Nasiha—Halin da Muke Nunawa ta Furuci da Ayyuka
BABU shakka, muna murna sosai idan wani ya yi mana nasiha, wato ya yi mana wani abin kirki! Muna hamdala idan mun lura cewa wani ya damu da mu. Da yake kowanenmu yana so a yi masa kirki, ta yaya za mu kasance da wannan hali mai kyau?
Nuna kirki yana nufin cewa za mu riƙa taimaka wa mutane ta furucinmu da ayyukanmu. Tun da muna nuna kirki ta ayyukanmu, kasancewa da fara’a ba ya nufin cewa mu masu kirki ne ba. Idan muna nuna kirki da gaske, za mu riƙa nuna ƙauna da tausayi. Ƙari ga haka, wannan hali ne da ruhun Allah ke haifarwa kuma an ƙarfafa Kiristoci su kasance da shi. (Gal. 5:22, 23) Wajibi ne mu riƙa nuna kirki. Saboda haka, bari mu tattauna yadda Jehobah da Ɗansa suka nuna kirki da kuma yadda za mu yi koyi da misalinsu.
JEHOBAH YANA YIN KIRKI GA KOWA
Jehobah yana nuna kirki da sanin yakamata ga kowa, har ga “mutanen da ba sa godiya da kuma mugaye.” (Luk. 6:35) Alal misali, Jehobah yana sa “rana ta yi haske a kan masu kirki da marasa kirki ma, ya kuma aiko ruwan sama a kan masu adalci da marasa adalci.” (Mat. 5:45) Saboda haka, har mutanen da ba su yi imani cewa Jehobah ne ya halicce su ba suna amfana daga abubuwan da ya yi don mu ji daɗin rayuwa.
Misali na musamman na yadda Jehobah ya nuna kirki shi ne abin da ya yi bayan Adamu da Hauwa’u sun yi zunubi. Jim kaɗan bayan lokacin, sun “samo ganyayen ɓaure suka ɗinɗinka suka yi wa kansu abin rufe tsiraicinsu.” Amma Jehobah ya san cewa za su bukaci tufafin da ya dace da yake ya kore su daga lambun Adnin. Jehobah ya riga ya la’anta ƙasa kuma ‘ƙayoyi da wuta-wuta sun tsiro tare da ciyawa mai kashe amfanin gona.’ Saboda haka, Jehobah ya tausaya musu kuma yi musu “abin rufe jiki na fata.”—Far. 3:7, 17, 18, 21.
Ko da yake Jehobah yana yin nasiha ga “masu kirki da marasa kirki,” amma ya fi son yin nasiha ga bayinsa masu aminci. Alal misali, a zamanin annabi Zakariya, wani mala’ika ya damu sosai sa’ad da ya lura cewa an daina gyara haikalin da ke Urushalima. Jehobah ya saurare shi kuma ya yi masa “kalmomin alheri da na ta’aziyya.” (Zak. 1:12, 13) Haka ma Jehobah ya bi da annabi Iliya. Akwai lokacin da Iliya yake baƙin ciki sosai har ya ce wa Jehobah ya ɗauki ransa. Jehobah ya lura da baƙin cikin da yake yi kuma ya aika mala’ika ya ƙarfafa shi. Ƙari ga haka, ya tabbatar masa da cewa ba shi kaɗai yake bauta masa ba. Bayan da Jehobah ya yi wa Iliya waɗannan maganganu masu daɗi, ya sami ƙarfin ci gaba da hidimarsa. (1 Sar. 19:1-18) Wane bawan Allah ne ya fi kasancewa da wannan hali na musamman?
YESU MUTUM NE MAI KIRKI
Sa’ad da Yesu yake duniya, an san da shi a matsayin mai nuna kirki da sanin yakamata. Bai taɓa yi wa mutane baƙar magana ba ko kuma ya taƙura musu. Ya furta da tausayi cewa: “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji, kuma kuna fama da kaya masu nauyi a kanku, zan ba ku hutawa. . . . Gama gungumena yana da sauƙi.” (Mat. 11:28-30) Da yake Yesu mai kirki ne, mutane suna bin sa zuwa duk inda ya je. ‘Tausayi’ ne ya motsa shi ya ciyar da su, ya warkar da marasa lafiya kuma ya koya musu “abubuwa da yawa” game da Ubansa.—Mar. 6:34; Mat. 14:14; 15:32-38.
