Ta Hannun Luka
9 Sai Yesu ya kira almajiransa goma sha biyu kuma ya ba su iko da izini su fitar da dukan aljanu kuma su warkar da cututtuka. 2 Sai ya aike su su yi waꞌazin Mulkin Allah, kuma su yi warkarwa. 3 Ya kuma ce musu: “Kada ku ɗauki wani abu don tafiyar, ko sanda, ko jakar abinci, ko burodi, ko kuɗi, kada kuma ku ɗauki riguna biyu. 4 A duk inda kuka shiga wani gida, ku zauna a wurin har sai lokacin da za ku tashi. 5 A duk inda mutane suka ƙi karɓan ku, yayin da kuke barin garin, ku kakkaɓe ƙurar da ke ƙafafunku domin ya zama shaida a gare su.” 6 Sai almajiran suka soma bin ƙauyuka, suna shelar labari mai daɗi, da kuma warkar da marasa lafiya a koꞌina.
7 Sai Hirudus* wanda shi ne mai mulkin yankin, ya ji labarin dukan abubuwan da suke faruwa, kuma ya damu sosai domin wasu mutane suna cewa an ta da Yohanna daga mutuwa. 8 Amma wasu suna cewa Iliya ne ya bayyana, har ila wasu suna cewa, ɗaya daga cikin annabawan dā ne aka ta da. 9 Sai Hirudus ya ce: “Na yanke kan Yohanna. To wane ne wannan da nake jin abubuwan nan game da shi?” Don haka, ya yi ta ƙoƙari ya ga Yesu.
10 Saꞌad da manzannin suka dawo, sai suka gaya wa Yesu dukan abubuwan da suka yi. Sai ya kai su wani wuri su kaɗai a cikin garin da ake kira Betsaida. 11 Amma saꞌad da jamaꞌa suka ji hakan, sai suka bi shi. Ya karɓe su hannu bibbiyu kuma ya soma koya musu game da Mulkin Allah, da kuma warkar da waɗanda suke bukatar warkarwa. 12 Da rana ta kusan faɗuwa, sai almajiransa goma sha biyu suka zo suka ce masa: “Ka sallami jamaꞌar su je ƙauyuka da yankunan da suke kewaye, su nemi wurin kwana da abinci, domin wurin nan da muke babu kowa.” 13 Amma ya ce musu: “Ku ba su abin da za su ci.” Sai suka ce masa: “Ba mu da kome ban da burodi biyar da kifi biyu, sai dai ko mu da kanmu mu fita, mu je mu saya abinci don dukan mutanen nan.” 14 Mutanen sun kai wajen maza dubu biyar. Sai ya gaya ma almajiransa cewa: “Ku sa su zauna a rukunoni hamsin-hamsin.” 15 Sai almajiran suka yi hakan kuma suka sa dukan mutanen suka zauna. 16 Sai Yesu ya ɗauki burodi biyar ɗin, da kifi biyun, ya kalli sama kuma ya yi godiya a kan su. Sai ya rarraba burodin, ya soma ba wa almajiransa don su ba wa jamaꞌar. 17 Sai dukansu suka ci suka ƙoshi, da suka tattara abin da ya rage, ya cika kwanduna goma sha biyu.
18 Daga baya, saꞌad da yake adduꞌa shi kaɗai, sai almajiransa suka zo wurinsa, kuma ya tambaye su cewa: “Jamaꞌa suna cewa ni wane ne?” 19 Sai suka ce masa: “Wasu sun ce Yohanna Mai Baftisma ne, wasu kuma sun ce Iliya. Har ila, wasu sun ce an ta da ɗaya daga cikin annabawan dā ne.” 20 Sai ya ce musu: “Ku kuma fa, a ganinku, ni wane ne?” Sai Bitrus ya amsa ya ce masa: “Kai ne Kristi na Allah.” 21 Sai ya ja musu kunne sosai cewa kada su gaya ma kowa, 22 amma ya gaya musu cewa: “Ɗan mutum zai sha wahala sosai kuma dattawa, da manyan firistoci, da marubuta za su ƙi yarda da shi kuma a kashe shi, amma a rana ta uku za a ta da shi.”
23 Sai Yesu ya ce ma dukansu: “Duk wanda yake so ya bi ni, sai ya ƙi kansa, kuma ya ɗauki gungumen azabarsa* a kowace rana ya ci-gaba da bi na. 24 Domin duk wanda yake so ya ceci ransa zai rasa shi. Amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, shi ne wanda zai ceci ransa. 25 A gaskiya, mece ce ribar mutum in ya sami dukan duniyar nan amma ya rasa ransa, ko ya jawo wa kansa matsala? 26 Duk wanda ya ji kunya saboda ni da maganata, Ɗan mutum ma zai ji kunyar sa saꞌad da ya zo a cikin ɗaukakarsa da ɗaukakar Ubansa, da kuma ɗaukakar malaꞌiku masu tsarki. 27 A gaskiya ina gaya muku, akwai wasu da suke tsaye a nan da ba za su taɓa mutuwa ba har sai sun ga Mulkin Allah.”
28 Wajen kwana takwas bayan da Yesu ya faɗi abubuwan nan, sai ya ɗauki Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, suka haura tudu don su yi adduꞌa. 29 Yayin da yake adduꞌa, sai kamannin fuskarsa ya canja kuma rigarsa ta zama fari fat. 30 Ga shi! mutane biyu suna magana da shi; wato Musa da Iliya. 31 Waɗannan sun bayyana a cikin ɗaukaka, kuma suka soma magana game da yadda Yesu zai bar duniya, wanda ya kusan faruwa a Urushalima. 32 Bitrus da waɗanda suke tare da shi suna barci, amma saꞌad da suka farka, sai suka ga ɗaukakar Yesu da kuma mutane biyu da suke tsaye da shi. 33 Yayin da mutanen suke tafiya, sai Bitrus ya ce wa Yesu: “Malam, yana da kyau da muka zo nan. Bari mu kafa tentuna* uku a nan, ɗaya domin ka, ɗaya na Musa, ɗaya kuma na Iliya.” Bai ma san abin da yake faɗa ba. 34 Amma yayin da yake faɗin abubuwan nan, sai gajimare ya haɗu kuma ya rufe su. Saꞌad da suka shiga cikin gajimaren, tsoro ya kama su. 35 Sai wata murya daga cikin gajimaren ta ce: “Wannan shi ne Ɗana, wanda na zaɓa. Ku saurare shi.” 36 Yayin da muryar take kan magana, sai suka ga Yesu shi kaɗai. Amma sai suka yi shuru, kuma a cikin kwanakin ba su gaya ma wani abubuwan da suka gani ba.
37 Washegari saꞌad da suka sauko daga tudun, sai jamaꞌa suka same shi. 38 Sai wani mutum daga cikin jamaꞌar ya ta da murya ya ce: “Malam, ina roƙon ka ka taimaka wa ɗana. Domin shi kaɗai ne nake da shi. 39 Aljani yakan shiga jikinsa, ya sa shi ya yi ihu, ya jefa shi ƙasa yana farfaɗiya da fitar da kumfa a baki. Da kyar ne yake barin sa bayan ya ji masa rauni. 40 Na roƙi almajiranka su fitar da aljanin, amma sun kasa.” 41 Sai Yesu ya amsa ya ce: “Ku mutanen zamanin nan marasa bangaskiya, masu mugunta, har yaushe zan ci-gaba da kasancewa tare da ku, da kuma yin haƙuri da ku? Ka kawo ɗanka nan.” 42 Amma yayin da yaron yake zuwa wurin Yesu, sai aljanin ya jefa shi ƙasa, ya sa shi ya soma farfaɗiya. Amma Yesu ya tsawata wa ruhu mai ƙazantan, ya warkar da yaron kuma ya miƙa yaron ga babansa. 43 Sai dukansu suka yi mamaki don sun ga ikon Allah.
Yayin da dukansu suke kan mamakin abubuwan da yake yi, sai Yesu ya ce wa almajiransa: 44 “Ku saurara da kyau kuma ku tuna da kalmomin nan, za a ci amanar Ɗan mutum kuma a ba da shi ga mutane.” 45 Amma ba su gane abin da yake cewa ba. An ɓoye musu maꞌanar don kada su fahimta, kuma suna tsoron yi masa tambaya game da abin da ya faɗa.
46 Sai almajiransa suka soma gardama a tsakaninsu a kan wanda ya fi girma. 47 Da Yesu ya gane abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, kuma ya sa yaron ya tsaya kusa da shi, 48 Sai ya ce musu: “Duk wanda ya marabci ƙaramin yaron nan saboda sunana ya marabce ni; kuma duk wanda ya marabce ni ya marabci wanda ya aiko ni ma. Domin wanda yake ɗaukan kansa a matsayin wanda ya fi ƙanƙanta a tsakanin dukanku, shi ne ya fi girma.”
49 Sai Yohanna ya ce: “Malam, mun ga wani yana fitar da aljanu da sunanka, kuma mun yi ƙoƙari mu hana shi domin ba ya bin mu.” 50 Amma Yesu ya ce masa: “Kada ku yi ƙoƙarin hana shi, domin duk wanda ba ya gāba da ku, yana tare da ku.”
51 Saꞌad da lokaci ya yi kusa da Yesu zai koma sama, ya ƙuduri niyyar zuwa Urushalima. 52 Sai ya aiki almajiransa su je wani ƙauyen Samariyawa don su yi masa shirye-shirye a wurin kafin ya zo. 53 Amma mutanen ba su marabce shi ba, domin ya ƙuduri niyyar zuwa Urushalima. 54 Saꞌad da Yaƙub da Yohanna suka ga haka, sai suka ce: “Ubangiji, kana so mu kira wuta daga sama ya sauko ya hallaka su?” 55 Amma sai ya juya ya tsawata musu. 56 Sai suka tafi wani ƙauye dabam.
57 Yayin da suke tafiya a kan hanya, sai wani ya ce masa: “Zan bi ka duk inda za ka je.” 58 Amma Yesu ya ce masa: “Karnukan daji suna da ramukansu, tsuntsaye kuma suna da wurin kwana, amma Ɗan mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.” 59 Sai ya ce ma wani: “Ka zama mabiyina.” Sai mutumin ya ce: “Ubangiji, bari in je in binne babana tukuna.” 60 Amma Yesu ya ce masa: “Ka bar matattu su binne matattunsu, amma kai, ka tafi ka je ka yi shelar Mulkin Allah a koꞌina.” 61 Har ila, wani ya ce masa: “Ubangiji, zan bi ka, amma bari in je in yi ban kwana da mutanen gidanmu tukuna.” 62 Sai Yesu ya ce masa: “Duk wanda ya fara noma da garma yana kuma duba abubuwan da ke baya, bai dace da Mulkin Allah ba.”