Ta Hannun Yohanna
8 12 Sai Yesu ya sake gaya musu cewa: “Ni ne hasken duniya. Duk wanda ya bi ni ba zai taɓa yin tafiya a cikin duhu ba, amma zai sami haske mai ba da rai.” 13 Sai Farisiyawan suka ce masa: “Kana ba da shaida game da kanka, don haka, shaidarka ba gaskiya ba ce.” 14 Sai Yesu ya amsa musu ya ce: “Ko da na ba da shaida game da kaina, shaidar da na bayar gaskiya ce, domin na san inda na fito da kuma inda zan je. Amma ba ku san inda na fito da kuma inda zan je ba. 15 Kuna yin shariꞌa yadda mutane suke yi, ni kuwa ba na yi wa kowa shariꞌa. 16 Kuma ko da na yi shariꞌa, shariꞌata gaskiya ce, domin ba ni kaɗai ba ne, amma Uba wanda ya aiko ni yana tare da ni. 17 Ƙari ga haka, a cikin Dokarku* an rubuta cewa: ‘Shaidar da mutane biyu suka bayar gaskiya ce.’ 18 Ina ba da shaida game da kaina, kuma Uba wanda ya aiko ni ma yana ba da shaida game da ni.” 19 Sai suka ce masa: “A ina ne Ubanka yake?” Yesu ya amsa musu ya ce: “Ba ku san ni ba kuma ba ku san Ubana ba. Da kun san ni, da za ku san Ubana ma.” 20 Yesu ya faɗi abubuwan nan ne a kusa da wurin da ake saka gudummawa yayin da yake koyarwa a cikin haikali. Amma babu wanda ya kama shi domin lokacinsa bai yi ba tukuna.
21 Sai ya sake ce musu: “Zan tafi kuma za ku neme ni, kuma duk da haka za ku mutu a cikin zunubanku. Wurin da za ni, ba za ku iya zuwa ba.” 22 Sai Yahudawan suka soma cewa: “Ko yana so ya kashe kansa ne? Domin ya ce, ‘Wurin da za ni, ba za ku iya zuwa ba.’” 23 Sai ya ci-gaba da ce musu: “Ku daga ƙasa kuke; ni kuwa na fito daga sama ne. Ku na duniyar nan ne; ni kuwa ba na duniyar nan ba ne. 24 Shi ya sa na gaya muku cewa: Za ku mutu a cikin zunubanku. Domin idan ba ku ba da gaskiya cewa ni ne shi ba, za ku mutu a cikin zunubanku.” 25 Sai suka soma gaya masa cewa: “Kai waye ne?” Yesu ya amsa musu ya ce: “Me ya sa ma nake magana da ku? 26 Ina da abubuwa da yawa da zan faɗa game da ku kuma in yanke muku hukunci a kai. Hakika, Wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, kuma abubuwan da na ji daga wurinsa ne nake faɗa a duniya.” 27 Ba su gane cewa Yesu yana yi musu magana game da Uban ba ne. 28 Sai Yesu ya ce musu: “Da zarar kun rataye Ɗan mutum a kan gungume, a lokacin ne za ku gane cewa ni ne shi kuma ba na yin kome yadda na ga dama; amma abubuwan da Uba ya koyar da ni, su ne nake faɗa. 29 Kuma wanda ya aiko ni yana tare da ni; bai yashe ni ba, domin a kullum ina yin abin da ke faranta masa rai.” 30 Yayin da yake faɗin abubuwan nan, mutane da yawa sun ba da gaskiya gare shi.
