Zuwa ga Romawa
1 Bulus, bawan Kristi Yesu, wanda aka kira ya zama manzo, kuma aka zaɓa* don ya yi waꞌazin labari mai daɗi na Allah. 2 Labari mai daɗi da Allah ya yi alkawarin sa tun dā, ta wurin annabawansa a cikin Nassosi masu tsarki, 3 labari mai daɗin kuwa game da Ɗansa ne, wanda aka haifa a duniya a zuriyar Dauda. 4 Amma ta wurin ikon ruhu mai tsarki, an sanar cewa shi Ɗan Allah ne saꞌad da aka ta da shi daga mutuwa—hakika, shi ne Yesu Kristi Ubangijinmu. 5 Ta wurinsa ne na sami alheri kuma na zama manzo, domin dukan alꞌummai su yi biyayya ta wurin bangaskiya kuma su girmama sunansa. 6 Daga cikin waɗannan alꞌummai ne aka kira ku ku zama na Yesu Kristi. 7 Wannan wasiƙa ce ga dukan waɗanda Allah yake ƙauna da ke Roma, waɗanda aka kira su su zama tsarkaka:
Bari alheri da kuma salama daga wurin Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kristi su kasance tare da ku.
8 Da farko dai, ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Kristi saboda dukan ku, domin ana magana game da bangaskiyarku a dukan duniya. 9 Gama Allah, wanda nake yi masa hidima mai tsarki da dukan zuciyata* ta wajen yin shelar labari mai daɗi game da Ɗansa, shi ne shaidata cewa ban fasa ambata ku a cikin adduꞌoꞌina ba, 10 ina roƙon Allah cewa idan zai yiwu kuma idan ya yi daidai da nufinsa, in sami damar zuwa wurinku a ƙarshe. 11 Ina marmarin ganin ku, don in ba ku wata kyauta daga wurin Allah domin ku iya tsayawa daram; 12 ko kuma, mu ƙarfafa juna da bangaskiyarmu, wato in ƙarfafa ku da bangaskiyata, kuma ku ƙarfafa ni da bangaskiyarku.
13 Amma ꞌyanꞌuwa, ina so ku san cewa sau da yawa na so in zo wurinku domin waꞌazina ya kawo sakamako mai kyau a tsakaninku, kamar yadda ya faru a wasu ƙasashe, amma har yanzu ba a bar ni in yi hakan ba. 14 Mutanen Girka da baƙi, masu hikima da marasa hikima, duk suna bi na bashi; 15 don haka, ku ma da ke Roma ina marmarin yi muku shelar labari mai daɗi. 16 Ba na jin kunyar yin shelar labari mai daɗi; a gaskiya, labari mai daɗi ne ikon da Allah yake amfani da shi ya ceci dukan masu bangaskiya, da farko Yahudawa, saꞌan nan mutanen Girka. 17 Ta wurin labari mai daɗin ne ake bayyana adalcin Allah ga waɗanda suka ba da gaskiya gare shi, kuma hakan na ƙarfafa bangaskiyarsu, kamar yadda yake a rubuce cewa: “Amma mai adalci zai rayu saboda bangaskiyarsa.”
18 Daga sama Allah yana nuna fushinsa a kan waɗanda suke yin abin da ba ya so, da kuma rashin adalcin mutanen da suke danne gaskiya a hanyar da ba ta dace ba, 19 domin abin da za a iya sani game da Allah a bayyane yake sosai a tsakaninsu, gama Allah ya bayyana musu shi. 20 Tun daga halittar duniya, ana iya sanin halayensa da ba a gani, domin ana iya gane halayen ta wurin abubuwan da ya yi, abubuwan suna ma nuna ikonsa marar iyaka, kuma suna nuna cewa shi ne Allah, har babu wanda zai ba da hujja cewa bai sani ba. 21 Ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, amma tunaninsu marar amfani ne, kuma zukatansu marasa wayo ta yi duhu. 22 Ko da yake suna cewa su masu hikima ne, sun zama wawaye, 23 kuma suka juya ɗaukakar Allah da ba ya mutuwa zuwa wani abu da ke kama da siffar mutum da ke mutuwa, da tsuntsaye, da dabbobi masu ƙafa huɗu, da kuma masu rarrafe.
24 Saboda haka, Allah ya bar su su bi shaꞌawoyin zuciyarsu ta wurin barin su su yi abubuwa masu ƙazanta har suka kunyatar da jikinsu. 25 Sun zaɓi su yarda da ƙarya maimakon su yarda da gaskiyar Allah, kuma sun yi sujada da hidima mai tsarki ga halittu maimakon ga Mahalicci, wanda ya kamata a yaba masa har abada. Amin. 26 Shi ya sa Allah ya bar su su kasance da shaꞌawoyin jimaꞌi masu ban kunya, don matansu sun daina kwana da maza yadda ya kamata, kuma sun soma kwana da mata. 27 Haka ma, mazansu sun daina kwana da mata yadda ya kamata, kuma suka soma yin shaꞌawa mai tsanani a kan juna, maza da maza suna aikata abin ƙazanta kuma suna samun cikakken hukunci da ya yi daidai da ayyukansu.
28 Da yake sun ƙi su ɗauki sanin Allah da muhimmanci, Allah ya bar su su ci-gaba da yin tunanin banza da wofi, da yin abubuwan da bai kamata a yi ba. 29 Kuma a cike suke da dukan rashin adalci, da mugunta, da haɗama,* da yin abubuwa marasa kyau, cike da kishi, da kisa, da faɗa, da yaudara, da riƙe mutum a zuciya, masu gulma, 30 masu ɓata suna, masu ƙin Allah, masu rena mutane, masu ɗaga kai, masu taƙama, masu ƙulla mugunta, marasa biyayya ga iyaye, 31 marasa ganewa, marasa cika alkawari, marasa ƙaunar wasu,* da kuma masu taurin zuciya. 32 Ko da yake sun san hukuncin adalci na Allah, wato waɗanda suke yin abubuwan nan sun cancanci mutuwa, duk da haka, ba ci-gaba da aikata waɗannan abubuwan kawai suke yi ba, amma har suna goyon bayan waɗanda suke yin su.