Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Mayu pp. 14-19
  • Mu Ci Gaba da Jiran Birnin da Zai Dawwama

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mu Ci Gaba da Jiran Birnin da Zai Dawwama
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA DOGARA GA JEHOBAH DOMIN BA ZAI TAƁA BARIN KA BA
  • MU YI BIYAYYA GA WAƊANDA SUKE JA-GORANCI
  • MU ƘAUNACI JUNA KUMA MU RIƘA YIN ALHERI
  • MENE NE ZAI FARU A NAN GABA
  • Wasiƙa da Za Ta Taimake Mu Mu Jimre har Karshe
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Yana da Kyau Mu Kusaci ꞌYanꞌuwa!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Mayu pp. 14-19

TALIFIN NAZARI NA 21

WAƘA TA 21 Mu Ci Gaba da Sa Mulkin Allah Farko

Mu Ci Gaba da Jiran Birnin da Zai Dawwama

“Muna dai sa ido ga birnin nan wanda yake zuwa.”—IBRAN. 13:14.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da za mu koya daga Ibraniyawa sura 13, da zai taimaka mana a yau da kuma a nan gaba.

1. Mene ne Yesu ya ce zai faru da Urushalima?

ꞌYAN kwanaki kafin Yesu ya mutu, ya gaya wa mabiyansa wani abin da zai faru a nan gaba. Ya gaya musu cewa a kwana a tashi, sojoji za su “kewaye Urushalima.” (Luk. 21:20) Ya kuma gaya musu cewa da zarar sun ga sojojin, su bar Yahudiya nan da nan.—Luk. 21:​21, 22.

2. Mene ne Bulus ya gaya wa Kiristoci da ke Yahudiya da Urushalima?

2 ꞌYan shekaru kafin sojojin Roma su kewaye Urushalima, manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci da ke Yahudiya wata wasiƙa mai muhimmanci. Wasiƙar ce littafin Ibraniyawa. A wasiƙar, Bulus ya gaya wa Kiristocin da ke Urushalima da Yahudiya abin da zai taimaka musu su kasance a shirye don mawuyacin halin da za su shiga a nan gaba. Mene ne zai faru? Za a halaka Urushalima. Idan Kiristocin suna son su tsira, wajibi ne su yi shirin barin gidajensu da sanaꞌoꞌinsu da dai sauransu. Game da Urushalima, manzo Bulus ya ce: “Ba mu da birni marar shuɗewa a nan . . . amma muna dai sa ido ga birnin nan wanda yake zuwa.”—Ibran. 13:14.

3. Wane birni ne “birnin nan wanda yake da tushe,” kuma me ya sa muke ci gaba da jiran sa?

3 Me yiwuwa, saꞌad da mutane suka ga Kiristocin suna barin Urushalima da Yahudiya, sun yi musu dariya domin suna ganin hakan wawanci ne. A yau ma, mutane suna ganin kamar mu wawaye ne domin ba ma sa neman kuɗi a kan gaba, kuma ba mu yarda cewa ꞌyanꞌadam za su iya warware matsalolin duniya ba. To, me ya sa muka kasance da irin wannan raꞌayin? Domin mun san cewa nan ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai halaka wannan muguwar duniya. Muna sa zuciya a kan “birnin nan wanda yake da tushe” wato, Mulkin Allah wanda yake zuwa. (Ibran. 11:10; Mat. 6:33) A wannan talifin, kowane ƙaramin jigo zai tattauna: (1) yadda abin da Bulus ya gaya wa Kiristoci a ƙarni na farko ya taimaka musu su ci gaba da jiran “birnin nan wanda yake zuwa,” (2) yadda abin da ya faɗa ya taimaka musu su kasance a shirye don lokacin da za a halaka Urushalima, da kuma (3) yadda abin da ya faɗa zai taimaka mana a yau.

