Talata, 29 ga Yuli
Ina jin daɗinka ƙwarai.—Luk. 3:22.
Sanin cewa Jehobah ya amince da bayinsa yana da ban ƙarfafa! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yahweh yakan ji daɗin mutanensa.” (Zab. 149:4) Amma a wasu lokuta, Kirista zai iya yin sanyin gwiwa kuma ya soma shakkar ko Jehobah ya amince da shi. Akwai bayin Allah masu aminci da yawa a Littafi Mai Tsarki da su ma sun yi fama da irin wannan tunani. (1 Sam. 1:6-10; Ayu. 29:2, 4; Zab. 51:11) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ꞌyan Adam ajizai za su iya samun amincewar Allah. Ta yaya? Ta wurin ba da gaskiya ga Yesu Kristi da kuma yin baftisma. (Yoh. 3:16) Ta yin hakan, za mu nuna wa mutane cewa mun tuba daga zunubanmu kuma mun yi alkawarin yin nufin Jehobah. (A. M. 2:38; 3:19) Jehobah zai yi farin ciki sosai idan muka ɗau matakan nan don mu zama abokansa. Idan muka ci-gaba da cika alkawarin da muka yi cewa za mu yi nufin Jehobah, Jehobah zai amince da mu kuma zai ɗauke mu a matsayin abokansa.—Zab. 25:14. w24.03 26 sakin layi na 1-2
Laraba, 30 ga Yuli
Ba za mu iya yin shiru a kan abin da muka ji, muka kuma gani ba.—A. M. 4:20.
Za mu iya yin koyi da almajiran Yesu ta wajen ci-gaba da yin waꞌazi ko da hukuma ta ce mu daina yin hakan. Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana mu iya yin aikin da ya ba mu. Don haka mu roƙi Jehobah ya ba mu ƙarfin zuciya da hikima, kuma ya taimake mu mu iya jimre matsalolinmu. Yawancinmu muna fama da matsaloli dabam-dabam. Ko rashin lafiya, ko rasuwar wani da muke ƙauna, ko wata matsala a iyalinmu, ko tsanantawa da dai sauran su. Annoba da tashe-tashen hankula sun sa jimre wa matsalolin nan ya ƙara yin wuya. Idan kana cikin matsala, ka faɗa wa Jehobah duk abin da ke zuciyarka. Ka bayyana masa abin da ke faruwa da kai kamar yadda za ka gaya wa amininka. Tabbas, Jehobah zai taimake ka, “zai lura da kai.” (Zab. 37:3, 5) Idan muka nace da yin adduꞌa, zai taimaka mana mu “yi haƙuri a cikin azaba.” (Rom. 12:12) Jehobah ya san matsalolin da bayinsa suke fuskanta. “Yakan kuma ji kukansu ya cece su.”—Zab. 145:18, 19. w23.05 5-6 sakin layi na 12-15
Alhamis, 31 ga Yuli
Ku tabbata cewa kun koyi abin da zai gamshi Ubangiji.—Afis. 5:10.
Idan muna so mu tsai da shawara mai muhimmanci, muna bukatar mu fahimci mene ne “nufin Ubangiji,” kuma mu bi shi. (Afis. 5:17) Idan muna neman ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da suka dace da yanayin da muke ciki, muna neman sanin raꞌayin Jehobah game da batun ke nan. Kuma idan muka gano ƙaꞌidodin Jehobah kuma muka bi su, za mu iya yin zaɓi mai kyau. “Mugun nan,” wato maƙiyinmu Shaiɗan, zai so ya cika mu da ayyuka da yawa har ma mu rasa lokacin bauta ma Jehobah. (1 Yoh. 5:19) Kirista zai iya sa neman abin duniya, ko makaranta, ko kuma aikin da yake yi, ya zama farko a rayuwarsa, maimakon ya nemi hanyoyin da zai bauta ma Jehobah. Idan ya yi hakan, ya nuna cewa ya soma bin tunanin mutanen duniyar nan ke nan. Hakika, biɗan abubuwan nan ba laifi ba ne. Amma bai kamata a ce su ne muka sa a kan-gaba ba. w24.03 24 sakin layi na 16-17