Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb25 Yuli pp. 8-9
  • 28 ga Yuli–3 ga Agusta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 28 ga Yuli–3 ga Agusta
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2025
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2025
mwb25 Yuli pp. 8-9

28 GA YULI–3 GA AGUSTA

KARIN MAGANA 24

Waƙa ta 38 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Ka Shirya Kanka don Ka Iya Magance Matsaloli a Nan Gaba

(minti 10)

Ku ci gaba da samun ƙarin ilimi da hikima (K. Ma 24:5; it-2-E 610 sakin layi na 8)

Saꞌad da kake sanyin gwiwa, ka tabbata kana adduꞌa da karanta Littafi Mai Tsarki da kuma halartan taro a kowane lokaci (K. Ma 24:10; w09 12/15 18 sakin layi na 12-13)

Idan muna da bangaskiya sosai kuma muna ƙaunar Jehobah, hakan zai sa mu shawo kan matsaloli (K. Ma 24:16; w20.12 15)

Wata ꞌyarꞌuwa da take ciwo mai tsanani tana waꞌazi da kawarta tana farin ciki. Tana nuna wa mata wani abu a wayarta.

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • K. Ma 24:27—Me muka koya daga wannan karin maganar? (w09 10/15 12)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) K. Ma 24:​1-20 (th darasi na 11)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 2) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Kun gama hira, da kake so ka soma yi masa waꞌazi, sai wani abu ya sa mutumin ya tafi. (lmd darasi na 2 batu na 4)

5. Fara Magana da Mutane

(minti 3) WAꞌAZI GIDA-GIDA. (lmd darasi na 3 batu na 4)

6. Fara Magana da Mutane

(minti 3) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. Ka gaya wa mutumin yadda muke nazari da mutane, sai ka ba mutumin katin nazarin Littafi Mai Tsarki. (lmd darasi na 4 batu na 3)

7. Jawabi

(minti 3) lmd ƙarin bayani na 1 batu na 11—Jigo: Allah Yana Magana da Mu. (th darasi na 6)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 99

8. Ku Taimaka wa Juna a Lokacin Wahala

(minti 15) Tattaunawa.

Annoba da balaꞌi da taꞌaddanci da yaƙi da kuma tsanantawa za su iya faruwa ba zato ba tsammani. Idan hakan ya faru, ꞌyanꞌuwa sukan haɗa kai su taimaka da kuma ƙarfafa juna. Ko da abubuwan nan ba su faru da mu ba, muna baƙin ciki idan hakan ya faru da ꞌyanꞌuwanmu, kuma muna iya ƙoƙarinmu don mu taimaka musu.—1Ko 12:​25, 26.

Hotuna: ꞌYanꞌuwa maza da mata suna taimaka wa ꞌyanꞌuwansu a hanyoyi dabam dabam. 1. ꞌYanꞌuwa maza da mata suna taimaka wajen gyara Majamiꞌar Mulki da balaꞌi ya lalatar. 2. ꞌYanꞌuwa maza da mata suna marabtar wata mai gudun hijira da ꞌyarta. 3. Wata ꞌyarꞌuwa tana saka kudi da akwatin gudumawa a Majamiꞌar Mulki. 4. ꞌYanꞌuwa maza da mata suna rarraba wa ꞌyan gudun hijra abinci a Majamiꞌar Mulki. 5. Masu ba da kai suna rarraba ruwa. 6. Wani danꞌuwa yana adduꞌa.

Karanta 1 Sarakuna 13:6 da Yakub 5:16b. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Me ya sa yin adduꞌa a madadin ꞌyanꞌuwa yana taimakawa?

Karanta Markus 12:​42-44 da 2 Korintiyawa 8:​1-4. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Ko da ba mu da abu da yawa da za mu ba ꞌyanꞌuwa da suke da bukata, me ya sa ya kamata mu bayar ko da kaɗan ne?

Ku kalli BIDIYON An Ƙarfafa ’Yan’uwa Lokacin da Aka Hana Aikinmu. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Waɗanne sadaukarwa ne ꞌyanꞌuwanmu suka yi don su taimaka wa ꞌyanꞌuwa da suke zama a wuraren da aka hana aikinmu a Gabashin Turai?

  • A lokacin da aka hana aikinmu, ta yaya ꞌyanꞌuwa suka bi umurni game da yin taro da kuma ƙarfafa juna?—Ibr 10:​24, 25

9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

(minti 30) lfb darasi na 4-5

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 112 da Adduꞌa

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba