Ta Hannun Luka
21 Yayin da Yesu yake kallon wurin da ake saka gudummawa, sai ya ga masu arziki suna zuba kuɗinsu a wurin saka gudummawar. 2 Sai ya ga wata matalauciya da mijinta ya mutu, ta zuba ƙananan tsabar kuɗi guda biyu da ba su da daraja sosai.* 3 Sai ya ce: “A gaskiya ina gaya muku, kuɗin da matalauciyar nan da mijinta ya mutu ta saka, ya fi na sauran mutanen. 4 Domin dukansu sun ba da kuɗaɗe daga cikin abubuwa masu yawa da suke da su, amma ita kuwa daga cikin talaucinta, ta ba da dukan abin da take dogara da shi.”
5 Daga baya, saꞌad da wasu suke magana game da haikalin, da yadda aka yi masa ado da duwatsu masu kyau, da abubuwan da aka keɓe wa Allah, 6 sai ya ce musu: “Waɗannan abubuwa da kuke gani, kwanaki na zuwa da ba dutse ko ɗaya da za a bari a kan wani dutse da ba za a rushe shi ba.” 7 Sai suka yi masa tambaya suna cewa: “Malam, yaushe ne abubuwan nan za su faru, da alamar da za ta nuna cewa abubuwan nan sun kusan faruwa?” 8 Sai ya ce musu: “Ku yi hankali don kada a ruɗe ku, mutane da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne shi,’* kuma, ‘Lokacin ya kusa.’ Kada ku bi su. 9 Ƙari ga haka, idan kun ji ana yaƙe-yaƙe da kuma tashin hankali, kada ku ji tsoro domin dole ne abubuwan nan su fara faruwa, amma ƙarshen ba zai zo nan da nan ba.”
10 Sai ya ce musu: “Alꞌumma za ta yaƙi alꞌumma, mulki kuma ya yaƙi mulki. 11 Za a yi munanan girgizar ƙasa, kuma za a yi ƙarancin abinci da annoba a wurare dabam-dabam. Mutane za su ga abubuwan da za su ba su tsoro kuma za su ga alamu masu ban mamaki daga sama.
12 “Amma kafin dukan abubuwan nan su faru, mutane za su kama ku kuma su tsananta muku, za su kai ku majamiꞌu da kuma kurkuku. Za a kai ku gaban sarakuna da gwamnoni saboda sunana. 13 Hakan zai ba ku damar ba da shaida. 14 Ku ƙudura a ranku cewa ba za ku shirya yadda za ku kāre kanku tun da wuri ba. 15 Zan ba ku kalmomi da kuma hikima waɗanda duk masu hamayya da ku ba za su iya ƙin su ko su yi mūsun su ba. 16 Ƙari ga haka, har iyayenku, da ꞌyanꞌuwanku, da danginku, da abokanku ma za su ba da ku* ga hukumomi, kuma za su kashe wasu daga cikinku. 17 Dukan mutane za su tsane ku saboda sunana. 18 Amma ko gashi ɗaya da ke kanku ba zai hallaka ba. 19 Ta wurin jimrewarku ne za ku ceci rayukanku.
20 “Amma idan kun ga sojoji sun kewaye Urushalima, ku san cewa an kusan hallaka ta. 21 Bari waɗanda suke Yahudiya su soma guduwa zuwa tuddai. Waɗanda suke cikinta kuma su fita, kuma waɗanda suke ƙauyuka kada su shiga cikinta. 22 Lokacin zai zama lokacin da Allah zai yi hukunci, domin a cika dukan abubuwan da aka rubuta. 23 Kaiton mata masu ciki da masu shayarwa a lokacin! Gama za a sha wahala sosai a ƙasar, kuma fushin Allah zai sauka a kan mutanen nan. 24 Za a kashe wasunsu da takobi, wasu kuma a kai su bauta a dukan alꞌummai. Alꞌummai* za su tattaka Urushalima, har sai lokacin da aka ba wa alꞌumman* ya cika.
25 “Ƙari ga haka, za a ga alamu a rana, da wata, da taurari, mutane a duniya za su ji tsoro sosai, kuma za su rasa abin da za su yi saboda yadda teku yake ruri da kuma hauka. 26 Mutane za su suma don tsoro da kuma abubuwan da suke sa rai cewa za su faru a duniya, domin abubuwan da ke sama za su girgiza. 27 Saꞌan nan za su ga Ɗan mutum yana zuwa a cikin gajimare tare da iko da ɗaukaka sosai. 28 Amma yayin da abubuwan nan suka soma faruwa, ku tashi tsaye ku ɗaga kanku sama, domin cetonku ya yi kusa.”
29 Bayan haka, sai ya ba su wani misali yana cewa: “Ku lura da itacen ɓaure da dukan sauran itatuwa. 30 Da zarar sun soma fitar da sababbin ganye, kukan gan su kuma ku gane cewa damina ta kusa. 31 Haka ku ma, idan kun ga abubuwan nan suna faruwa, ku san cewa Mulkin Allah ya yi kusa. 32 A gaskiya ina gaya muku, wannan tsarar ba za ta shuɗe ba, har sai dukan abubuwan nan sun faru. 33 Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.
34 “Ku mai da hankali don kada yawan ci, da yawan sha, da yawan damuwa su cika zuciyarku, har ranar ta zo a lokacin da ba ku yi tsammani ba, 35 kuma ta zama muku tarko. Don za ta zo a kan dukan waɗanda suke zama a duniya. 36 Ku zauna a shirye, kuna adduꞌa kullum don ku iya tsira ma dukan abubuwan nan da za su faru, ku kuma tsaya a gaban Ɗan mutum.”
37 A kowace rana yakan koyar da mutane a haikali, amma idan dare ya yi, yakan fita ya je ya kwana a tudun da ake kira Tudun Zaitun. 38 Kuma dukan mutane za su zo su same shi a cikin haikali da sassafe don su saurare shi.