KA DOGARA GA JEHOBAH DOMIN BA ZAI TAƁA BARIN KA BA

4. Me ya sa Kiristoci a ƙarni na farko suke ɗaukan Urushalima da muhimmanci?

4 Urushalima wuri ne mai muhimmanci ga Kiristoci a ƙarni na farko. A wurin ne aka kafa ikilisiyar Kirista ta farko a shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu, kuma a wurin ne ꞌyanꞌuwa da suke kula da ayyukan Kiristoci a lokacin suke zama. Ban da haka ma, Kiristoci da yawa suna da gidaje da dukiyoyi da yawa a birnin. Duk da haka, Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa dole ne su bar Urushalima har ma da yankin Yahudiya gabaki ɗaya.—Mat. 24:16.

5. Ta yaya Bulus ya shirya Kiristocin don abin da zai faru da Urushalima?

5 Bulus ya taimaka wa Kiristocin su yi shirin barin Urushalima ta wajen sa su fahimci yadda Jehobah yake ji game da birnin. Bulus ya tuna musu cewa Jehobah ya daina amincewa da firistocin da suke aiki a haikalin, da kuma hadayun da ake bayarwa a wurin. (Ibran. 8:13) Yawancin mazaunan birnin sun ƙi amincewa da Almasihu. Kuma mutane ba sa bukatar su je Urushalima don su bauta wa Jehobah. Ban da haka ma, za a halaka Urushalima da haikalinta.—Luk. 13:​34, 35.

6. Me ya sa Kiristocin suke bukatar gargaɗin da Bulus ya ba su a Ibraniyawa 13:​5, 6?

6 A lokacin da Bulus ya rubuta wa Ibraniyawan wasiƙa, mutane da yawa suna jin daɗin zuwa da kuma zama a Urushalima. Wani marubuci ɗan Roma a lokacin ya ce, Urushalima ne “birnin da aka fi sani a yankin da Urushalima take.” Yahudawa daga wurare da yawa suna zuwa Urushalima sau uku kowace shekara don su yi bukukuwa, kuma hakan yana ƙara bunƙasa tattalin arzikin birnin. Don haka, wataƙila akwai wasu Kiristocin da suke da arziki sosai a birnin. Mai yiwuwa shi ya sa Bulus ya gaya musu cewa: “Ku yi nesa da halin son kuɗi, ku kuma kasance da kwanciyar rai da abin da kuke da shi.” Bayan haka, sai ya yi ƙaulin wani Nassi inda Jehobah ya tabbatar wa bayinsa cewa: “Har abada ba zan bar ka ba, sam sam ba zan yar da kai ba.” (Karanta Ibraniyawa 13:​5, 6; M. Sha. 31:6; Zab. 118:6) Kiristocin da suke zama a Urushalima da yankin Yahudiya sun bukaci su tuna cewa Jehobah ba zai taɓa barin su ba. Me ya sa? Domin jim kaɗan bayan sun sami wasiƙar manzo Bulus, za su bukaci su gudu su bar gidajensu da sanaꞌoꞌinsu da kuma yawancin dukiyoyinsu. Saꞌan nan za su soma rayuwa a wani wuri dabam.

7. Me ya sa yake da kyau mu dogara ga Jehobah da dukan zuciyarmu tun yanzu?

7 Abin da hakan ya koya mana: Nan ba da daɗewa ba, za a soma “azaba mai zafi” wato, ƙunci mai girma kuma za a halaka wannan muguwar duniyar. (Mat. 24:21) Kamar Kiristocin da ke Urushalima a ƙarni na farko, wajibi ne mu kasance da aminci yanzu kuma mu yi shiri don lokacin. (Luk. 21:​34-36) A lokacin ƙunci mai girma, za mu iya rasa gidajenmu ko wasu abubuwa da muke da su. A lokacin muna bukatar mu tabbata cewa Jehobah ba zai taɓa barin mu ba. Amma tun kafin a soma ƙunci mai girma, muna da damar nuna ko wane ne, ko kuma mene ne muke dogara a kai. Zai dace kowannenmu ya tambayi kansa, ‘Shin shawarwarin da nake yankewa da kuma shirye-shiryen da nake yi don nan gaba suna nuna cewa na dogara ga Jehobah ne, ko ga arziki?’ (1 Tim. 6:17) Gaskiyar ita ce, za mu iya koyan darussa da dama masu kyau daga abin da ya faru da Kiristoci a ƙarni na farko, da za su taimaka mana a lokacin ƙunci mai girma. Amma ba wanda ya taɓa shan irin wuyan da za a sha a lokacin ƙunci mai girma. To, ta yaya za mu san abin da za mu yi a lokacin?