Abin da ya kuma nuna cewa Yesu yana da kirki sosai shi ne yadda yake yin la’akari da mutane kuma yake bi da su. Yesu ya ‘marabci’ kowa ko da sun ce ya yi wani abu mai wuya sosai. (Luk. 9:10, 11) Alal misali, bai tsauta wa wata mata mai zub da jini da ta taɓa tufafinsa ba, duk da cewa ta ƙarya doka. (L. Fir. 15:25-28) Matar ta yi shekara 12 tana fama da wannan cutar kuma Yesu ya tausaya mata. Ya ce mata: “ ’Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, kin warke daga ciwonki.” (Mar. 5:25-34) Babu shakka, wannan misali ne mai kyau na nuna kirki ga mutane!
YIN AYYUKA MASU KYAU ZA SU NUNA CEWA MU MASU KIRKI NE
Misalan da muka tattauna ɗazu sun nuna cewa ayyukanmu na nuna ko mu masu kirki ne da gaske. Yesu ya nanata hakan a kwatancin wani Basamare da ya yi. Ko da yake akwai ƙiyayya tsakanin Samariyawa da Yahudawa, wannan Basamare ya tausaya wa wani Bayahude da ’yan fashi suka yi wa dūka kuma suka jefar da shi a hanya. Halin kirki ne ya motsa Basamaren ya ɗauki wannan matakin. Ya sa magani a raunin mutumin kuma ya kai shi masauki. Basamaren ya biya kuɗi don a kula da mutumin kuma ya ce idan ya dawo, zai biya duk wani kuɗin da aka kashe.—Luk. 10:29-37.
Ba ta ayyukanmu kaɗai za mu iya nuna kirki ba, amma ta furucinmu mai sanyaya zuciya. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Damuwa a zuciya takan hana mutum sakewa, amma kalmar ƙarfafawa takan faranta rai.” (K. Mag. 12:25) Yin nagarta da kirki za su motsa mu mu riƙa yin maganganu da za su ƙarfafa mutane da kuma sa su farin ciki.a Furucinmu zai nuna cewa mun damu da su. Maganganu masu ban-ƙarfafa da muka yi musu za su taimaka musu su jimre da matsalolin da suke fuskanta.—K. Mag. 16:24.
YADDA ZA MU ZAMA MASU KIRKI
Dukanmu za mu iya zama masu nuna kirki domin Allah ya halicce mu cikin “kamanninsa.” (Far. 1:27) Alal misali, wani sojan Roma mai suna Yuliyus wanda aka ce ya kai manzo Bulus ƙasar Roma, ya yi masa “alheri, ya bar shi ya je ya ga abokansa su biya masa bukatarsa” a birnin Sidon. (A. M. 27:3) Bayan wannan lokacin, mazaunan tsibirin Malita sun nuna “alheri ƙwarai da gaske” ga Bulus da wasu da jirginsu ya nitse a kogi. Har ma sun kunna wuta don su ɗumama kansu. (A. M. 28:1, 2) Duk da yake abin da mutanen nan suka yi ya dace sosai, amma nuna kirki ba abu da ake yi a wasu lokuta kawai ba ne.
Idan muna so mu faranta wa Allah rai, dole ne mu riƙa nuna kirki a koyaushe. Shi ya sa Jehobah ya ce mu “ɗauki hali” na yin kirki ga mutane. (Kol. 3:12) Gaskiya ne cewa kasancewa da wannan halin a koyaushe ba shi da sauƙi. Me ya sa? Domin wataƙila muna jin kunya ko ana tsananta mana ko kuma muna ɗan ji da kanmu. Amma, za mu iya magance wannan matsalar idan mun dogara ga ruhu mai tsarki da kuma yin koyi da yadda Jehobah yake nuna kirki.—1 Kor. 2:12.
