiwu. Don fansar Yesu, za mu iya addu’a ga Jehobah “domin mu karɓi jinƙai, mu kuma sami alheri wanda zai taimake mu a lokacin bukata.” (Ibran. 4:15, 16; 10:19-22) Addu’a tana taimaka mana mu ƙuduri niyyar guje wa yin zunubi.—Luk. 22:40.
Na uku, ku yi biyayya ga Yesu. Manzo Yohanna ya ce: “Dukan wanda yake ba da gaskiya ga Ɗan, yana da rai na har abada. Amma duk wanda ya ƙi Ɗan, ba zai sami rai ba, sai dai fushin Allah ya kasance a kansa.” (Yoh. 3:36) Ka lura cewa Yohanna ya kwatanta yin imani da yin biyayya. Don haka, idan ka yi wa Yesu biyayya, hakan yana nuna cewa ka yi imani da shi. Za ka yi wa Yesu biyayya idan ka bi dokar Kristi, wato dukan koyarwarsa da kuma umurninsa. (Gal. 6:2) Ƙari ga haka, kana wa Yesu biyayya idan ka bi ja-gorancin “bawan nan mai aminci.” (Mat. 24:45) Idan kana yi wa Yesu biyayya, za ka sami ƙarfin jimre matsaloli ko da suna da ban-tsoro kamar guguwa.—Luk. 6:47, 48.
“KU YI TA GINA KANKU A KAN BANGASKIYARKU NAN MAFI TSARKI”
Akwai lokacin da wani mutum ya gaya wa Yesu cewa: “Na ba da gaskiya, ka taimake ni in ƙara gaskatawa!” (Mar. 9:24) Mutumin nan yana da bangaskiya, amma ya fahimci cewa yana bukatar ya ƙara ba da gaskiya. Kamar wannan mutumin, mu ma za mu iya fuskantar yanayin da za mu bukaci ƙarin bangaskiya. Kuma dukanmu muna iya ƙarfafa bangaskiyarmu a yanzu. Kamar yadda muka gani, za mu ƙarfafa bangaskiyarmu idan muna yin nazarin Kalmar Allah da yin tunani a kan abin da muka nazarta. Yin hakan zai sa mu daɗa daraja Jehobah. Ƙari ga haka, bangaskiyarmu za ta daɗa ƙarfi idan muna bauta wa Jehobah tare da ’yan’uwanmu da yin wa’azi da kuma nacewa da yin addu’a. Idan muka ƙarfafa bangaskiyarmu ga Allah, za mu sami lada sosai. Kalmar Allah ta ce: “Ku waɗanda nake ƙauna, ku yi ta gina kanku a kan bangaskiyarku, . . . domin ku kiyaye kanku cikin ƙaunar Allah.”—Yahu. 20, 21.