Zuwa ga Romawa
12 Don haka, ꞌyanꞌuwana, ina roƙon ku saboda yawan tausayin Allah, ku miƙa jikinku a matsayin hadaya mai rai, mai tsarki, kuma wadda Allah zai karɓa, ta haka za ku yi wa Allah hidima mai tsarki da dukan tunaninku. 2 Kuma ku daina barin zamanin nan* yana mulmula tunaninku, amma ku sabunta kanku ta wajen canja yadda kuke tunani, don ku iya sanin nufi mai kyau na Allah, wanda yake daidai* da kuma wanda ya amince da shi.
3 Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini, ina gaya wa kowannenku kada ya riƙa ɗaukan kansa da muhimmanci fiye da yadda ya kamata ya yi, amma bari kowannenku ya nuna cewa yana tunani mai kyau, daidai da bangaskiyar da Allah ya ba kowannenku. 4 Kamar yadda ake da gaɓoɓi da yawa a jiki ɗaya, kuma gaɓoɓin suna aiki dabam-dabam, 5 haka ma, ko da yake muna da yawa, mu jiki ɗaya ne cikin Kristi, amma kowannenmu gaɓa ne da ke dogara da sauran gaɓoɓin jikin. 6 Tun da yake muna da kyauta dabam-dabam bisa ga alherin da aka nuna mana, idan kyautar yin annabci ne, bari mu yi shi daidai da bangaskiyarmu; 7 ko idan kyautar yin hidima ce, bari mu yi hidimar; ko wanda yake koyarwa ne, bari ya yi koyarwar; 8 ko mutumin mai ba da ƙarfafa* ne, bari ya ba da ƙarfafa;* idan mutumin mai rarrabawa* ne, bari ya yi hakan hannu sake; idan mutumin mai ja-goranci ne, bari ya yi hakan da ƙwazo; idan mutumin mai yin jinƙai ne, bari ya yi hakan da farin ciki.
9 Kada ƙaunarku ta zama na munafunci. Ku tsani mugunta; amma ku manne wa abu mai kyau. 10 Ku riƙa ƙaunar juna sosai kamar ꞌyanꞌuwa. Ku zama a kan gaba wajen girmama juna. 11 Ku zama masu ƙwazo ba masu ƙiwuya ba. Bari ruhu mai tsarki ya sa ku himma. Ku yi hidima kamar bayi ga Jehobah.* 12 Ku yi farin ciki don begenku. Ku jimre shan wahala. Ku yi ta adduꞌa babu fasawa. 13 Ku raba abin da kuke da shi da tsarkaka daidai da bukatunsu. Ku riƙa karɓan baƙi hannu bibbiyu. 14 Ku ci-gaba da yi wa waɗanda suke tsananta muku albarka; ku albarkace su, kada ku laꞌanta su. 15 Ku yi murna da waɗanda suke murna; ku yi kuka da waɗanda suke kuka. 16 Ku riƙa ɗaukan mutane yadda kuke ɗaukan kanku; kada ku riƙa sa zuciya a kan manya-manyan abubuwa, amma ku riƙa sa zuciya a kan ƙananan abubuwa. Kada ku ɗauka cewa kun fi wasu hikima.
17 Kada ku rama mugunta da mugunta. Ku lura don ku aikata abin da kowa zai iya gani cewa daidai ne. 18 Ku yi iya ƙoƙarinku in zai yiwu, ku yi abin da zai sa ku yi zaman salama da kowa. 19 ꞌYanꞌuwana, kada ku yi ramuwa, amma ku bar wa Allah ya nuna fushinsa; gama a rubuce yake cewa: “‘Ramuwa tawa ce; Ni kuwa zan rama,’ in ji Jehobah.”* 20 Amma “idan abokin gābanka yana jin yunwa, ka ciyar da shi; idan yana jin ƙishin ruwa, ka ba shi abin sha; ta yin hakan, za ka zuba garwashin wuta a kansa.”* 21 Kada ku bar mugunta ta yi nasara a kanku, amma ku ci-gaba da yin nasara a kan mugunta ta wurin yin nagarta.*