31 Sai Yesu ya gaya wa Yahudawan da suka ba da gaskiya gare shi cewa: “Idan kun ci-gaba da bin abubuwan da na faɗa, ku almajiraina ne na gaske, 32 za ku san gaskiya, kuma gaskiyar za ta ꞌyantar da ku.” 33 Sai suka amsa masa suka ce: “Mu zuriyar Ibrahim ne kuma ba mu taɓa zama bayin kowa ba. To me ya sa ka ce, ‘Za ku sami ꞌyanci’?” 34 Sai Yesu ya amsa ya ce musu: “A gaskiya ina gaya muku, duk mai yin zunubi bawan zunubi ne. 35 Ƙari ga haka, bawa ba ya ci-gaba da zama a gidan maigidansa har abada; amma ɗa yana ci-gaba da zama a gidan har abada. 36 Don haka, idan ɗan ya ꞌyantar da ku, za ku samu ꞌyanci na gaske. 37 Na san cewa ku zuriyar Ibrahim ne. Amma kuna neman ku kashe ni, domin ba ku amince da abin da nake faɗa ba. 38 Ina faɗin abubuwan da na gani saꞌad da nake tare da Ubana, amma ku kuna yin abubuwan da kuka ji daga ubanku.” 39 Sai suka amsa suka ce masa: “Ibrahim ne ubanmu.” Yesu ya ce musu: “Da ku ꞌyaꞌyan Ibrahim ne, da kuna yin ayyukan da Ibrahim ya yi. 40 Amma yanzu kuna so ku kashe ni, ni wanda na gaya muku gaskiyar da na ji daga Allah. Ibrahim bai yi hakan ba. 41 Kuna yin ayyukan da ubanku yake yi ne.” Sai suka ce masa: “Ba ta hanyar lalata* ce aka haife mu ba; muna da Uba ɗaya, wato Allah.”
42 Sai Yesu ya ce musu: “Da Allah Ubanku ne, da kun ƙaunace ni, domin na fito ne daga wurin Allah kuma ina nan. Ba ni ne na aiko kaina ba, amma Shi ne ya aiko ni. 43 Me ya sa ba kwa fahimtar abin da nake faɗa? Domin ba kwa iya sauraron abin da nake faɗa ne. 44 Ku ꞌyaꞌyan Ibilis ne, kuma kuna so ku yi abubuwan da ubanku yake so. Shi mai kisa ne tun daga farko, kuma bai tsaya da kyau a cikin gaskiya ba, domin babu gaskiya a cikinsa. A duk lokacin da ya yi ƙarya, yana nuna halinsa ne, domin shi maƙaryaci ne da kuma uban ƙarya. 45 Saboda ina gaya muku gaskiya, ba ku gaskata da ni ba. 46 Wane ne a cikinku zai iya faɗan zunubin da na taɓa yi? Idan gaskiya nake faɗa, me ya sa ba ku gaskata da ni ba? 47 Wanda ya fito daga wurin Allah yana saurarar abubuwan da Allah yake faɗa. Shi ya sa ba kwa saurarar abubuwan da nake faɗa, domin ba ku fito daga wurin Allah ba.”
48 Sai Yahudawan suka amsa masa suka ce: “Ai gaskiya ne muka faɗa saꞌad da muka ce, ‘Kai mutumin Samariya ne kuma kana da aljani.’” 49 Sai Yesu ya amsa ya ce: “Ba ni da aljani, amma ina daraja Ubana ne, kuma ku ba kwa daraja ni. 50 Amma ba na neman a ɗaukaka ni, akwai Wanda yake neman a ɗaukaka ni, shi ne kuma mai yin shariꞌa. 51 A gaskiya ina gaya muku, duk wanda yake yin abin da nake faɗa, ba zai taɓa mutuwa ba.” 52 Sai Yahudawan suka ce masa: “Yanzu kam mun tabbatar da cewa kana da aljani. Ibrahim ya mutu, har ma da annabawa, amma ka ce, ‘Duk wanda yake yin abin da nake faɗa, ba zai taɓa mutuwa ba.’ 53 Ka fi babanmu Ibrahim, wanda ya mutu ne? Annabawa ma sun mutu. Kana ganin kai waye ne?” 54 Sai Yesu ya amsa musu ya ce: “Idan na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba kome ba ne. Ubana wanda kuka ce shi ne Allahnku, shi ne yake ɗaukaka ni. 55 Duk da haka, ba ku san shi ba, amma na san shi. Kuma idan na ce ban san shi ba, zan zama maƙaryaci kamar ku. Amma na san shi kuma ina yin abin da ya faɗa. 56 Ibrahim babanku ya yi farin ciki domin zai ga zamanina, ya gani kuma ya yi farin ciki.” 57 Sai Yahudawan suka ce masa: “Ba ka kai shekara hamsin ba tukuna, to ta yaya ka ga Ibrahim?” 58 Yesu ya ce musu: “A gaskiya ina gaya muku, kafin a haifi Ibrahim, ina raye.” 59 Sai suka ɗibi duwatsu don su jejjefe shi, amma Yesu ya ɓoye kansa kuma ya fita daga cikin haikalin.