Ta Hannun Luka
1 Da yake mutane da yawa sun yi ƙoƙari su sani kuma su rubuta labarin abubuwan da suka faru da gaske, waɗanda mu ma muka gaskata da su, 2 kamar yadda muka ji daga waɗanda suka shaida abubuwan nan tun daga farko, kuma suka yi shelar sa, 3 saboda haka, ya mai girma Tiyofilus, da yake na bincika abubuwan nan daidai yadda suka faru tun daga farko, na ƙuduri niyyar rubuta maka su bi da bi, 4 domin ka sani da kyau kuma ka tabbatar da gaskiyar abubuwan da aka koya maka.
5 A zamanin Hirudus* sarkin Yahudiya, akwai wani firist mai suna Zakariya da ya fito daga ƙungiyar firistoci na gidan Abijah. Sunan matarsa Alisabatu, kuma ta fito ne daga zuriyar Haruna. 6 Su biyun masu adalci ne a gaban Allah, suna bin dukan dokokin Jehobah,* da kuma umurnansa da dukan zuciyarsu. 7 Amma ba su da ɗa, domin Alisabatu ba ta haifu ba, kuma su biyun sun tsufa.
8 Yayin da Zakariya yake hidimarsa na firist a gaban Allah, yana aikin da aka ba wa ƙungiyarsa, 9 a lokacin shi ne yake da hakkin ƙona turare, sai ya shiga haikalin Jehobah* bisa ga tsarin* da aka kafa da firistoci za su bi a hidimarsu. 10 Kuma dukan mutane suna waje suna adduꞌa a lokacin da yake ƙona turare. 11 Sai malaꞌikan Jehobah* ya fito masa, yana tsaye a hannun dama na bagaden ƙona turare. 12 Da Zakariya ya ga malaꞌikan, sai ya rikice kuma tsoro ya kama shi sosai. 13 Amma malaꞌikan ya ce masa: “Kada ka ji tsoro Zakariya, domin Allah ya amsa roƙonka. Matarka Alisabatu za ta haifa maka ɗa, kuma za ka ba shi suna Yohanna. 14 Idan aka haife shi, za ka yi farin ciki da murna sosai, kuma mutane da yawa za su yi farin ciki. 15 Domin zai zama mutum mai muhimmanci a gaban Jehobah.* Amma kada ya sha ruwan inabi ko wani abin sha da ke da giya a ciki ko kaɗan. Kuma za a cika shi da ruhu mai tsarki tun kafin a haife shi.* 16 Zai maido da mutanen Israꞌila da yawa ga Jehobah* Allahnsu. 17 Ƙari ga haka, yaron zai riga Allah zuwa da ruhu da kuma ikon Iliya, don ya mayar da zukatan ubanni su zama kamar na yara. Kuma ya sa marasa biyayya su soma yin abubuwa da hikima na masu adalci, don ya shirya mutane ga Jehobah.”*
18 Sai Zakariya ya ce wa malaꞌikan: “Ta yaya zan san cewa abin da ka faɗa zai faru da gaske? Domin na tsufa, matata ma ta tsufa.” 19 Sai malaꞌikan ya amsa ya ce masa: “Ni ne Jibraꞌilu, wanda yake tsayawa kusa da Allah, an aike ni in yi magana da kai kuma in gaya maka wannan labari mai daɗi. 20 Amma, za ka yi shuru kuma ba za ka iya magana ba, har sai ranar da abubuwan nan sun faru, domin ka ƙi ka yarda da abubuwan da na gaya maka, waɗanda za su cika a lokacinsu.” 21 Mutanen kuwa, sun ci-gaba da jiran Zakariya, kuma suna tunanin dalilin da ya sa ya daɗe sosai a cikin haikalin. 22 Saꞌad da ya fito, bai iya yin magana da su ba, sai suka gane cewa ya ga wahayi a cikin haikalin. Ya ci-gaba da yi musu alamu da hannayensa domin ya kasa magana. 23 Saꞌad da kwanakin hidimarsa* suka ƙare, sai ya koma gidansa.
