Ta Hannun Matiyu
24 Da Yesu yake barin haikalin, sai almajiransa suka zo wajensa don su nuna masa gine-ginen haikalin. 2 Sai ya ce musu: “Kun ga dukan waɗannan gine-ginen? A gaskiya ina gaya muku, ba dutse ko ɗaya da za a bari a kan wani dutse da ba za a rushe shi ba.”
3 Da Yesu yake zaune a Tudun Zaitun, sai almajiransa suka zo suka same shi shi kaɗai, suka ce: “Ka gaya mana, yaushe ne abubuwan nan za su faru, da alamar da za ta nuna cewa ka dawo,* da kuma ta ƙarshen zamani?”*
4 Yesu ya amsa musu ya ce: “Ku mai da hankali don kada wani ya ruɗe ku. 5 Mutane da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne Kristi,’ kuma za su ruɗi mutane da yawa. 6 Za ku ji ana yaƙe-yaƙe da kuma labaran yaƙe-yaƙe. Kada hankalinku ya tashi, domin dole ne abubuwan nan su faru, amma ƙarshen bai zo ba tukuna.
7 “Alꞌumma za ta yaƙi alꞌumma, mulki kuma ya yaƙi mulki. Za a yi ƙarancin abinci da girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam. 8 Duk abubuwan nan su ne somawar azaba.*
9 “Saꞌan nan mutane za su tsananta muku, kuma su kashe ku. Ƙari ga haka, dukan alꞌummai za su tsane ku saboda sunana. 10 A lokacin kuma, mutane da yawa za su yi tuntuɓe,* za su ci amanar juna kuma su tsani juna. 11 Annabawan ƙarya da yawa za su taso kuma su ruɗi mutane da yawa. 12 Da yake mugunta za ta ci-gaba da ƙaruwa, ƙaunar mutane da yawa za ta yi sanyi. 13 Amma duk wanda ya jimre har zuwa ƙarshe za a cece shi. 14 Kuma wannan labari mai daɗi na Mulki, za a yi waꞌazin sa a dukan duniya domin ya zama shaida ga dukan alꞌummai, saꞌan nan ƙarshe zai zo.
15 “Saboda haka, idan kun ga abin ƙyamar nan da ke jawo hallaka yana tsaye a wuri mai tsarki, kamar yadda annabi Daniyel ya faɗa (sai mai karatu ya yi ƙoƙari ya fahimta), 16 bari waɗanda suke Yahudiya su soma guduwa zuwa tuddai. 17 Kada wanda yake saman gida ya sauko don ya kwashi kaya daga gidansa, 18 kada wanda yake gona kuma ya koma gida don ya ɗauki mayafinsa. 19 Kaiton mata masu ciki da masu shayarwa a lokacin! 20 Ku ci-gaba da adduꞌa kada gudun nan ya zo muku a lokacin sanyi ko Ranar Assabaci; 21 domin a lokacin, za a yi ƙunci mai girma irin wanda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har zuwa yanzu, kuma ba za a sake yin irinsa ba. 22 Idan ba a rage kwanakin ƙuncin nan ba, ba wanda zai tsira. Amma saboda waɗanda aka zaɓa, za a rage kwanakin.
23 “Saꞌan nan idan wani ya ce muku, ‘Ga Kristi a nan,’ ko kuma ‘Ga shi can!’ kada ku yarda. 24 Don Kristin ƙarya da annabawan ƙarya za su taso, su yi alamu da abubuwan ban mamaki don su ruɗi mutane, har da waɗanda aka zaɓa in zai yiwu. 25 Ga shi fa, na gargaɗe ku tun yanzu. 26 Saboda haka, idan mutane suka ce muku, ‘Ga shi, yana cikin daji,’ kada ku fito; ‘Ga shi fa, yana cikin ɗaki,’ kada ku yarda. 27 Kamar yadda walƙiya take fitowa daga gabas, ta haskaka har zuwa yamma, haka zai zama a lokacin da Ɗan mutum ya dawo.* 28 A duk inda gawa take, a wurin ne gaggafa* suke taruwa.
29 “Nan da nan bayan kwanakin ƙuncin, rana za ta yi duhu, wata kuma ba zai ba da haskensa ba. Taurari za su faffaɗo daga sama, kuma abubuwan da ke sama za su girgiza. 30 Saꞌan nan za a ga alamar Ɗan mutum a sama, kuma dukan kabilun duniya za su bugi ƙirjinsu saboda baƙin ciki. Ƙari ga haka, za su ga Ɗan mutum yana zuwa a cikin gajimaren sama da iko da ɗaukaka sosai. 31 Zai aiko malaꞌikunsa ta wajen busa kakaki mai ƙara sosai, za su kuma tattara waɗanda aka zaɓa daga gabas, da yamma, da kudu, da kuma arewa. Daga wannan iyakar sama zuwa wancan iyakar.
32 “Ku koyi wani abu daga misalin nan na itacen ɓaure: Da zarar kun ga ya soma fitar da ƙananan rassa da kuma ganye, kun san cewa damina ta kusa. 33 Haka ku ma, idan kun ga dukan abubuwan nan, ku san cewa yana dab da bakin ƙofa. 34 A gaskiya ina gaya muku, wannan tsarar ba za ta shuɗe ba, har sai dukan waɗannan abubuwan sun faru. 35 Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.
36 “Ba wanda ya san ranar, ko ƙarfe nawa ne wannan zai faru, ko malaꞌikun da suke sama, ko kuma Ɗan, ba su sani ba sai Uban kaɗai. 37 Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a lokacin da Ɗan mutum ya dawo.* 38 Kamar yadda yake kafin Babbar Ambaliyar Ruwa, mutane suna ci suna sha, maza suna aure, kuma ana aurar da mata, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga cikin jirgin, 39 ba su lura ba har sai da Babbar Ambaliyar Ruwan ta zo ta kwashe su duka, haka ma dawowar Ɗan mutum zai kasance. 40 Saꞌan nan mutane biyu za su kasance a gona; za a ɗauki ɗaya a bar ɗayan. 41 Mata biyu za su kasance suna niƙa; za a ɗauki ɗaya a bar ɗayan. 42 Don haka, ku ci-gaba da yin tsaro, don ba ku san ranar da Ubangijinku zai dawo ba.
43 “Amma, ku sani cewa: Da a ce maigida ya san lokacin da ɓarawo zai zo, da ba zai yi barci ba, kuma ba zai bari a shiga gidansa ba. 44 Saboda haka, ku ma sai ku kasance a shirye, domin Ɗan mutum zai zo a lokacin da ba ku yi tsammani ba.
45 “Wane ne bawan nan mai aminci da hikima wanda maigidansa ya naɗa shi ya lura da bayi da ke gidansa, don ya ba su abincinsu a daidai lokaci? 46 Bawan nan zai yi farin ciki idan maigidansa ya dawo, kuma ya same shi yana yin abin da ya ce ya yi! 47 A gaskiya ina gaya muku, zai ba shi hakkin kula da dukan mallakarsa.
48 “Amma idan bawan nan mugu ne, kuma ya yi tunani a zuciyarsa cewa, ‘Maigidana yana jinkirin dawowa,’ 49 Sai ya soma dūkan sauran bayin, kuma yana ci da sha da masu buguwa, 50 maigidan wannan bawan zai dawo a ranar da bawan bai yi tsammani ba kuma a lokacin da bai sani ba. 51 Maigidansa zai yi masa hukunci mafi tsanani kuma ya haɗa shi wuri ɗaya da munafukai. A wurin ne zai yi ta kuka da cizon haƙora.