MU YI BIYAYYA GA WAƊANDA SUKE JA-GORANCI

8. Mene ne Yesu ya gaya wa almajiransa?

8 ꞌYan shekaru bayan Kiristocin sun sami wasiƙar Bulus, sojojin Roma sun kewaye Urushalima. Da Kiristocin suka ga hakan, sun gane cewa lokaci ya yi da za su gudu su bar Urushalima da Yahudiya, don ba da daɗewa ba za a halaka Urushalima da Yahudiya. (Mat. 24:3; Luk. 21:​20, 24) Amma, ina ne za su gudu su je? Abin da Yesu ya gaya musu kawai shi ne: “Waɗanda suke cikin yankin Yahudiya, su gudu zuwa cikin tuddai.” (Luk. 21:21) Akwai tuddai da yawa a yankin. Don haka, ta yaya za su san wanda za su je?

9. Waɗanne tuddai ne Kiristocin za su iya gudu su je? (Ka kuma duba taswira.)

9 Alal misali, akwai tuddai na yankin Samariya, da na Galili, da tudun Hermon, da tuddan da ke Lebanon, da kuma waɗanda suke tsallaken kogin Urdun. (Ka duba taswira.) Akwai birane a wuraren da tuddan nan suke, kuma mutane za su iya gani kamar ba za a taɓa samun tashin hankali a wuraren ba. Alal misali, birnin Gamla yana kan wani babban tudu mai tsayi sosai, kuma hawan sa bai da sauƙi. Wasu Yahudawa sun ɗauka cewa birnin nan wurin ɓuya ne mai kyau. Amma, sojojin Roma sun kai wa birnin hari, sun yi kacakaca da birnin, kuma sun kashe mutane da yawa.a

Taswirar da ke nuna wasu birane da tuddai a ƙasar Israꞌila a ƙarni na farko. A arewacin Urushalima akwai tuddan Lebanon, da na Galili, da na Samariya, da na Gilead, da kuma tudun Hermon da na Tabor. Biranen da ke arewacin Urushalima su ne Gamla, da Kaisariya, da kuma Pella. A kudancin Urushalima akwai tuddan Yahudiya da na Abarim, da kuma birnin Masada. Taswirar ta kuma nuna yankunan Yahudawa da Romawa suka yaƙa kuma suka ƙwace daga shekara ta 67 B.H.Y. zuwa 73 B.H.Y.

Akwai tuddai da yawa da Kiristoci a ƙarni na farko za su iya gudu su je, amma ba dukan su ne za su iya zuwa su tsira ba (Ka duba sakin layi na 9)


10-11. (a) Ta yaya mai yiwuwa Jehobah ya taimaka wa Kiristocin su san abin da za su yi? (Ibraniyawa 13:​7, 17) (b) Ta yaya Kiristocin suka amfana don sun yi biyayya ga waɗanda suke musu ja-goranci? (Ka kuma duba hoton.)

10 Da alama cewa Jehobah ya yi amfani da waɗanda suke ja-goranci a ikilisiya wajen taimaka wa Kiristocin su san abin da za su yi. Daga baya wani masanin tarihi mai suna Eusebius ya rubuta cewa: “Allah ya yi ma wasu ꞌyanꞌuwa a Urushalima magana ta wahayi cewa Kiristoci su gudu daga Urushalima zuwa Pella, wani birni a Perea.” Pella wuri ne mai kyau da Kiristocin za su iya zuwa. Bai da nesa da Urushalima, don haka, zuwa wurin ba zai yi musu wuya ba. Ƙari ga haka, yawancin mutanen da ke Pella ba Yahudawa ba ne, don haka ba sa ƙoƙarin yi wa Romawa tawaye.—Ka duba taswira.

11 Kiristocin da suka gudu zuwa kan tuddan sun bi shawarar da Bulus ya bayar cewa, “ku yi wa shugabanninku biyayya,” wato waɗanda suke ja-goranci a ikilisiya. (Karanta Ibraniyawa 13:​7, 17.) Da yake sun yi biyayya, hakan ya sa suka tsira. Jehobah bai bar su ba domin sun ci gaba da jiran “birnin nan wanda yake da tushe.” —Ibran. 11:10.

