Zuwa ga Romawa
6 Me za mu ce ke nan? Za mu ci-gaba da yin zunubi ne don Allah ya ƙara nuna mana alheri? 2 Aꞌa! Da yake mun sami ꞌyanci daga zunubi,* yaya kuma za mu ci-gaba da yin rayuwa cikin zunubi? 3 Ko dai ba ku sani cewa dukanmu da aka yi mana baftisma cikin Kristi Yesu, cikin mutuwarsa ne aka yi mana baftisma ba? 4 Saboda haka, an binne mu tare da shi ta wurin baftismarmu cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka ta da Kristi daga mutuwa ta wurin ɗaukakar Uba, mu ma ya kamata mu yi sabuwar rayuwa. 5 Da yake mun zama ɗaya da shi cikin irin mutuwarsa, babu shakka za mu kuma zama ɗaya da shi ta yadda aka ta da shi daga mutuwa. 6 Gama mun san cewa an rataye halinmu na dā a kan gungume tare da shi, domin kada jikinmu da ke da zunubi ya yi iko a kanmu, ta haka ne muka daina zama bayi ga zunubi. 7 Gama wanda ya mutu an riga an ꞌyantar da shi daga zunubinsa.*
8 Ƙari ga haka, idan mun riga mun mutu tare da Kristi, mun ba da gaskiya cewa za mu kuma rayu tare da shi. 9 Gama mun san cewa, da yake an ta da Kristi daga mutuwa, ba zai sake mutuwa ba; a yanzu mutuwa ba ta da iko a kansa. 10 Gama mutuwar da ya yi sau ɗaya tak, ta faru ne don ya share zunubai, amma rayuwar da yake yi yanzu, yana yi ne don Allah. 11 Haka ku ma, ku yi kamar ku matattu ne idan ya zo ga yin zunubi amma masu rai don Allah ta wurin Kristi Yesu.
12 Saboda haka, kada ku bar zunubi ya ci-gaba da yin iko a jikin nan naku mai mutuwa, don kada ku yi biyayya ga shaꞌawoyinsa. 13 Kuma kada ku ci-gaba da miƙa jikinku* ga zunubi a matsayin makamai na rashin adalci, amma ku miƙa kanku ga Allah a matsayin waɗanda aka ta da su daga mutuwa, kuma ku miƙa jikinku* ga Allah a matsayin makamai na adalci. 14 Kada zunubi ya yi iko a kanku, da yake ba kwa ƙarƙashin doka amma kuna ƙarƙashin alheri.
15 To me kuma za mu ce? Za mu yi zunubi domin ba ma ƙarƙashin doka amma muna ƙarƙashin alheri ne? Aꞌa, ba za mu yi haka ba! 16 Ba ku san cewa idan kuka miƙa kanku ga kowane mutum a matsayin bayi masu biyayya, ku bayi ne ga wanda kuke yi masa biyayya ba? Ko dai bayi ga zunubi wanda ke kai ga mutuwa, ko kuma bayi ga biyayya wanda ke kai ga adalci. 17 Amma godiya ga Allah domin ko da yake a dā ku bayi ne ga zunubi, kun yi biyayya da dukan zuciyarku ga irin koyarwa da aka danƙa muku. 18 Hakika, tun da yake kun sami ꞌyanci daga zunubi, kun zama bayi ga adalci. 19 Ina magana kamar yadda ɗanꞌadam yake yi domin kasawar jikinku; kamar yadda kuka miƙa gaɓoɓin jikinku a matsayin bayi ga ƙazanta, da mugunta da ke kai ga yin mugunta, a yanzu sai ku miƙa gaɓoɓin jikinku a matsayin bayi ga adalci, wanda yake kai ga yin abubuwa masu tsarki. 20 A lokacin da kuke bayin zunubi, kuna da ꞌyanci daga adalci.
21 Wane amfani kuka samu daga abubuwan da kuka yi a dā? Abubuwan da yanzu suka zama muku abin kunya. Gama ƙarshen waɗannan abubuwa mutuwa ne. 22 Amma yanzu da kuka sami ꞌyanci daga zunubi kuma kuka zama bayin Allah, kuna ba da amfani a hanya mai tsarki, kuma a ƙarshe za ku samu rai na har abada. 23 Gama ladan da zunubi yake biya shi ne mutuwa, amma kyautar da Allah yake bayarwa ita ce rai na har abada ta wurin Kristi Yesu Ubangijinmu.