24 Bayan wasu kwanaki, sai matarsa Alisabatu ta yi ciki, kuma ta yi wata biyar ba ta fita daga gida ba, tana cewa: 25 “Ga abin da Jehobah* ya yi mini a wannan lokacin. Ya tuna da ni, domin ya cire mini kunya a gaban mutane.”
26 Saꞌad da cikin ya kai wata shida, sai Allah ya aiki malaꞌika Jibraꞌilu wani gari a Galili da ake kira Nazaret, 27 zuwa wurin wata budurwa wadda Yusufu da ya fito daga gidan Dauda ya yi mata alkawarin aure, kuma sunan budurwar, Maryamu ce. 28 Saꞌad da malaꞌikan ya shigo, sai ya ce mata: “Na gaishe ki, ke da kika sami alheri sosai, Jehobah* yana tare da ke.” 29 Da Maryamu ta ji gaisuwar, ta damu sosai, tana tunani ko wace irin gaisuwa ce haka. 30 Sai malaꞌikan ya ce mata: “Kada ki ji tsoro Maryamu, domin kin sami alheri a gaban Allah. 31 Ga shi za ki yi ciki, za ki haifi ɗa, kuma za ki ba shi suna, Yesu. 32 Zai zama mutum mai muhimmanci, kuma za a kira shi Ɗan Mafi Ɗaukaka, Jehobah* Allah zai ba shi kujerar mulkin babansa Dauda. 33 Zai yi mulki a kan gidan Yakubu har abada, kuma Mulkinsa ba zai taɓa ƙarewa ba.”
34 Amma Maryamu ta ce wa malaꞌikan: “Ta yaya hakan zai faru, da yake ban taɓa kwana* da namiji ba?” 35 Sai malaꞌikan ya amsa ya ce mata: “Ruhu mai tsarki zai sauko a kanki, ikon Mafi Ɗaukaka kuma zai rufe ki. Saboda haka, yaron nan da za a haifa, za a kira shi mai tsarki, Ɗan Allah. 36 Ga shi Alisabatu danginki wadda aka ce ba za ta haifu ba, tana da cikin wata shida duk da tsufarta. 37 Domin babu abin da Allah ya faɗa da ba zai iya yi ba.” 38 Sai Maryamu ta ce: “Ni baiwar Jehobah* ce! Bari ya faru da ni kamar yadda ka faɗa.” Sai malaꞌikan ya tafi ya bar ta.
39 A cikin kwanakin nan, Maryamu ta yi shiri, ta tafi da sauri zuwa wani gari da ke yankin tuddan Yahuda. 40 Sai ta shiga gidan Zakariya kuma ta gai da Alisabatu. 41 Da Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, sai jaririn da ke cikinta ya yi tsalle, kuma aka cika Alisabatu da ruhu mai tsarki. 42 Sai Alisabatu ta ɗaga murya ta ce: “Ke mai albarka ce a cikin mata, kuma jaririn da ke cikinki mai albarka ne! 43 To, ta yaya na samu wannan gata da mamar Ubangijina ta zo wurina? 44 Domin da jin gaisuwarki, sai jaririn da ke cikina ya yi tsalle don murna. 45 Mai albarka* ce kuma wadda ta ba da gaskiya, domin dukan abubuwan nan da Jehobah* ya gaya mata za su cika.”
46 Sai Maryamu ta ce: “Raina yana yabon Jehobah,* 47 kuma zuciyata tana murna sosai saboda Allah Mai Cetona, 48 domin ya tuna da ni baiwarsa ko da yake ni ba kome ba ce. Daga yanzu, dukan tsara za su ce da ni, mai farin ciki. 49 Domin Allah Mai Iko ya yi mini manyan abubuwa, kuma sunansa mai tsarki ne. 50 Daga tsara zuwa tsara, yana yin jinƙai ga waɗanda suke tsoron sa. 51 Ya yi manyan abubuwa da hannunsa, ya watsar da waɗanda suke tunani a zuciyarsu cewa sun fi wasu. 52 Ya saukar da masu iko daga kujerar mulkinsu, kuma ya ɗaukaka waɗanda ba kome ba ne. 53 Ya ba wa masu jin yunwa abubuwa masu kyau su ci su ƙoshi, kuma ya kori masu arziki hannu wofi. 54 Ya zo ya taimaki bawansa Israꞌila domin ya tuna da alkawarin da ya yi na nuna jinƙai, 55 kamar yadda ya gaya wa kakanninmu, da Ibrahim, da kuma zuriyarsa har abada.” 56 Maryamu ta zauna da Alisabatu na wajen wata uku, sai ta koma gida.
57 Sai lokaci ya yi da Alisabatu za ta haifu, kuma ta haifi ɗa. 58 Da maƙwabta da kuma danginta suka ji cewa Jehobah* ya nuna mata jinƙai sosai, sai suka taya ta murna. 59 A rana ta takwas, sai suka zo su yi wa yaron kaciya, kuma suna so su ba shi sunan babansa, Zakariya. 60 Amma mamarsa ta ce musu: “Aꞌa! sunansa Yohanna ne.” 61 Da suka ji haka, sai suka ce mata: “Babu wani danginki da ake kira da wannan sunan.” 62 Sai suka tambayi babansa sunan da yake so a ba wa yaron ta wurin yin alama da hannaye. 63 Sai ya ce a ba shi allo kuma ya rubuta cewa: “Sunansa Yohanna ne.” Da jin hakan, dukansu sun yi mamaki. 64 Nan da nan sai bakin Zakariya ya buɗu kuma ya soma magana yana yabon Allah. 65 Sai tsoro ya kama dukan maƙwabtansu, kuma mutane suka soma magana a kan dukan waɗannan abubuwan, a dukan yankin tuddan Yahudiya. 66 Kuma dukan waɗanda suka ji, sun yi tunani a zuciyarsu cewa: “Mene ne yaron nan zai zama?” Domin ba shakka hannun Jehobah* yana tare da shi.
67 Sai aka cika babansa Zakariya da ruhu mai tsarki, kuma ya yi annabci yana cewa: 68 “Bari a yabi Jehobah,* Allah na Israꞌila, domin ya mai da hankalinsa ga mutanensa, kuma ya kawo musu ceto. 69 Ya ta da mai ceto da ke da iko* dominmu, daga gidan bawansa Dauda, 70 kamar yadda ya faɗa ta bakin annabawansa na dā, 71 cewa zai cece mu daga abokan gābanmu da kuma hannun dukan maƙiyanmu. 72 Zai yi mana jinƙai kamar yadda ya yi wa kakanninmu alkawari, kuma zai tuna da yarjejeniyarsa mai tsarki 73 da ya rantse wa Ibrahim kakanmu, 74 cewa bayan ya cece mu daga hannayen abokan gābanmu, zai ba mu gatan yi masa hidima mai tsarki ba tare da jin tsoro ba, 75 tare da adalci da aminci a gabansa a dukan kwanakinmu. 76 Amma kai kuma ɗan yaro, za a ce da kai annabin Mafi Ɗaukaka, domin za ka riga Jehobah* zuwa don ka shirya hanyoyinsa, 77 kuma ka sanar wa mutanensa cewa Allah zai cece su ta wurin yafe zunubansu. 78 Domin Allahnmu mai tausayi ne. Kuma saboda wannan tausayin, za mu ga haske daga sama da zai haskaka kamar wayewar gari, 79 domin ya ba da haske ga waɗanda suke zama a cikin duhu da inuwar mutuwa kuma ya nuna mana yadda za mu bi hanyar salama.”
80 Yaron ya yi girma kuma ya yi ƙarfi da taimakon ruhu mai tsarki. Ya ci-gaba da zama a daji* har zuwa lokacin da ya fito ya nuna kansa ga mutanen Israꞌila.