Wasu Kiristoci a ƙarni na farko suna tafiya da kayayyakinsu a yankunan da akwai tuddai.

Pella wuri ne da Kiristocin za su iya zuwa su tsira kuma bai da nesa (Ka duba sakin layi na 10-11)


12-13. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa bayinsa a lokaci mai wuya sosai?

12 Abin da hakan ya koya mana: Jehobah yana amfani da waɗanda suke ja-goranci don ya gaya wa mutanensa abin da yake so su yi. Akwai misalai da yawa a Littafi Mai Tsarki da suka nuna yadda Jehobah yake amfani da mutane masu aminci wajen yi wa mutanensa ja-goranci a lokaci mai wuya. (M. Sha. 31:23; Zab. 77:20) Mu ma a yau muna ganin yadda Jehobah yake amfani da masu yi mana ja-goranci wajen taimaka mana.

13 Alal misali, a lokacin da aka soma annobar korona, ꞌyanꞌuwa da suke ja-goranci sun gaya mana abin da ya kamata mu yi. ꞌYanꞌuwan nan sun gaya wa dattawa yadda ikilisiyoyi za su ci gaba da yin taro da kuma yin ayyukan ibada. ꞌYan watanni bayan ɓarkewar annobar, mun yi taron yanki a yaruka 500 kuma ꞌyanꞌuwa maza da mata sun saurari taron ta intane ko ta talabijin, wasu ma a rediyo suka saurara. Ba a taɓa yin irin wannan taron yankin ba. Duk da annobar, mun ci gaba da samun umurnai daga wurin Jehobah. Hakan ya sa mun kasance da haɗin kai. Muna da tabbaci cewa Jehobah zai ci gaba da taimaka ma ꞌyanꞌuwa da suke ja-goranci, don su tsai da shawarwarin da suka dace. Ko da wace irin matsala ce muka fuskanta a nan gaba, dogara ga Jehobah da kuma biyayya ga dokokinsa, za su taimaka mana mu yi shiri kuma mu tsai da shawarwarin da suka dace a lokacin ƙunci mai girma. Amma wane hali ne kuma zai iya taimaka mana?

MU ƘAUNACI JUNA KUMA MU RIƘA YIN ALHERI

14. Bisa ga Ibraniyawa 13:​1-3, waɗanne abubuwa ne Kiristoci a ƙarni na farko suke bukatar su yi kafin lokacin da za a halaka Urushalima?

14 Idan aka soma ƙunci mai girma, za mu bukaci mu riƙa nuna wa juna ƙauna fiye da yadda muke yi yanzu. A lokacin, za mu bukaci mu bi misalin Kiristocin da suke zama a Urushalima da Yahudiya a ƙarni na farko. Tun dā ma suna ƙaunar juna. (Ibran. 10:​32-34) Amma ꞌyan shekaru kafin a halaka Urushalima, sun bukaci su ƙara ƙaunar juna da kuma nuna alheri. (Karanta Ibraniyawa 13:​1-3.) Mu ma za mu bukaci mu ƙara ƙaunar juna a lokacin ƙunci mai girma.

15. Me ya sa Kiristocin suke bukatar su taimaka kuma su ƙaunaci juna bayan da suka gudu?

15 Bayan da sojojin Roma sun kewaye Urushalima, haka kawai sai suka tafi ba tare da wani dalili ba. Hakan ya ba wa Kiristocin dama su gudu, kuma kayayyakinsu kaɗan ne kawai suka iya ɗaukawa. (Mat. 24:​17, 18) Saboda haka, sun bukaci taimakon juna saꞌad da suke guduwa. Kuma da suka isa Pella, sun bukaci taimakon juna don samun wurin zama da kuma aikin yi. ꞌYanꞌuwa da yawa sun bukaci abinci da riguna da wurin da za su zauna. Ta wurin taimaka wa juna da raba wa juna abin da suke da shi, Kiristocin sun nuna cewa suna ƙaunar juna sosai kuma su masu alheri ne.—Tit. 3:14.

16. Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu a lokacin da suke da bukata? (Ka kuma duba hoton.)

16 Abin da hakan ya koya mana: Zai dace mu ma mu taimaki ꞌyanꞌuwanmu maza da mata a lokacin da suke yanayi mai wuya, don haka zai nuna cewa muna ƙaunar su. Alal misali, ꞌyanꞌuwa da yawa sun taimaki ꞌyanꞌuwa maza da mata da suka yi gudun hijira don yaƙi ko wani balaꞌi. Sun yi wa ꞌyan gudun hijirar tanadin abubuwan da suke bukata kuma sun taimaka da kuma ƙarfafa su su ci gaba da bauta wa Jehobah. Alal misali, wata ꞌyarꞌuwa a Yukiren da ta gudu ta bar gidanta don ana yaƙi ta ce: “Mun ga yadda Jehobah ya yi amfani da ꞌyanꞌuwanmu wajen taimaka mana da kuma kula da mu. Sun marabce mu kuma sun taimaka mana sosai a Yukiren, da Hungary, kuma har yanzu a Jamus, ꞌyanꞌuwanmu sun ci gaba da yin hakan.” Idan muna kula da kuma taimaka ma ꞌyanꞌuwanmu maza da mata a lokacin da suke da bukata, muna aiki tare da Jehobah ke nan.—K. Mag. 19:17; 2 Kor. 1:​3, 4.

Wani ɗanꞌuwa da matarsa da suka tsufa suna marabtar wasu ꞌyanꞌuwa da suka yi gudun hijira zuwa cikin gidansu. ꞌYanꞌuwan sun fito daga gida ɗaya ne. Suna riƙe da akwati guda da kuma wasu jakunkuna.

A yau muna bukatar mu taimaka wa Kiristocin da suka yi gudun hijira (Ka duba sakin layi na 16)


17. Me ya sa yake da muhimmanci sosai mu ƙaunaci ꞌyanꞌuwa kuma mu taimaka musu tun yanzu?

17 Babu shakka, a lokacin ƙunci mai girma, za mu bukaci mu riƙa taimaka wa juna fiye da yadda muke yi yanzu. (Hab. 3:​16-18) Jehobah yana koya mana yadda za mu riƙa ƙaunar juna da kuma taimaka wa juna tun yanzu, domin za mu bukaci yin hakan sosai a lokacin ƙunci mai girma.

MENE NE ZAI FARU A NAN GABA

18. Ta yaya za mu yi koyi da Kiristocin da suka gudu daga Urushalima?

18 Kiristocin da suka yi biyayya kuma suka gudu zuwa kan tuddai sun tsira lokacin da aka halaka Urushalima. Sun gudu sun bar birnin, amma Jehobah bai bar su ba. Mene ne hakan ya koya mana? Ko da yake ba mu san dalla-dalla yadda abubuwa za su faru a nan gaba ba. Yesu ya gaya mana cewa mu zauna da shiri. (Luk. 12:40) Ƙari ga haka, muna da shawarar da Bulus ya rubuta wa Ibraniyawa a ƙarni na farko a wasiƙarsa. Wannan shawarar za ta taimaka mana a yau kamar yadda ta taimaka wa Kiristocin a dā. Ban da haka ma, Jehobah da kansa ya yi ma kowannenmu alkawari cewa har abada ba zai taɓa barin mu ba. (Ibran. 13:​5, 6) Saboda haka, bari dukanmu mu ci gaba da jiran birnin nan wanda yake zuwa, wato, Mulkin Allah, inda za mu more albarku masu yawa har abada.—Mat. 25:34.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa muke bukatar mu ƙara dogara ga Jehobah yanzu?

  • Me ya sa muke bukatar mu yi biyayya a lokacin ƙunci mai girma?

  • Me ya sa yake da muhimmanci sosai mu ƙaunaci ꞌyanꞌuwa kuma mu taimaka musu tun yanzu?

WAƘA TA 157 Salama Za Ta Zo!

a Hakan ya faru a shekara ta 67 bayan haihuwar Yesu, ba da daɗewa ba bayan Kiristocin sun gudu daga Urushalima da Yahudiya.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba