Zuwa ga Romawa
14 Ku marabci mutumin da bangaskiyarsa ba ta da ƙarfi, amma kada ku shariꞌanta shi idan raꞌayinsa ya yi dabam da naku. 2 Bangaskiyar wani mutum za ta bar shi ya ci duk abin da ya ga dama, amma wani da bangaskiyarsa ba ta da ƙarfi, kayan lambu ne kawai yake ci. 3 Bari wanda yake ci kada ya rena wanda ba ya ci, kuma wanda ba ya ci, kada ya shariꞌanta wanda yake ci, domin Allah ya marabce shi. 4 Wane ne kai da za ka shariꞌanta bawan wani? Maigidansa ne zai iya yanke shawara cewa abin da ya yi daidai ne ko ba daidai ba. Hakika, da yake Jehobah* yana taimaka masa, zai iya amincewa da shi.
5 Wani mutum yakan ɗauki rana ɗaya da muhimmanci fiye da sauran ranaku; wani mutum kuma yana ganin dukan ranaku iri ɗaya ne; bari dai kowa ya kasance da tabbaci sosai a zuciyarsa. 6 Wanda yake ɗaukan rana ɗaya da muhimmanci yana yin hakan ne ga Jehobah.* Kuma wanda yake ci, yana ci ne ga Jehobah,* domin yakan miƙa godiya ga Allah; kuma wanda ba ya ci, ba ya ci ne ga Jehobah,* duk da haka yakan miƙa godiya ga Allah. 7 Hakika, babu wani a cikinmu da ke rayuwa don kansa kaɗai kuma ba wanda yake mutuwa don kansa kaɗai. 8 Domin idan muna a raye, muna raye ne don Jehobah,* kuma idan muka mutu, mun mutu ne domin Jehobah.* Saboda haka, ko da muna raye ko mun mutu, mu na Jehobah* ne. 9 Wannan dalili ne ya sa Kristi ya mutu kuma ya sake rayuwa, domin ya zama Ubangiji ga matattu da masu rai.
10 To me ya sa kake shariꞌanta ɗanꞌuwanka? Ko kuma me ya sa kake rena ɗanꞌuwanka? Gama dukanmu za mu tsaya a gaban kujerar shariꞌa na Allah wanda zai yi mana shariꞌa. 11 Domin a rubuce yake cewa: “‘Muddin ina raye,’ in ji Jehobah,* ‘kowace gwiwa za ta durƙusa mini kuma kowane harshe zai ba da shaida cewa ni ne Allah.’” 12 Don haka, kowannenmu zai ba da lissafin abin da ya yi ga Allah.
13 Saboda haka, kada mu sake shariꞌanta juna, a maimakon haka, ku ƙuduri niyyar cewa ba za ku yi abin da zai raunana bangaskiyar ɗanꞌuwanku ko ya sa shi tuntuɓe ba. 14 A matsayina na mabiyin Ubangiji Yesu, na sani kuma ina da tabbaci cewa babu abin da yake da ƙazanta da kansa; sai dai idan wani yana ganin wani abu yana da ƙazanta, a gare shi ne abin yake da ƙazanta. 15 Idan kana ɓata wa ɗanꞌuwanka rai saboda abinci, ka daina nuna ƙauna ke nan. Kada abincinka ya jawo hallaka ga wanda Kristi ya mutu domin sa. 16 Don haka, kada ka sa mutane su ɗauki abu mai kyau da kake yi, a matsayin abu marar kyau. 17 Domin Mulkin Allah ba ya nufin ci da sha, amma yana nufin adalci da salama da farin ciki, cikin ruhu mai tsarki. 18 Duk wanda yake yi wa Kristi hidima a matsayin bawa a wannan hanyar zai faranta wa Allah rai, kuma mutane za su yarda da shi.
19 Saboda haka, mu yi ƙoƙari mu yi abubuwan da za su kawo salama da abubuwan da za su ƙarfafa* juna. 20 Ku daina rusa ayyukan Allah saboda abinci. A gaskiya, dukan abubuwa suna da tsabta, amma ba daidai ba ne mutum ya ci idan hakan zai sa wani tuntuɓe. 21 Zai fi kyau kada ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko kuma ka yi wani abu idan yin hakan zai sa ɗanꞌuwanka tuntuɓe. 22 Bari bangaskiyarka ta kasance tsakaninka da Allah. Mai farin ciki ne wanda zuciyarsa ba ta ɗaura masa laifi a kan abin da shi da kansa ya amince da shi. 23 Amma idan yana da shakka, ya riga ya kama kansa da laifi idan ya ci, domin bai ci bisa bangaskiya ba. Hakika, duk wani abin da ba bisa bangaskiya yake ba, zunubi ne.