Shin ka lura da hanyoyin da za ka iya yin gyara don ka zama mai nuna kirki? Ya kamata mu yi wa kanmu waɗannan tambayoyin: ‘Ina sauraron mutane cikin tausayi kuwa? Ina lura da bukatun wasu ne? Yaushe rabona da nuna kirki ga wani dangina ko abokina?’ Bayan haka, za mu iya kafa maƙasudin sanin mutanen da ke kusa da mu, musamman ’yan’uwa a cikin ikilisiya. Hakan zai taimaka mana mu san bukatunsu. Bugu da ƙari, zai dace mu nuna wa mutane kirki yadda mu ma za mu so su nuna mana. (Mat. 7:12) A sakamakon haka, Jehobah zai taimaka mana mu riƙa nuna kirki idan mun ce ya taimaka mana.—Luk. 11:13.
KASANCEWA MAI KIRKI NA SA A ƘAUNACE MU
Sa’ad da manzo Bulus ya ambata abubuwan da suka nuna cewa shi bawan Allah ne, ya ambata “kirki” a ciki. (2 Kor. 6:3-6) Mutane sun kusaci Bulus domin ya nuna cewa ya damu da su ta furucinsa da ayyukansa. (A. M. 28:30, 31) Hakazalika, halinmu zai iya sa mutane su soma bauta wa Allah. Idan muna yin kirki ga kowa har da mutanen da suke tsananta mana, za mu iya sa su daina tsananta mana. (Rom. 12:20) Da sannu-sannu, za su iya soma son saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki.
Babu shakka, miliyoyin mutanen da suka tashi daga matattu za su yi murnar shaida kirki na gaske a Aljanna a duniya. Wataƙila wannan zai zama lokaci na farko da suka taɓa shaida hakan. Hakan zai motsa su su nuna kirki ga wasu. A lokacin, duk mutumin da ya ƙi nuna kirki ko nasiha ba zai yi rayuwa a cikin Aljanna ba. Amma, mutanen da Allah ya yarda su rayu har abada za su riƙa nuna kirki da ƙauna ga juna. (Zab. 37:9-11) Babu shakka, kowa da ke rayuwa a lokacin zai kasance da kwanciyar rai! Amma kafin wannan lokacin, ta yaya za mu iya amfana a yanzu don nuna kirki?
YADDA ZA MU AMFANA IDAN MU MASU KIRKI NE
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutumin kirki yakan sami ladan kirkinsa.” (K. Mag. 11:17) Mutane suna yawan son masu yin kirki kuma suna nuna musu kirki. Yesu ya ce: “Da mudun da kuke auna wa mutane da shi, da shi za a auna muku.” (Luk. 6:38) Mutum mai kirki yana saurin samun abokan kirki.
Manzo Bulus ya ƙarfafa ’yan’uwan da ke ikilisiyar Afisa cewa: Ku riƙa “yi wa juna kirki, ku ji tausayin juna, ku yafe wa juna.” (Afis. 4:32) Idan kowa a cikin ikilisiya yana da kirki da kuma tausayi, kowa a ciki zai amfana sosai. ’Yan’uwan da ke da waɗannan halayen ba za su so yin baƙar magana ko zagi da dai sauransu ba. A maimakon yin gulma, za su yi amfani da furucinsu don su taimaka wa mutane. (K. Mag. 12:18) A sakamakon haka, dangantakarsu da Jehobah za ta yi danƙo sosai.
Hakika, muna nuna kirki ta furucinmu da ayyukanmu. Idan muna da kirki, za mu nuna cewa muna yin koyi da Allahnmu, Jehobah. (Afis. 5:1) Za mu ƙarfafa ’yan’uwa a ikilisiyarmu kuma mu sa wasu su soma bauta wa Jehobah. Saboda haka, bari kowa ya san da mu a matsayin masu yin nasiha ko kirki!
a A nan gaba, za mu tattauna nagarta a jerin talifofi na ’ya’yan ruhu mai tsarki.